01 Tsautsayi

10.8K 361 15
                                    


CIKIN TASHA:

    A cikin cinkoson mutanen dake fitowa daga cikin motar hayar har da wata matashiyar budurwa, wacce in ka lura da yadda take waige-waige tana zare idanu zaka tabbatar yau ne farkon shigowanta garin Gombe, wanda ake musu kirari da 'Gombawa d'iban fari, ba'a kwana daku ba an tashi daku'.
Itama FATU haka ya kasance da ita domin yanzu misalin karfe bakwai ne na safe. Sanye take cikin atamfa koriya riga da zani, sai babban hijabi bak'i da ta sanya wanda ya kai har k'aurin kafarta. Duk da girman hijabinta bai hanata mannawa fuskarta nik'abi ba wanda hakan yasa ba'a ganin komai na jikinta sai k'afarta, tafin hannunta da kuma kwayar idanunta da suke farare kamar madara.
  Daga ganin yanayinta kadai zaka gane ita bak'uwa ce a cikin wannan gari mai tarin jama'a.
  Fatu matsawa tayi gefe ta tsaya inda babu mutane ta cigaba da dube dubenta tana neman hanyar da zata bi ya fitar da ita wajen tashan. A can nesa ta hango wata mai sayar da k'osai tayi saurin kawar da kanta, amma jin yanda cikinta ke murd'awan yunwa yasa ba shiri ta nufi gurin cikinta na bada wani sauti 'kululululu', domin rabon da taci abinci tun shekaran jiya da rana, sai kuma fura da Kakanta ya bata jiya da dare ta sha kad'an nan ma sai da ya matsa mata. A nan ta yarda da cewa yunwa ba abokin wasanta bane, sannan Idan har tana son cikar burinta dole ne ta ci abinci ko don ta rayu. Bata da za6i ita kanta ta yarda da hakan.
  Da saurinta ta isa, sallama tayiwa mata mai sayar da k'osai, matar ta amsa. A nan ta tsaya har layi ya iso kanta tace a bata k'osan d'ari. Ba'a jima ba matar tasa mata a leda ta mik'a mata. Sabuwar d'ari biyar Fatu ta ciro daga cikin jakarta ta mik'a aka bata canji ta sokesu a jakan ta k'ara gaba.
  A nan kusa ta ga wasu yara masu sayar da pure water ta tsayar da su ta sayi guda biyu. A nan dinne kuma ta fara tunanin a ina zata zauna taci abun karyawanta, don har masu shaguna sun fara bud'ewa sannan ga hayaniyar jama'a da kuma ta motoci a duk cikin tashan motar.
  Tana daga tsayen ta hango wani bakin shago wanda babu mutane ta isa gurin cikin sassarfa gudun kar mai shagon ya rigata zuwa ya bud'e. Zama tayi tana mai juyawa tashar baya ta fuskanci k'ofar shagon saboda kar mutane su kalleta a yayin da take cin abinci. A hankali ta fara cin k'osan tamkar an mata dole tana korawa da pure water Idan ya tsaya mata a wuya. Ko rabinsa bata ci ba taji ya fita a kanta, ta kulle ledan kana ta mik'e tsaye tana furta 'Alhamdulillah'.
A gefen shagon ta wanke hannu sannan ta goge bakinta da zumbulelen hijabin da ke jikinta. Wani almajiri da ke tsaye yana kallonta tun d'azu shi ta yafuto da hannu ta mik'a masa sauran k'osan ya kar6a yana cewa
  "Allah shi kar6a."  
"Ameen." Ta amsa masa.
Juyawa tayi ta bi hanyar da ta ga motoci ke shige-da-fice wanda ta tabbatar nan ne zai sadata da kofar fita daga tashan.
  Tunani ne tuli jibgi a cikin kwakwalwarta wanda hakan yayi sanadiyyar har ta fito daga tashan ta kuma hau kan titi bata sani ba.
"Ke ki tsaya!"
"Ki dawo baya. Bakya ji ne? Ke ga mota!!   
"Ke! Ke! Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun!!"
Fatu bata tashi fahimtar maganganun mutanen ba sai da taga motar da ake fad'a daf da ita. Second d'aya da haka motar ta kwasheta ta watsar a titi 'timm' tamkar wata himilin wanki.
Kan kace me guri ya rud'e da ihu da Innalillahi ta ko'ina. A kid'ime wata mata ta fito daga motar ta yi kan Fatu da ke yashe a k'asan titi hannunta bisa kanta tana cewa,
"Innalillahi, na shiga uku na buge 'yar mutane. Don Allah ku dubamin ita kar na kashe rai. Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun!"
  Kafin ta isa har mutane sun fara taruwa a kan Fatu ana dubata bayan an yaye mata nik'abin fuskarta. Kutsawa matar ta yi cikin mutanen ta isa kan Fatu da saurinta tana cewa su taimaka mata su sakata cikin motarta ganin bata mutu ba, amma kuma bata cikin hayyacinta.
   A nan wasu mata masu sharan titi suka taimaka mata suka saka Fatu a motarta, cikin azama matar ta shiga mazaunin direba ta cilla kan titi sai Asibiti.

Cikin Asibiti:

Tana isa asibiti bata yi wata-wata ba ta shiga, minti d'aya da haka sai gata ta fito da Nurses biyu had'e da gadon tura marasa lafiya. A nan suka cicci6i Fatu dake bayan mota suka d'aurata akan gadon suka shiga Emergency da ita cikin gaggawa.
  Sai a lokacin hankalin matar ya dawo kan d'anta karami d'an shekara biyar wanda sai a yanzu ta lura kamar a gigice yake. Da sauri ta isa gurin motarta ta bud'e gaba in da yake zaune ta jawoshi jikinta tana mai cewa,
"Faruk yaya dai? Me ya sameka? Baka jin dad'i ne?"
Sarai tasan firgita yayi wanda itama a cikinshi take amma baza ta bari ya gane halin da take ciki ba balle ya k'ara tsorita.
"Ammi kin buge wancan Aunty! Ta fad'i a kan titi Ammi! Ta mutu ko?" Ya tambayeta bayan ya dago kansa yana kallonta idonsa cike da tsantsan tsoro hade da firgici.
Shafa kanshi tayi ta mayar dashi kan kirjinta tana cewa,
"Babu abun da ya sameta Faruk, suma kawai tayi, kuma da zarar Doctor ya mata allura zata tashi garau kamar babu abun da ya sameta, ka ji ko?" Ta fad'i hakan don ta kwantar masa da hankali ba tare da ita kanta ta san makomar yarinyar ba. Fatanta kar ta yiwa 'yar mutane illah.
Haka taci gaba da kawar da tunaninsa har sai da ta tabbatar ya nitsu sannan ta ce,
"Mu je in kaika gida tunda na ga ka tsorita."
Mak'e kafad'a yayi yana cewa,
"A'a nikam ki kaini makarantana, su Akram suna jirana."
Shafa kanshi ta yi kana ta rufe marfin motar ta koma cikin asibitin ta samu wata Nurse da ta fito daga d'akin emergency zata koma ciki ta tareta, a nan ta fad'a mata cewa zata kai yaro makaranta amma yanzu zata dawo.
A tsanake Nurse d'in ta bita da kallo, ganin suturun jikinta da kuma motar da ta faka a haraban asibitin yasa ta sanya a ranta cewa matar ba guduwa zata yi ba. Bayan sun gama magana Ammi ta koma cikin mota ta fita a asibitin kai Faruk makaranta. Dama can suka nufa garin sauri kar yayi latti wannan kaddaran ta faru har ta buge 'yar mutane. Gaskiya ne da aka ce 'sauri ya haifi nawa'.
  Bayan minti goma ta dawo cikin asibitin a daidai lokacin da wani Likita ya fito daga d'akin emergency, Ammin Faruk ta yi sauri ta tareshi tana tambayarshi batun mara lafiyar.
"Jikinta da sauk'i babu wani babban matsala na tayar da hankali. Sannan ba ta bugu sosai kamar yanda ake zato ba, hasalima tsoritan da ta yi yasa ta suma, sai kuma kurjewa da tayi a kafa da kuma hannunta. Yanzu Nurses zasu kai ta d'akin hutawa zata farka nan ba da jimawa ba saboda tana bukatar hutu a kwakwalwarta." Yana gama fad'in haka yayi gaba bayan sun yi sallama.
  A bakin k'ofar ta tsaya jiran fitowarsu, sai can ga wata Nurse ta gangaro da Fatu a kan gadon marasa lafiya ta kaita d'akin hutu Ammi na biye da ita a baya. Da taimakonta suka mayar da Fatu kan gadon da ke d'akin sannan Nurse ta fita ta bar su.
Ammi tsayawa ta yi akan yarinyar tana mai kallon fuskarta wanda gefe d'aya ya kumbura alamar buguwa. Sai a lokacin hankalinta ya kwanta ganin bata kashe d'iyar mutane ba.
  Godiya ta yiwa Allah babu adadi, sannan ta zauna a kujera d'aya tilo da ke d'akin tana mai cigaba da kallon yarinyar tana fatan ta farka da wuri ta mayar da ita gurin Iyayenta.

FATU A BIRNI (Complete)Where stories live. Discover now