02

3.8K 195 5
                                    

Fitowa Ammi ta yi daga motar ta zagayo in da Fatu take, bude murfin k'ofar tayi ta kamo hannunnta suka shigo cikin gida ta zaunar sa ita a kan d'aya daga cikin kujerun da ke falon, har a lokacin Fatu na cigaba da kuka.
"Dija, Dija!" Ammi ta shiga kwala mata kira, da gudu Dija ta fito daga kitchen tana cewa,
"Gani Hajiya."
"Taimaka ki kawomin ruwa yanzu."
Komawa kitchen Dija ta yi, sai ga ta ta fito tire an aza ruwan gora da kofi a kai. Akan teburin tsakiyar falon ta ajiye sannan ta bud'e marfin goran ta tsiyayi ruwa a kofi ta mik'awa Ammi, tana tunanin wace yarinya ce haka? Ko dai itace wacce Hajiya ta buge don ga alamu jikinta ya nuna ta yi karo da mota.
Fatu da kukanta ya tsagaita amma bata bar sheshshekar ba ta kar6i ruwan da Ammi ke mik'a mata ta kur6i kad'an har tana k'okarin kwarewa.
Ajiyar zuciya ta sake tana mai goge hawayen fuskarta bayan ta daidaita numfashinta.
A nan Ammi ta fara magana bayan Dija ta basu guri ta ce,
"Fatu a yanda na lura da yanayinki kina cikin matsala, kuma kinyi k'arama a barki ki fito daga kauyenku ke kadai ba tare da wani dan uwanki ba. Tambaya nake son miki, ki fadi tsakaninki da Allah, gurin waye kika zo anan garin?"
Fatu da tunda Ammi ta fara magana kanta na k'asa ta ce,
"Gurin dan'uwana nazo."
"A ina dan'uwan naki yake?" Ammi ta sake jeho mata wata tambayar.
Shiru Fatu tayi wanda sai da Ammi ta sake maimaita mata tambayar sannan ta budi baki ta ce,
"Na manta sunan unguwan amma yana cikin jakata, idan na fita zan duba." Ta k'ara wata karyar don so kawai take ta rabu da Hajiyar kar ta tonawa kanta asiri, tasan Idan ta gane karya take yi zata iya mayar da ita garinsu wanda In hakan ta faru tasan kashinta ya bushe sannan zata ji kunyar Kakanta sosai, a yanda ya dauketa bai cancanci ta masa haka ba.
"Faruk? Ammi ta kwala kiran yaronta wanda tun sha biyun rana aka d'aukoshi daga makaranta.
"Gani Ammi." Ya fad'a bayan ya fito ya zauna kusa da Ammi yana kallon Fatu kamar In ta mishi magana zai gudu.
"Ka je cikin motana zaka ga wani jakan makaranta akan kujeran baya ka d'auko min."
Gyad'a kai yayi ya tashi tsaye amma hankalinshi na kan Fatu, ya mayar da dubansa kan mamanshi ya ce,
"To Ammi ba wannan ce ta mutu d'azu ba?"
"A'a, ban ce maka ta mutu ba Faruk. Maza je ka d'aukomin jakar."
Da gudunshi ya je ya d'auko ya mik'awa Ammi ita kuma ta bawa Fatu. Isa gurin Fatu yayi ya tsaya a kanta ya tsura mata ido wacce itama tun shigowarshi d'azu take kallonshi.
"Dazu Ammina ta bugeki da motarta, kin ji ciwone?" Ya tambayeta ya kallon bandejin dake manne a hannunta.
A karon farko tun shigowarta garin Gombe ta murmusa gareshi ta ce,
"Dan kad'an kawai naji ciwon."
"Ammi tace kin suma ko?"
Ta gyad'a masa kai tana mamakin surutunsa.
Zai kara wata tambayar Ammi ta katseshi da cewa,
"Faruk ka tafi d'akinka ka fara shirin islamiyya. In ka dawo she will answer all your questions."
"Laa! A gidanmu zaki zauna kenan? Ina Mamanki da Babanki to?"
Wannan karon bai samu amsa daga Fatu ba domin sunkuyar da kanta tayi k'asa tana jin kewar iyayenta a ranta. A tunaninta da suna tare da ita da wannan kaddaran bai faru da ita. Da itama tana rayuwa ne kusa da iyayenta rayuwa na zuwa mata yanda take so. To amma hakan ba tsararre ne cikin kaddaran rayuwarta ba. Wai Tun ran gini tun ran zane.
"Faruk. Ka tafi d'akinka yanzun nan kar in kara jin kayi magana." Cewar Ammi ganin tambayar da yayi ya canja yanayin Fatu sosai.
Bai kara cewa komai ba ya wuce d'akinsa da ke saman bene amma da ganin fuskarsa zaka gane yayi fushi ne saboda an hanashi magana.
Sai da ya tafi Fatu ta bud'e jakarta ta ga komai da ta zo dashi yana ciki. Wata k'aramar zip dake cikin jakar ta bud'e, ajiyar zuciya ta sauk'e da ta yi tozali da abun da ke ciki. Da hanzari ta mike tsaye tana cewa,
"Hajiya nagode da karamcin da kika nuna mini, amma zan tafi yanzu."
"Mu je in kaiki." Cewar Ammi itama tana mai mikewa tsaye.
Zaro ido Fatu tayi don ba haka ta so ba. Tsayawa ta yi a gurin kamar wacce aka dasa tana kallon Hajiyar na saka hijabinta wanda ke nuni da eh lallai da gaske take.
Narai-narai Fatu ta yi da ido tana mai jin nauyin karyan da ta yiwa Hajiya wacce tun had'uwarsu take ganin girmanta da kuma jin nauyinta. Bata cancanci haka ba, bata cancanci a mata karya a fuskarta ba ko don girmanta, domin Fatu ta yi imanin cewa Hajiya ta haifeta haihuwa ba na d'aya ko na biyu ba, sai dai na hud'u ko biyar.
Daga in da take tsaye Fatu ta zauna a kan kujeran tana ayyanawa a ranta cewa zata fad'awa Hajiyar labarinta watakila ta taimakata mata ta tayata nemo wannan mutumin tunda ta ga kamar nan ne unguwarsu ko kuma yana da wasu wanda ya sani a nan din.
Ganin Fatu ta zauna yasa Ammi jin dadi a ranta saboda da alama ta ciyo kanta, a waje kuma ta tattara fuskarta tamkar wacce ta rasa gane wani abun ta ce,
"Yaya dai na ga kin zauna?"
"Hajiya wallahi ban san in da zan je ba. Hasalima in banda hoto da nake dashi bani da wata kwakkwarar shaida da zai sadani da dan'uwan nawa. Hajiya zan baki labarina ko don ki taimakeni kamar yanda kema Allah ya taimakeki in nemo mutumin da aka d'auramin aure dashi. A halin da nake ciki yanzu ban san Ina zan fara nufa ba, kece kad'ai zaki taimakeni don darajar Allah." Fatu ta k'arishe maganan hawaye na tsiyaya a fuskarta tana kallon Ammi da take mata kallon zallan tausayi.
Zama Ammi ta yi bayan ta cire hijabinta ta dubi Fatu cike da nitsuwa da kuma tausayi muryanta kasa-kasa ta fara magana.
"Tun farko da kika fara bani bakin wai cewa kin zo ne gurin yan'uwanki wanda ma basu san da zuwanki ba naji raina bai kwanta da hakan ba. Mun sha jin labarai a gidan radio da tv ana cikiyar yan mata ire-irenki wanda aka musu auren dole suka wanke k'afa suka gudu cikin birane domin su kaucewa k'addaran aurensu. Sai dai a garin neman ido wato neman y'anci sai ki ga sun fad'a harkar karuwanci, wanda dashi gwara auren dolen sau dubu, tunda wanda kike aure ko a gaban Allah muharraminki ne, kuma idan kinyi hakuri kika zauna sai ki ga hakan yafi miki alkhairi akan ki shigo bariki neman y'anci kai. Duk da ban san me ya faru tsakaninki da wannan mijin naki ba, ki sani da zarar kin fita ke kad'ai nemanshi babu wanda zai lura da aurenki sai dai a miki kallon tsuntsu daga sama gasheshshe. Kina ji na?"
Gyada kai Fatu ta yi, tasan gaskiya Hajiyar take fad'a mata kuma ta godewa Allah a ranta da yasa har Hajiyar ta bugeta da yanzu bata san a wani halin take ba. Wannan shi bature ke cewa, 'blessing in disguise'. Ta yarda kuma ta aminta da ita, fatanta Allah yasa ta taimaka mata wajen cigiyar mijinta.
"Ban san me yasa nake jinki a raina ba, amma haka kawai naji bazan iya barinki ki fita ba tare da masaniyar ina kika dosa ba. Nasan na miki katsalandan, amma kisa a ranki haka kowacce uwa take ji idan taga d'anta ko na wani na shirin fad'awa tarkon masu zalunci. Me ya fito da ke daga garinku Fatu?"
"Zan fad'a miki Hajiya zan fad'a miki komai." Fatu ta ce tana mai zaro wani guntun hoto daga cikin jakanta ta mik'awa Ammi tana cigaba da cewa,
"Wannan shine mijina, shi kuma na fito nema."
Duk sanyin a.c dake falon bai hana Ammi hada gumi ba, Lokacin daya zuciyarta ta fara bugawa da karfi da kuma sauri fat fat fat domin ko a mafarki tasan mamallakin wannan fuskar. Shafa hoton ta yi tana tunanin ko idonta ke mata gizo, amma ko da hannunta ya bar jikin hoton fuskar tasa ta kara tozali da ita. Yana zaune a kan tumin icce ya had'e fuskarsa tamau tamkar wanda aka yiwa albishirin mutuwa, gefensa kuma Fatu ce a tsakure guri daya tamkar a ce kyatt ta ruga da gudu. Yanayin muhallinsu kuma k'auye ne irin futuk din nan, gefe-da-gefensu duk bukkace sai kuma rumbu na ajiyar abinci.
'Me ya kaishi kauye? Ya aka yi yayi aure basu sani ba? Shin shine ko dai wani ne mai kama da shi? Me yake shirin faruwa ne?
"Ya aka yi kuka yi aure da wannan d'in? Tukunna me sunansa?" Ammi ta tambayeta Don har ta fara kawo kokonto a ranta an ya ba gadar zare aka so kulla musu ba da yarinyar nan?
"Sunansa Sultanu, abokinsa yace min unguwar JRA suke."
"GRA, GRA ne." Ammi ta fad'a idonta na kankancewa tsabar 6acin rai da kuma takaicin duniya.
Sharce gumin goshinta ta yi ta ce,
"Shi kuma abokin nasa sunanshi Jamil ko?"
"Eh Hajiya. Wallahi haka sunansa yake." Cewar Fatu da tsananin mamaki a fuskarta.
"Munafukin yaro." Cewar Ammi a hankali yanda Fatu baza ta ji ba.
Har wannan lokacin ita kanta Ammi a cikin duhu take da kuma bakin ciki mara misali, wani gefe na zuciyarta kuma na cikin waswasi, amma ganin hoton nan a hannunta tasan gaskiya Fatu take fad'a. Don su ba yara bane balle a zaunar dasu dole a daukesu a hoto. Kafin ta yanke hukunci zata so ta ji ainihin labarin, me ya kai su kauye har d'ayansu yayi aure basu da labari? Hauka suka fara ko shaye-shaye?
"Me ya faru Fatu? Ki bani labarin me ya faru." Cewar Ammi tana kife hoton a gefenta hankalinta na kan Fatu.
Fatu bata kawo komai a ranta ba ganin canjawar Hajiyan da kuma kama sunan Jamil abokin mijinta da ta yi, gyara zamanta ta yi ta numfasa ta ce,
"Hajiya zan fada miki ko zaki taimaka min in nemoshi in je har gidansu in kuma nemi takardata."
'Dumm' zuciyar Ammi ta k'ara bugawa, ta share gumi da hijabinta dake gefenta ta kad'a kai alamar tana jinta.
Fatu ta bud'e baki ta fara bada tarihin rayuwarta.

FATU A BIRNI (Complete)Where stories live. Discover now