4

38 2 0
                                    

*SILAR  HALLACI...*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

_Wattpad:Janafnacy13 or Aisha Alto alto_

        *🅿️4*

"Ranta in yayi Dubu yagama Baci na irin Wulakantatan da ake Niyyar yi a ma"aikatar mijinta,Cikin Fushi ta juya baya tana kallon Motar da tazo da ita,wanda  Direbanta ya tukota,waya ta ciro cikin karamar jakar dake Hannunta   wata faskekiyar waya ta zaro cikin Sauri da alamun Fushi ta lalubo lambar da zata kira ta kara kunni Sauran ma"aikatan suna daga gefe suna kallon Ikon Allah cikin Fushi ta Fara mgana da cewa

"Alhaji dama Ashe duk ma"aikatan da ke dauka marasa mutumci ne bansani ba..?Alhaji Bashir dake zaune falon Hajiya Rabi yayi Saurin mikewa yana Fadin"Meya faru ne gimbiya..?cikin Fada tace'Miye ma bai Faru ba Don Tsabar Wulakanci kamar Ni nazo Shopping mall dinka a hanani yin Abunda nake so..? Saboda nace ina Bukatar kowa ya Fita sai nagama Abunda zanyi na Tafi kana wani zai iya Shiga Shine wasu kananan kwari ke gayamin mgana har kiran wani suke yana bada odar in bazan Shiga ba sai dai na kara gaba.."Tafada tana wani jijjga jiki cikin rawan jiki dana baki Alhaji ke fadin"Haba gimbiya Waya isa yayi miki iko da wannan Wurin..?basu sam cewa Dani da komai nawa muna karkashin ikon ki bane..?

Baki ta tabe kafin tace"oho inaga baka Taba sanar dasu bane...Sai ka kirasu ka sanar dasu matsayina ko nasaka duka su Zama korarru musamman ma wannan Banzan dake ciki yake bada Umarni.."Cikin lallashi yake Fadin"Allah huci Ran Gimbiyata Haba Sami na..kiyi hakuri kece da Zan Fita baki gayamin zaki Fita Siyayyah da ba sai ma kin Wahalar da kanki ba,Har gida za"a kawomiki duk Abunda kike Bukata.."Tsaki ta saki tana Fadin"Ai bamu taba Haka dakai ba..na In zan fita anguwa sai na Sanar dakai ba,Ka kira kowaye ka sanar dashi ina son ganinshi yanzu agabana.."Cikin Rawan murya yace"Hakane Bari na Kirashi inaga Ahmed ne mijin Abida.."

Sanda ya kira Sunan Ahmed sai da Zuciyarta ta amsa cikin Wani yanayi tace"Ahmed.... ? Eh Ahmed mijin Abida mana Baki sanshi ba ammh ai kina jin Sunansa abakina shine Wakilina a Duka Harkan kasuwancina"Baki ta tabe kafin tace"Koma mijin Rabi ne ba Abida ina son ganinshi yanzu yanzu nan..."Daga haka ta yanke Kiran ta bar Alhaji da Zufan goshi Cikin mamaki Hajiya Rabi ke kallon sa kafin tace"Wai lafiya Alhaji..?

Yana lalubo lambar Ahmed yake fadin"Ina fa lafiya gimbiya taje Siyayyah Shopping mall dina sun hanata shiga wai sai dai in zata shiga tare da mutane ita kuma kin santa bata son hayaniya shine tace tana bukatar kowa ya Fita sai ta gama toh kinsan Ahmed akwai zafin Zuciya inaga shi ya bada Umarni kar abarta ta Shiga batare da yasan Gimbiyata bace nasan daya sani bazai fara ba.."Galala Hajiya Rabi ta bishi da kallo Daidai Lokacin dayake saka wayarsa bisa kunni cikin Takaichi da mamaki take Fadin"Yamin daidai wlh...Ita yar gidan Uban wacece da zatace Kowa sai ya Fita zata shiga tayi Siyayyah..? Aiko yar Shugaban kaasa,tana shiga waje kuma ta cukuda da mutane ma ba"a ganeta ba balle ita yar Yariman kashi..'

Wani kallo yake ta watsa mata kafin ya kama hanyar Barin Falon Daidai lokacin da Ahmed ya Daga wayar yana fadin"Ina kwana Abba.."bai tsaya amsa gaisuwan nasa ba yafara fada yana Fadin"Kai Ahmadu kana da Hankali kuwa..? Gimbiya ce fa tazo ta kuma bada Umarni tana Bukatar kowa ya fita sai ta gama Abunda takeyi ta tafi kana kowa zai iya Shiga kuma domin Rashin mutumci sai kuka hanata shiga Kasan wacece kuwa..? Cikin mamaki Ahmed yace"Abba wacece Bansanta ba..?

Cikin Haushi Abba yace"Gidanku nace Ahmed...Samiha ce fa gimbiyata.."Da Sauri Ahmed yace'Oho Abba ai bansani ba ammh kuma tazo tace duka costumer su fita waje kana ganin daidai ne Abba.."inda Ahmed na kusa dashi ba abunda zai hana bai kasheshi da mari ba cikin Bacin rai yace"Bansani ba nace...Mallam maza kaje ka bata Hakuri kuma abi Umarninta duk Abunda tace shine za"ayi.."

Cikin mamaki Ahmed ya bude baki zaiyi mgana Abba yace"Kaji Abunda nace ko..? Cikin Sanyin Jiki Ahmed yace'Naji Abba za"ayi yadda kace.."Dan sakin Rai yayi yana fadin"yauwa ko kaifa Ahmed..ka bata hakuri kaji ko..? Numfashi ya saki yana fadin"Shikenan Abba.."Dariya yayi yana Fadin"Allah maka albarka Shiyasa nake sonka akwai Hankali kaji sai hakuri nima Hakuri nake da ita.."Saboda takaichin Abba dakyar ya iya amsawa sukayi sallama Daidai lokacin da suka karisa Fitowa haraban  mall din manaja na binsa abaya,ajiyar zuciya ya sauke yana karema Matar kallo wacce ke Tsaye jikin Motarta prado baka ta juya baya Hannuwansa ya Tusa cikin Aljihun Shaddar dake Jikinsa yana kallon Manaja yace"Wai Ashe Amaryan Abba ce.."

SILAR HALACCIWhere stories live. Discover now