05

3K 175 0
                                    

  Kamar wanda aka aika Faruk ya tashi ya je ya d'auko jakan makarantarshi ya fara ciro littafansa yana cewa,
"Ammi nikam yau wannan ne zata min Homework d'ina." Ya fad'a yana mai nuna Fatu.
"Sunanta Aunty Fatima ba wannan ba." Ammi ta gyara masa.
Wani dad'i ne ya ziyarci Fatu jin an kirata da Aunty kuma wai Fatima ba Fatu ba. Murmusawa ta yi ta jawo yaron jikinta tana tambayarshi in da aka bashi homework d'in.
  Yanda take nuna masa komai dalla-dalla yasa Ammi cikin mamaki, don da harshen turanci take masa bayani yana amsawa, Idan yana neman k'arin bayani sai ta k'ara fahimtar dashi.
Ko da suka gama ya d'auki jakanshi ya mayar d'akinsa. Yana dawowa Ammi ta ce dare yayi ya je ya kwanta. Ransa bai so hakan ba amma haka ya wuce bayan ya musu sai da safe.
A nan Ammi ta dubi Fatu wacce tafiyan Faruk bai mata dad'i ba, don har ta fara takura, surutun yaron yana mantar da ita damuwar da take ciki.
"Fatima kin ce a Garin Modibbo kika yi Primary, to Secondary fa?"
  "Eh, a Garin Modibbo na yi Primary, Secondary ne na yi a cikin Kumo. Wannan abokin Babana da ya kawoni tasha shi yake zuwa gida da sassafe ya kaini cikin Kumo, idan an tashi kuma sai In tari Acaba ya maidani gida."
"Kin yi WAEC da NECO ne?" Ammi ta k'ara mata wata tambayar don wani tunani da ta yi na cigaban Fatu.
  "Na yi, har JAMB duka na yi."
  "Da fatan dai kin samu abunda ake buk'ata na shiga Jami'a?"
"Duk na samu, hatta JAMB din 202 points nake dashi. Sau biyu kenan Ina yin JAMB sai wannan shekarar na samu."
"Masha Allah. Ashe baza mu sha wahalan sama miki Admission ba, na ji dad'in hakan sosai." Ammi ta fad'a cikin farin ciki.
"Hajiya a ina zan samu Admission din? Makaranta zan koma?" Fatu ta tambaya cikin rashin gaskata kunnenta.
"Insha Allah makaranta zaki koma. Yanzu dare yayi ki je ki kwanta ki huta, gobe in Allah ya kaimu zamu k'arasa maganan."
  Bayan sun fito falo ne Ammi ta nuna mata wani d'aki kusa da nata ta ce,
"Wannan d'akin Faruk ne nasan yanzu yayi bacci, wancan k'ofar na gaba kuma d'akin 'Yata ce Aisha wacce a yanzu take aure a Kano. Yanzu ya zama naki kafin mu ga abunda Allah zai yi gaba."
  D'akin da aka kira na Fatu d'aki ne madaidaici da band'akinshi a ciki, gado ne mai d'an girma sai wardrobe d'inshi da mirrow wanda kalarsu yake Fari, can gefe kuma table ne na karatu tare da kujerarsa wanda shima kalarsa Fari. Labulaye da fentin d'akin kuma kalarsu kore. Sosai d'akin ya burge Fatu ta yi sana'ar tata ta sake baki. Wai nan d'akinta ne? A nan zata dinga kwana?
"Yanzu Hajiya duka wannan d'akin ni kad'ai? Ni kam ko a d'akin mai aikinki zan dinga kwana." Fatu ta yi saurin fad'a ganin Ammi na shirin fita.
  "A'a Fatima. A nan d'in zaki zauna, bana son kina banbanta kanki dasu Faruk duk d'aya kuke a gurina. Ina so ki saki jikinki tamkar nan ne gidanku, abunda nake buk'ata kenan daga gareki in har zan samu."    
"Hajiya kin fi karfin buk'atar abu a gurina sai dai ki bani umarni In yi. In Allah ya yarda zaki sameni mai miki biyayya. Wallahi ban taba tsammanin masu kud'i suna son jama'a ba sai da na had'u da ke. Nagode sosai da d'awainiyarki a kaina, Allah ne kad'ai zai iya biyanki. Nagode."
Murmusawa kawai Ammi ta yi ta fita bayan ta yiwa Fatu sallama.
  Fatu ajiye jakanta ta yi a kan gado ta zauna a kai tana gwada laushinsa tana murmushi. Can kuma ta mik'e ta shiga band'aki, nan d'in ma sai da ta gama kare masa kallo sannan ta tu6e kayanta ta shiga wanka bayan ta ciro soso da sabulu a cikin jakanta. Ta fito kenan tana tsane jikinta ta ga an sakawa gadon bedsheet ga kuma wasu night wears riga da wando kalar Orange a kan gadon. Sai da ta mulkawa jikinta Vaseline sannan ta d'auko kayan masu taushi ta saka don dai hankalinta ya bata ita aka ajiyewa.
"Alhamdulillah." Ta furta bayan ta zauna a kan gadon tana kallon kayanta kala uku da ta jera a cikin wardrobe d'in.
Jakanta da ke kusa da ita ta bud'e ta ciro kud'in sadakinta da kuma hotonta ita da Sultan ta k'ura musu ido. Hawaye ne ya taru a idonta ta yi saurin mayar dasu amma zuciyarta bai daina suya ba.
"Daga yau na daina kuka a kanka Sultan, na yi a baya amma banda yanzu da nake shirin kwatar yancina. Na gaji da zubar hawaye a kan mutumin da baya k'aunata, idan har bai tausayamin a matsayina na matarsa ba to kuwa ya kamata ya tausayamin tun da ni dashi jini daya ne. Na gaji kuma na daina." Kalaman Fatu kenan a daidai lokacin da take mayar da kudin da hoton cikin jakar kana ta wurga jakar cikin wardrobe d'in ta rufe.
Addu'a ta yi tana tunanin yanda wahalan rayuwa yasa ta fara yankewa kanta hukunci ba tare da ta jira an mata ba.

FATU A BIRNI (Complete)Where stories live. Discover now