06

3K 231 5
                                    


"Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya tsara wannan halitta." Ya furta a hankali yana mai lalumar hankalinshi da nitsuwarshi wanda ya nema ya rasa a halin da yake ciki.
Sun fi sakan talatin a haka, wanda ganin hakan yasa Fatu fara takawa ta nufeshi.
Tafiya take yi a hankali tana rausaya dalilin karkarwa da jikinta ke yi, shi kuma Sultan ganin hakan yayi a matsayin iya tafiya mai d'auke hankali, ai kuwa ya k'ara malmalcewa da kallonta har ta iso, bud'e baki ta yi da niyyar fad'a masa yanda aka yi ta zo nan don a tunaninta ya ganeta, amma sai ta tsinkayo muryarsa a dodon kunnenta yana cewa,
"Sannnu yan mata." Da kyakkyawar murmushi a fuskarsa.
Tsayawa tayi cakk, ta kalli cikin idonsa da shima ita d'in yake kallo ta yi saurin kawar da kanta.
"Yauwa." Kawai ta iya cewa muryanta a shak'e kana tayi saurin k'ara yin gaba zuwa gurin Mallam Usman.
"Ammi tace tana son ganinka." Kawai ta fad'a don Sultan na kusa da su.
Mallam Usman yayi k'asa-k'asa da murya ya ce,
  "Fatima Yalla6ai ya ganeki kuwa?" (Wai maza ma sun iya gulma.)
Shiru ta yi tana kallon gefe, sannan ta ce,
"Ammi ta ce kar irin wannan maganar yana had'amu Mallam Usman."
Duk'ar da kansa yayi k'asa kamar me neman gafara yana cewa,
"Hakane, Hakane. Ki yi hak'uri, wallahi mantawa nayi, bakin nawa ne ba sakata."
Murmushi kawai ta yi ta juya ta bi hanyar da zai sadata da falo.
Ko da ta zo wucewa wannan karon ma ta gaban Sultan ta zo ta wuce, wanda tun tafiyanta gurin Mallam Usman ya tsaya a gurin ya zuba mata ido tamkar wani maye, shi bai ma san me suke cewa ba.
  Sultan bin Fatu yayi a baya yana k'arewa halittarta kallo har yana mamakin rashin control d'insa, wai nan ma a hakan hijabine a jikinta.
  Ita kuma Fatu k'afafunta ne suka fara hard'ewa don ta tabbatar bayanta yake kallo. Haushinshi ta ji ya turnuketa ta dakata ta juyo tana aika masa wani wawan kallon tsana.
Shi bai ma gane kallon me aka mishi ba amma dai yasan ta gane ita yake kallo.
"Sorry." Ya furta a hankali yana jin d'an kunya. Ta gefenta ya ratse ya shiga cikin falon.
K'amshin jikinshi da kuma na turarensa ne ya bugi hancin Fatu ta lumshe ido tana mai jin wani abu na fisgarta game da Sultan.
Girgiza kai ta yi itama ta bi bayanshi tana mai danne zuciyarta, domin so take ta haramta mata tsohon bege ta ta6a ji game da Sultan.
Tana shiga falo ta isarwa Ammi sak'onta, bata ko kalli in da yake ba ta yi saurin haurawa saman stairs, Sultan da ke zaune a kan d'aya daga cikin kujerun falon ya zubawa bayanta ido a ranshi kuma fad'i yake, duk duniya babu wanda ya kai wannan bak'uwar Ammi iya haura stairs.
Sai da ta 6acewa ganinsa sannan hankalinsa ya dawo jikinsa, kunya ce ta rufeshi da ya had'a ido da Ammi wacce ta zuba masa ido tana masa kallon k'urilla.
"Ammi kamar kin yi magana." Abun da ya iya fad'a kenan yana gyara zamansa cikin jin nauyin Ammi.
"Ya wuce ai. Naga hankalinka baya ma kaina." Tace dashi tana mai canja tashan tv zuwa Arewa24.
Dariyar yak'e yayi don gabad'aya a tsarge yake kamashi da Ammi tayi yana kalla mata bak'uwa.
"Wato tun da abokinka Jamil yayi tafiya shikenan ka d'auke k'afarka daga gidan nan."
Murmushi yayi yana mai sosa keya, ya ce,
"Ammi ban zauna bane wallahi, last week ne ma na dawo daga China, kuma na zo gaisheki Faruk yace kina bacci."
"Haka fa aka yi. Faruk ya nuna mini tsarabarshi, kai kam dai baka gajiya. Allah ya kara bud'i ya kawo mata tagari don kai kam naga alama so kake wannan azumin a fara kad'a maka gangan tuzuru." Ammi tace dashi ciki zolaya.
Dariya yayi sosai ya ce,
"Ammi ki shirya bayan sallah zaku yi bikina, da mun daidaita zan sanar muku."
Ammi ta ta6e baki ta ce,
"A ina ka samu matar?"
"Ai kin santa ma, ki tayani da addu'a kawai."
Ammi na jin haka ta gane da waye yake yi, murna fal a ranta amma a waje ta d'an 6ata fuska ta ce,
"To, ni dai ban gane wacece ba, Allah ya baka sa'a."
Ganin bai samu fuska gurin Ammi ba balle har ya mata tambaya kan bak'uwarta yasa ya maiyar da kallonshi kan tv.
Ya fi minti talatin tare da Ammi suna hira sai dai ko kad'an bata kawo masa tad'in bak'uwarta ba, Fatu kuma ta k'i fitowa. Da ya gaji da jiran fitowarta yayi wa Ammi sallama ya fita zuciyarsa na masa ba dad'i.
  Sultan na fita haraban gidan ya had'u da Faruk ya dawo daga islamiyan safe. Tafawa suka yi yana cewa,
"Big boy soldier, ka dawo? Ya school?"
"Lafiya kalau. Yau mun yi rubutu a allo."
"Ai kana k'ok'ari sosai Soldier, give me five."
Suka k'ara tafawa, Sultan ya sassauto da muryarsa tamkar mai rad'a ya ce,
"Nikam Soldier wacece wannan bak'uwar Ammi wata fara kyakkyawan nan?"
"Umm.. Sunanta Aunty Fatima, Ammi tace ta zo karatu ne a GSU." Ya fad'i abun da Ammi tace ya fad'a da zarar Sultan ya tambayeshi wacece Fatima.
"Daga wani gari take to?" Sultan ya k'ara jeho masa wata tambayar.
"Ammi ta ce daga Bauchi take." Ya k'ara nanata abunda Ammi ta bashi daman fad'i.
Sultan bai samu yanda yake so ba, don ya sone Faruk ya bud'e baki ya fad'a masa komai a kan yarinyar. Shiru yayi ya shafa kan Faruk d'in ya ce,
"Good boy, maza in ka shiga gidan kace ina gaishe da Aunty Fatiman."
Sai da Faruk ya shige cikin gidan sannan yayi ajiyar zuciya.
"Fatima." Ya furta a hankali.
Suna mai dadi ga fuska mai kyau. Murmushi ya yi, ya d'an bugi kirjinsa saitin zuciyarsa. (ko me hakan yake nufi?)
Fita yayi daga gidan, a bakin gate ya had'u da Mallam Amadu yazo kar6an Mallam Usman gadi, suka gaisa ya wuce gidansu.

FATU A BIRNI (Complete)Where stories live. Discover now