(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
😈 *MATAR KULLE* 😈_(Thriller)_
_Short story_
©️2020 specialтнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Blog : prowritersnovels.blogspot.com
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*24🧛🏽♂️
Ihu mai tsananin ƙara na ƙwalla cikin firgici da tsananin tashin hankali na diro daga kan gadon na ƙarasa jikin gawar khamis ina jijjiga shi da iya ƙarfi na kaman yanda ko wani lokaci nake ganin inayi a cikin mafarki ina kiran sunan shi da ƙarfi ko zan samu ya farka,Mutumin da ya kira kanshi da kunama ne ya ƙaraso wurin da nake durƙushe ya tsunguna tare da saita min bindigan da ya kashe khamis dashi a ƙirji na, ya saka yatsan shi daya a saman lebben shi yana furta "shhhh" alaman nayi shiru na daina ihun da nake yi,
barin ihun nayi na dawo sai kuka, inayi Jannat tana yi ina kallon kunama da jajaen idanu na zuciya ta fall da tsoro,
Dariyan mugunta yayi mai sauti yana gwada ni ma abokin ta'addancin shi da suka shigo tare shima yana taya shi darawa, ɗan tsagaitawa yayi ya tambaye ni da
"Yusrah sunan ki ko?"Shiru nayi ban amsa ba naci gaba da kuka na ina kallon jinin dake kwaranya daga jikin Khamis, da ya daka min wata uwar tsawa ban san lokacin da na gyada mishi kai ba shiri ba,
"Hakan yayi kyau, nasan kina son sanin cikakken bayani akan dalilin da yasa na kashe mijin ki da kuma asalin wanda ya kashe wato ɗan uwa na cinnaka ko?"
Shina gyada kai nayi ba tare da na san nayi hakan ba, yace
"Yayi!!! To shi dai cinnaka ƙani na ne uwa ɗaya uba ɗaya kuma magajin gadon mulki na na daba, kullum buri na bai wuce idan na fadi cinnaka ya hau ya zauna ba ya amshi sunan kunama kuma hakan ne yake faruwa yana iya bakin ƙoƙarin shi wajen ganin sunan shi ya zaga ko ina ya zama abin tsoro,Saidai kuma daga baya ban san abinda ya faru ba, wani malami yayi wa cinnaka wa'azi kuma ya dauka ya tuba ya canza halayen shi da sunan shi, abokan mu'amalan shi, harma da dabi'un shi, kwata_kwata banji daɗin hakan ba amman babu yanda na iya dole na rungumi cinnaka a duk inda yazo min domin shi kadai ya rage min jini na a duniyar nan, iyayen mu an kashe musu tun kafin su an mu yayi ƙauri lokacin muna saran ka kashe a kashe maka, daga baya ma suka kashe ƙanwar mu mace ɗaya tilo,
Saidai rayuwa bata zo ma cinnaka da sauƙi ba bayan tuban shi a garin adamawa, yana fiskantar tsangwama da kyara ko hada sahu dashi ba'a yi a masallaci duk inda ya ratsa ko kuma ya zauna haka zaki ga mutane suna darewa basu son zama kusa dashi shiyasa ya yanke shawaran canza wurin zama can nesa da garin Yola yanda zai shimfida sabuwar rayuwa,
Ni da kaina na zaba ma cinnaka garin da zai je Kebbi kenan nasa aka kama mishi sana'a aka bashi jari yana ta fafutukar canzawa zuwa cikakken kamilin mutum harda tara gemu da ƙasumba amman rana tsaka, wannan daƙiƙin mijin ki mahaukaci yaje har gidan da yake zama ya farr mishi, haka aka kawo min cinnaka yana ƙaƙarin mutuwa cikin jini kaman yanda mijin ki yake kwance a yanzu,
A hannu na ina kallo cinnaka ya mutu ko damar maganar ƙarshe ban samu yi dashi ba, bai fada min wanda yayi masa wannan aika aikan ba amman na saka yara na su bincika min kuma idan kere na yawo zabo na yawo wata rana dole su hadu, na san dole zan hadu da makashin cinnaka kuma na ɗau mishi fansa,
YOU ARE READING
MATAR KULLE(Short story)
Short Storythere is no marriage without love, so also no love without trust, but jealousy have overpowered KHAMIS love, that he tortured his wife YUSRAH to the extent that she can't endure it anymore, will he become a good man and ask for her forgiveness? or s...