chapter 1

1.9K 152 12
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
 
😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

*This novel is 100% fiction, so any resemblance to it should be considered as coincidence*

بسم الله الرحمن الرحيم

01🧛🏽‍♂️
Hankaɗe ta yayi da ƙarfi tayi baya hade da buga kunkumin ta jikin gadon barcin su, ta sake yunƙurawa a karo na biyu zata tashi ya cukumo wuyan ta hade da manna ta da jikin bango yana binta da kallon mugunta sai huci yake yana zazzare idanu saboda tsananin masifa jijiyoyin kanshi da na jikin sa sun tashi rada_rada,

Qara ta sake cike da azaba saboda riqon da yayi mata numfashin ta har neman daukewa yake yi, kuka mara sauti take dan ta galabaita sosai har bata iya magana sai faman girgiza kai take yi,

"Wato Ni zaki mayar mutumin banza ko? Saboda gaki tunkiya ko wani namiji naki ne duk iya ƙoƙarin da nakeyi don kare miki mutuncin ki sai kin saka Ni na gaza, kinyi tunanin zakiyi min wayo dake da ɗan iskan saurayin ki ku yaudare Ni a gaban ido na kuma ban gane ba?"

Da qyar ta iya bude bakin ta cikin ginin kuka tace "khamis wallahi ba saurayi na bane kawai diban jini na yayi, Ni babu komai tsakani na dashi ka yarda dani"

"Babu komai tsakanin ki dashi shine bayan na nemo nurse mace ta dibi jinin kin kika kirashi yana tattaba hannun ki Kuna jin dadi sannan zaki fake da ɗiban jinin ki yake ko? Bari kiga abinda zanyi miki gobe ba zaki sake gangancin raina min hankali ba" ya fita a fusace fuuu,

Daga murya tayi cikin kuka tana qwala mishi kira "khamis! Khamis dan Allah kayi haquri na tuba wallahi" saboda tasan irin abinda zai iya aikatawa,

Bai bata lokaci ba ya dawo hannun shi dauke da vacuum plask Wanda ta zuba tafasasshen ruwa dazu da safe kafin su tafi asibiti, ya qaraso wurin da take zaune yana bude marfin plask din,

Zaro Ido tayi cike da tsoro ta fara ja da baya_baya tana "dan  Allah kayi haquri" Amman  Bai saurare ta ba ya sunkuya ya riqo hannun ta na dama "ina wannan hannun ya taba? Wannan hannun da nake matuqar so kika bashi dama ya taba qazamin jikin shi?"

Kwarara mata ruwan yayi a wrist dinta a zabure ta miqe tana sakin ihu cikin radadi da azaba ta fettu gefe tana diddirje wurin da hannun ta na hagu ko zata samu zafin da take ji ya ragu aikuwa saiga fatan wurin ya tattare garin sosawa ta kwaile shi,

"Wannan shine hukuncin ki na yau, bazan taɓa lamuntan iskanci ba kina da aure Amman Baki san mutuncin kanki ba, to bari kiji Ni ba sakarai bane kuma Ni kadai na biya sadakin ki na aure ki dan haka ke tawa ce Ni kadai duk wanda yayi ƙoƙarin shiga tsakani na dake sai na kawar dashi, kuma shi wannan ɗan iskan zaisan ya tabo matar khamis wallahi! Billahi!! Daga yau ba zai sake kwana a duniyar nan ba sai na kashe shi dan uban shi"

Ya ja qofar dakin da qarfi ya rufe da key ta waje tana jin fitan shi yanda ya kulle qofar parlor da qaran fitar motar shi ta kulle gate din waje,

Kuka ta sake sakawa tana nadaman auren khamis a karo na babu adadi, tayi danasanin yarda dashi tayi danasanin amincewa da soyayyar shi khamis ya lalata mata rayuwa data sani da ta ɗauki shawaran A'isha da duk hakan bai faru ba,

Ya saka ta rayuwa cikin qunci da wahala, tunda ya auro ta dauko ta daga Adamawa ya kawota Birnin Kebbi ya bude mata babin azaba saboda baqin kishi, ya hana ta riqe waya wai dan kada ta kira namiji ya hana ta kallon TV saboda kada ta ga namiji, tunda sukayi aure sai ɗaya taje gida shima wuni ɗaya tayi ya dawo da ita saboda yayun ta da qannen ta duka maza ne ita da qanwar ta guda daya ne kawai mata, babu ziyara, babu ta'aziyya, babu gaisuwan mara lafiya, babu Barka, babu suna rabon ta da fita gate kafin yau da suka je asibiti da safe har ta manta, khamis ya gama lalata mata rayuwa ta *tsane shi!!!*

🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ Yanzu muka fara tafiyar🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ zamu garin nisa😂
Insha Allah zan dinga ƙoƙorin update akai_akai Amman posting kullum sai na gama *kama da wane* insha Allah

Kuci gaba da bin alqalamin Ummu Najma, masoya na ina alfahari daku matuqa🤩💝

Don't forget to follow me and vote for my stories on Wattpad @ayeeshatmuhd ✔️

Aci gaba da gashi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

MATAR KULLE(Short story)Where stories live. Discover now