(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
😈 *MATAR KULLE* 😈_(Thriller)_
_Short story_
©️2020 specialтнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Blog : prowritersnovels.blogspot.com
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*21🧛🏽♂️
I was Shocked!!! Stunned!! Khamis ne tsaye a gaba na, ta yaya akayi ya fito daga psychiatry?? Wani kyarma jiki na ya fara yana tsuma purse dina da key din motar ya Safwan dake hannu na duka suka zube,Ɗan qaramin murmushi yayi ya ɗaga hijab dina yasa hannun shi yana shafa ciki na, "baby ina ciki na? Kin aife shi ko? Yanzu na samu qaramin baby kenan, yana ina? Ko mace ce?
Duk maganar da yake yi ban samu daman amsa shi ba ko sau daya, jiki na banda ɓari babu abinda yake yi, ɓata rai yayi ya matsa fatan ciki na da qarfi har saida na saki ƙara yana "ba zaki min magana bane?"
A maimakon na bashi amsa kawai na fara convulsion kaman wata mai farfadiya, na fita a cikin hayyaci na gaba daya ina ƙame ina shaking, dariya yayi mai sauti wanda ban ma san yana yi ba yayi min peck a lips yana fadin
"That's my lovely wife, yanzu na tabbatar da kin tuna da ni, so I'm back kuma ɗaukan ki zanyi da baby na mu tafi can nesa mu ci gaba da rayuwa like we used to be before, all...alone"Sai ya sake bushewa da dariya, just then ya Safwan ya fito daga store din dauke da Jannat a hannun shi idanun shi suka sauƙa a kan khamis, shima saida abin ya firgita shi gani na tare da khamis ina tsaye sai shaking nakeyi kaman wanda aka saka wa shocking, daga murya yayi yana kiran sunana jin haka yasa Khamis daga ido ya kalle shi, ya maido da duban shi wuri na sannan ya nuna shi da yatsa yace "wannan kuma fa?"
Bani da damar da zan iya magana na gama hada zufa ina kallon shi, ya cukumo ni ya manna ni da ƙirjin shi tare da zare min idanuwa cikin ƙaraji yace "me ya hada ki da wancan mutumin Yusrah?? Da auren nawa a kanki wani gardi ya samu daman kiran sunan ki?"
Cikin sassarfa ya safwan ya qaraso gudun kada Khamis ya cutar dani, da ɗaya hannun shi ya bugi kafadan Khamis ya bude baki kenan zaiyi magana Khamis ya kai masa psychiatric punch😅 saida ya kusan zubewa a ƙasa take hancin sa ya balle da jini, Khamis ya sake taƙarƙarewa ze kai mishi lunatic punch a take hankali na ya dawo jiki na nayi saurin qarasa wurin su da ƙarfi nace
"Khamis ka bari dan Allah kada ka cutar da ƴarka"Tsayawa yayi hannun shi na reto a iska shi bai kai naushi ba kuma bai sauqe ba yana kallo na cike da mamaki har na qarasa na karbi Jannat a hannun Safwan sai zunduma ihu take taga tashin hankalin da tun da na aifota duniya bata taba ganin irin shi ba,
Har wasu hawaye ne suka kwanta a cikin idon shi jijiyoyin jikinshi sun tashi rada_rada, da muryan bacin rai da takaici yace
"Yusrah yanzu har wani ya samu damar dora hannun shi a kan ƴata da sunan kina tare da shi? Ya maye gurbi na fa kenan!!""B...ba...ba hak..ka bane fa..kh.."
"To idan ba haka bane menene??" Ya fada cikin tsawan da ya kaɗa hanjin ciki na, harta kukan Jannat saida ya tsaya cakk, ganin kaman fada akeyi a wurin da muke tsaye yasa securities din dake gadin store din suka nufo mu amman kafin su ƙaraso ya Safwan yayi yunƙurin maida ma Khamis raddi amman kashh!! Ya tafka babban kuskure,
YOU ARE READING
MATAR KULLE(Short story)
Short Storythere is no marriage without love, so also no love without trust, but jealousy have overpowered KHAMIS love, that he tortured his wife YUSRAH to the extent that she can't endure it anymore, will he become a good man and ask for her forgiveness? or s...