03

3.1K 196 1
                                    

An yi murna ga masu yin murna, wani iko na Allah sai ciki yazo da sauki babu cuta babu kasala. Amma da ranar haihuwa ta zo Ramatu ta jikkata sosai tamkar baza ta haihu ba. Ai kuwa tana haihuwa tace ga garinku. Mamuda yayi kukan rashin matarsa mai hak'uri da juriya ga sanin dattako.
Ran suna yarinya ta ci sunan kakarta na gurin uba wato Fatima ana kiranta Fatu. Yarinya ta taso cikin kulawan mutum uku, Kakaninta da kuma Babanta, ganin duk wani so an d'aura mata ne yasa Muntari ya fara bin hud'ubar su Goggo Innani akan cewa an fi son Fatu a kan yayansu.
Fatu ta yi makarantar Primary a nan k'auyensu, in da tana cikin masu k'okari na ajinsu. Ko da ta gama Babanta ya sakata a Secondary a cikin garin Kumo. Tana Jss two Babanta yayi hatsari akan hanyarshi ta zuwa kasuwancinsa. Basu samu labari ba sai gawarsa da aka kawo. Fad'in irin tashin hankalin da suka shiga ma bata lokaci ne. Fatu ta yi kuka har ta rasa inda zan tsoma ranta ta ji dad'i. A nan kuma take tunanin ko dai gaskiansu Goggo Asabe da Goggo Innani da suke cewa zuri'ar Fulanin yawo akwai mayu masu cinye duk wanda suka ra6esu. Inna Binta kuma tun daga rasuwar Mamuda ta fara k'ananun rashin lafiya, yau itace ciwon k'irji, gobe k'afa jibi kuma kai.
Fatu taci gaba da karatunta dalilin Kakanta ya jajirce sai ta gama Secondary kamar yanda Mamuda yaci buri, duk zund'en da ake kawo masa na cewa sa'annin Fatu sun yi aure daga mai 'ya'ya biyu sai mai uku baya dauka.
Da haka har Fatu ta gama makaranta ta dawo zaman gida. A nan kuma samari suka yi mata caaa! Don a da duk wanda yazo gurinta sai Kakanta ya ce sai ta gama karatu, to yau gashi ta gama makarantar kuma har a lokacin bata da wanda ya ta6a burgeta balle har ta ji zata yiwa aurensa. A cikin maneman auren Fatu har da d'an Baffa Muntari da d'an Goggo Innani.

Ranan Fatu tana bacci cikin dare ta ji tamkar ana shafata, bud'e idon da zata yi ta ga Bello d'an Baffa Muntari tsugune kusa da ita hannunsa bisa k'ugunta. Da ya ga zata masa ihu ya toshe bakinta, ita kuma ta tak'ark'are ta dank'ara mishi cizo yayi saurin d'age hannunsa a bakinta yana yarfe hannu. Ihu ta yi mutanen gida suka fito ana haskawa aka shigo d'akin da take kwana da yara, dalilin sa'anninta mata 'yayan Baffa Muntari duk sun yi aure sun barta.
"Fatu menene ya sameki?" Kaka ya tambayeta yana haska fuskarta da tocilan hannunsa.
Bata ji tsoron komai ba ta ce,
"Bello ne ya shiga d'akinmu yana ta6ani." Ta bashi amsa tana goge kwallar fuskarta kuma har a lokacin jikinta bai daina rawa ba.
Kafin Kaka ko wani yayi magana Inna asabe ta ca6e,
"Munafukar yarinya masharranciya! sharri zaki yiwa yayan naki? Me abun gani a jikin naki da har zai bi dare ya ta6a?"
Ran Kaka 6aci ya dakatar da ita da hannunsa ya dubi Bello da yake zare idanu ya ce,
"Kaji abunda Fatu tace, me ma ya kaika d'akinsu da tsakar dare haka?
"Wallahi k'arya take mini, na fito zaga bayan gida ne na ji kamar nishin mutum a dakin, nayi zaton ko dayansu bashi da lafiya ne yasa na shiga, ko da na haskasu sai naga Fatu ce take yin wannan nishin tana fisge-fisge. Dalilin kenan da yasa na bugi hannunta tana tashi kuwa tasa ihun nan har kuka fito."
Salallamai Goggo Asabe tasa tana kuka wai na yiwa danta sharri. Shi kuma Bello ya fita zaure in da d'akinsu yake yana mita wai dama ba'a sonsu a gidan an tsani uwarsu yanzu kuma ya dawo kansu.
Fatu kuma ta rantse da Allah cewa abunda ta fada ne gaskiya. Ganin hayaniyar ya yi yawa a tsakiyar daren yasa Kaka ya sallamesu duka da zazzafar kashedi ga Baffa Muntari kan ya kula da d'ansa. Inna Binta ce ta jawo Fatu d'akinta ta k'arasa kwanan a nan. Daga ranar Fatu ta koma kwana a d'akin Kakarta.
Kwana biyu da faruwar wannan al'amari Inna Binta ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazzabi ga jiri da yake d'ibanta, an yi magani na gida har asibiti aka je a nan suka ce jininta ne ya hau sosai, bata jima a asibitin ba ta koma ga mahaliccinta. Damuwa goma da ashirin.

Fatu hawaye ta fara zubarwa Ammi cikin tausayawa ta zaro Tissue paper ta mika mata ta goge fuskarta sannan taci gaba.

"Hajiya kin ta6a jin labari makamancin nawa wanda duk masu sona sun mutu sun barni? Wani lokacin na kan yarda cewa watakila da gaske akwai maita a tare dani da shine dalilin da yasa kowa nawa ya mutu ya barni. Na shaku da Kakata sosai, a matsayin mahaifiya na d'auketa domin ita na tashi nake gani a matsayin uwata. Ko kusa bana jin rasuwar mahaifiyata kamar na Kakata dalilin ban santa ba amma nakan yi kewarta a duk lokacin da na ga gurbinta."

FATU A BIRNI (Complete)Where stories live. Discover now