*SILAR HALLACI...*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
_Follow us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_
*🅿️14*
"Idanuwansa sun kurama Saman Cealling din dakin ido ammh azaharin gaskiya ba kallon wajen yakeyi ba Hankalinsa ya Tafi chan wata Duniya Tunanin Mafita game da Abunda Samiha take nemanshi Dashi.
Baisan iya adadin Wasu Mintina da awannin ya kwashe daga kwancen nan ba abunda dai kawai ya sani ya kan mulmula Daga hannunsa na Dama zuwa na Hagu yana fama da Nurfarfashi kamar wani mai Ciwon Asthma bai ankara ba sai da yaji masallacin kusa dasu suna Rangada kiran sallah Kasala ta gama Lullebe Ahmed kansa saramai yake Saboda Damuwa da Rashin mafita yana kwance Har aka Tada sallah bai iya Tashi ba Sai da aka idar kamar wanda Shedan ya Danne gabadaya Jinsa yake a sake kamar bashi ba.
Dakyar ya iya Saukowa Daga saman gadon yana Mika lokaci daya da Salati wayarsa ya cire daga Aljihu ya ijiye Bisa Side Drower din gadon tare da Link din Rigarsa,idanuwansa yakai Duba Bisa agogon Bangon Dake Cikim Daki yaga har 1:30pm na Rana ya wuce yana kwance bai samu Mafita ba kansa kawai ya Shafa yana Tafiyar Rangaji ya Nufi Tiolet Ruwa yafara kamawa kafin ya Dauro alwala ya Fito yana Goge Sauran Ruwan Dake Fuskarsa Sallaya ya shimfida ya Kalli Gabas ya Tada sallar bayan ya idar ya Dade yana Kwararoma Allah kirari kafin ya Dora da Addu"ar Allah yayimai gatan gan karfe da Samiha ya kuma Rufamai Asiri Duniya da lahira,bayan ya Shafa Addu"ar karamin Qur"anin dayake karatu Dashi ko da yaushe ya mika Hannu ya Dauko wanda ke saman Side Drower din gadon ya Bude Suratul yusuf yafara karantawa Cikin Muryansa mai Cike da Damuwa.
Sai wajen Uku saura kana ya Dakata lokaci Zuciyarsa tayimai Sanyi Maida Qur"anin yayi ma"adanarsa ya mike lokaci Daya yana Ninke Sallayar dayayi sallar da ita saman madubi ya Ijiyeta inda yagani ya koma ya kwanta bayan ya Cire Rigar Jikinsa ya Rage dagashi sai Singlet Gudun A.C yarage kafin ya Saka kanshi Bisa Filo yana maida Numfashi Daya bayan Daya Cikin Ikon Allah Barci mai Nauyi ya Daukesa wanda ya Dade yana yinsa baisan Lokaci ya Tafi ba.
Bangaren Samiha kuwa Tana Fita Ta fada Motarta dama ita kadai tazo yau bata nemi Direba ba Kwallah take Sharewa mganganun Ahmed na mata yawo acikin kwanyar kanta Har ta Fice Daga Haraban wajen tana Tsiyayan Hawaye Tun tana da Zarafin saka hannu ta goge har ta barsu sukayi ta Shatata ba kukan komai take ba sai na Bakinciki da Kishi da kuma gajiyawa Tsakani ga Allah tagaji hakanan itama tana Bukatar kwanjin Da Namiji a kanta ba kuma kowani Namiji ba Sai Ahmed wanda Tun bata Fahimci ya sha"awar Namiji yake ga Mace ba,akansa ta fara jin tana Sha"awar Namiji komai na Ahmed na irin Tsarin Mijin datake mafarkin Aure ne,Kaddara ta rabasu abaya kuma yanzu Kaddara ta kara Hadasu,saboda mutane kalilan Wanda basu da muhimmanci acikin Rayuwarta bazata Cuci kanta ba Dole ne tabama kanta da Zuciyarta Abunda takeso ko Ahmed yaso ko bai so ba yazama Dole ne kowa ya Fahimci Halin da Suke ciki.
Har ta isa gida tana kuka Sanda Ta Zuba hon a bakin tamgamemen Get din gidanta megadi ya Bude mata kuka take har ta Gama adana Motar a Parking space bata fito ba sai da goge kwallarta kana ta Fito ta Nufi Cikin gidan Ranta duk ba Dadi Abun takaichi tana Shiga Falon Taci karo da Abba sai da Ta ganshi ta Tuna yau yana gidanta ne,Bayan Fitatan kenan ya Shigo yana Kishingide yana kallon Tashar Sunna Tv ta shigo yana ganinta ya Gyara zama yana Fadin"Gimbiya kin dawo..? Na shigo Tun dazu ma"aikatanki suka ce min kin fita..'
Kallonsa Tayi cikin Wani Tsanarsa Da Takaichi Domin Tanaganin Shine mai laifin dayayi mata gatangan karfe da Masoyinta Ahmed Dakyar ta kakalo Mirmishin yake ta sakarmai kafin ta kada kai kawai ta Haura sama da Sassarfa da Kallo Abba ya Bita yana Tunanin toh meya batama Samiha rai baiyi Yunkurin Binta ba saboda Sanin Halinta ya koma ya kishingida yana Cigaba da kallonsa ammh gefe daya na Zuciyarsa na cike da Zullumi dama in zata fita ba kasafai take gayamai ba sai tayi Ra"ayi don kanta Shima kuma bai damu ba Domin Shi ya bata dama Tun Farko take Abunda taga dama yanzu ko yaso ya Hanata baza ta taba Hannuwan masa ba.
YOU ARE READING
SILAR HALACCI
FantasyAhmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alƙawarinmu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda rayuwar Aurenmu zata kasance..? amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballantana makama kakeso kaƙi amfani da...