(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
😈 *MATAR KULLE* 😈_(Thriller)_
_Short story_
©️2020 specialтнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*
*The writer of*
*HAR ABADA* and
*KAMA DA WANE*14🧛🏽♂️
Qanqameni yayi a jikin shi Yana kuka kaman qaramin yaron da za'a raba shi da uwan shi Yama kasa magana sai ihu yakeyi irin na bebaye Yana da'da cukuikuye ni, burin shi bai wuce kada a raba ni dashi ba, ni kuwa Ina tsaye qyamm kaman gunki na kasa tabuka komai Khamis is now my biggest weakness,da qyar aka zo aka banbare shi daga jiki na wasu qattin maza majiya qarfi su uku suka tattara shi suka nufi hanyar waje dashi Amman Saida yasan Yanda yayi ya qwace ya sake kwasowa da 'dan iskan gudu zai riqe ni baba na ya Shiga tsakanin mu ya taqarqare ya zabga ma Khamis Mari,
Shi kuwa ko a jikin shi kaman bashi aka daka ba, ya saka dukkan qarfin shi ya hankada tsoho na gefe ya sake riqo ni abinda yayi ma baba yayi min zafi shiyasa Nima nayi amfani da sauran qarfina na ture shi sannan na juya da sauri zanbar court room din yasha gaba na tare da hade hannayen shi biyu,
"Please, please, please kada ki rabu dani wallahi na fada Miki bazan rabuwa dake ba duk inda Kika je Zan biki faaa wallahi sai na biki, Babu inda Zan tafi na barki, eh wallahi Babu Wanda ya Isa ya raba mu tamm zanyi kisa wallahi zanyi kisa a kanku kizo mu tafi gida kinji na fada miki" Da sauri_sauri yake maganar, kana ji kasan zautacce ne ba'a cikin hankalin shi yake ba,
Hannu na ya riqo zai jani mu tafi Amman sai ya tsaya cakat na 'yan sakwanni sai Kuma ya zube a qasa ragwab sakamakon alluran da suka danna mishi a wuya, muna kallo aka tattare shi aka saka shi a mota sai a lokacin kuka yazo min na fita da sauri sukabi baya na, ban tsaya sauraran Kiran da suke min ba don bani son gwada ragonta na a bainar jama'a na qarasa bakin titi na tsari napep ba tare da munyi ciniki ba na fada mishi wurin da ze kaini na fada ciki mukayi gaba,
Duk iya Yanda naso nayi controlling kaina Saida kuka yaci qarfi na har Jin kaina nakeyi Yana mugun Sara min kaman ana daba min adda, I cried my eyes out kafin mu Isa gida tausayi na sosai ya Kama me Keke Yanda na birkice na fita hayyaci na ga tsohon ciki shiyasa Yana ajiye ni ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya karban kudin shi ba,
Da Kama garu na Shiga gida har wani zazzabi naji Yana Shirin rufe ni, ga ciwon ciki da na baya na Shiga dakin mu na Danna kwado ta ciki Dan a irin wannan lokacin bani buqatar kowa a tare Dani, zama nayi daram a qasa akwai sanyin floor inajin Yana ratsa ni amman ban damu ba na hade Kai da guiwa Ina risgan kuka harda majina,
Inajin dama ace duk wa'innan abubuwan da suka faru mafarki ne, da kuwa idan na farka bazan sake komawa cikin sauqi ba, cikin wannan yanayin su mama suka shigo suka same ni harda mahaifiyar Khamis da Aisha da ya Safwan, tun daga waje suke jiyo sautin kuka na sunyi bugun duniyar Nan naqi na bude musu qofa bani ma Jin Zan iya dan qabobi na gaba daya sun mutu,
"Yusrah dan Allah kiyi haquri haka Nan ki bude qofar kada ki cutar da abinda ke cikin ki bai Kamata laifin Khamis ya shafi 'danshi ba kin riga kin dauki fansar abinda Khamis yayi Miki burin ki ya cika kin lalata mishi rayuwa yanzu abinda ke cikin ki shi kadai ne abinda nake dashi Wanda ya dangance shi dan Allah kada ki cutar da kanki" cewar mahaifiyar shi Kenan,
YOU ARE READING
MATAR KULLE(Short story)
Historia Cortathere is no marriage without love, so also no love without trust, but jealousy have overpowered KHAMIS love, that he tortured his wife YUSRAH to the extent that she can't endure it anymore, will he become a good man and ask for her forgiveness? or s...