(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
😈 *MATAR KULLE* 😈_(Thriller)_
_Short story_
©️2020 specialтнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Blog : prowritersnovels.blogspot.com
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*26🧛🏽♂️
*Wurobokki village*Duk abinda yake yi yana bayani ma yaron shi kuma ya zuba ido da kunne yana kallo yana sauraro, yana cire bullet ɗin ya zuba wani abu tsalalo kaman ruwa ya goge wurin tass sannan ya saka zare da allura ya fara dinke wurin,
Basu dauki lokaci mai tsawo ba ya gama mishi ɗinkin ya saka bandage ya zagaye kunkumin shi dashi yanda zai rufe ciwon sannan suka koma kan raunin shi dake kai, wannan karon ma yaron ya bada aikin yana yi yana masa gyara kuma yana ƙara guiding dinshi har ya gama ya naɗe kanshi yanda germs ba zasu sauƙa kan ciwon ba sannan yaron mai suna Jaɗe ya fita da kayan da sukayi aiki dashi domin tsaftace su,
Mahaifiyar Jaɗe ne ta shigo da sallama ta ajiye mishi garwashin wuta a cikin kasko mai ɗan girma sannan ta fita ba tare da tayi wani magana ba ko kuma ta tambayi waye mutumin da suka shigo dashi, dan ta saba da hakan aikin mai gidan ta ne jinya ma marasa lafiya,
Wani kullin magani ya dauko ya ɗibi kadan ya zuba a cikin wutan, ya ɗebo wasu itacuwa ƙananu ya zuba, a haka saida ya haɗa magani kusan kala 5 duk hayaƙi ya gauraye dakin, yana zaune yana daɗa duba jinkin shi jaɗe ya dawo da cup din ƙarfe mai dauke da ruwa da kuma wasu mutattun yadi da sun gama yin laushi riga daban wando daban,
Miƙa wa mahaifin shi kayan yayi, sai ya karbi wando zallah yace ya maida rigan babu musu kuwa ya ajiye kofin ruwan ya koma da rigan a hannun shi, mutumin ya saka aska ya farke rigan jikin shi harda singlet ɗin ciki sannan ya sauya masa wandon jikin sa, ya ɗauki ruwan kofin yayi addu'a a ciki sosai sannan ya shafe masa fuskar sa da ƙirjin shi dashi yana gamawa shima ya fita tare da sauƙe asabarin ƙofar dakin,
Sallamar da yaji ana kwaɗawa a kofar gidan ne yasa fuskar shi sauyawa zuwa yanayi mai muni, daga gani baiji daɗin zuwan wanda yake sallamar ba, jaɗe ne ya ƙaraso wurin da yake tsaye ya dauki sandar sa dake jikin ɗakin da suka kwantar da mutumin ɗazu ya ɗaura saman kafadar shi yace
"Baba hara naje nace mata bakki na, nashan gulma ce kawai ta kawo ƴar Laraba""A'a ɗan nan, bari naje na shame ta naji yau kuma dame tajo kada kuma aikan mai gari ne, nashan ba jai wucce a kan maganar baƙuwar nan da muka sinto gaɓar ruwa ba"
Da fadan haka ya zura takalmin shi ya fita wurin ɗan Laraba a ƙofar gida, kaman mutumin arziƙi ya bashi hannu suka gaisa sai washe haƙwara yake yi gulma yau tayi kasuwa,
"Malam Arɗo, mai gari taa aiko ni na gaya maki tana shon ganin ki a fada yanjun nan"
"Ƴar Laraba fatan dai laafiya koo?"
"Kin shan dai maganar guda ɗaya ce kullum, boɗɗi ce ya shake racin ɗa'a wa mai gidan shi yarima to shine don kada a koro miki ɗan ki ba tare da kin shan abin da yake faruwa ba mai gari tace a nimo ki, kinga nan ƙafa ta ƙafar ki"
Sauƙe ajiyan zuciya malam Arɗo yayi don baiyi tunanin abin kenan ba, lokacin da suka tsinto baƙon nan a bakin ruwa da suka zo wucewa da shi tabbas ɗan Laraba ya gansu shiyasa yayi tunanin har yaje ya kai rahoto gaba ne,
YOU ARE READING
MATAR KULLE(Short story)
Short Storythere is no marriage without love, so also no love without trust, but jealousy have overpowered KHAMIS love, that he tortured his wife YUSRAH to the extent that she can't endure it anymore, will he become a good man and ask for her forgiveness? or s...