(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
😈 *MATAR KULLE* 😈_(Thriller)_
_Short story_
©️2020 specialтнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Blog : prowritersnovels.blogspot.com
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*12🧛🏽♂️
Baice dani koman ba ya zaunar dani a kujera, sannan ya warware bandage din da na Nade qunan dashi ya dauko maganin da ya siyo ya fara shafa min, rintse idanu na nayi saboda radadin Yanda Khamis yake murtsuke min ciwo da sunan shafa magani Amman a hakan sai maimaita "I'm very sorry baby" yake yi,I hate him! Na tsani Khamis to the core, that maganar da yake min yanzu jinta nakeyi kaman fitar wuta daga kogo, haka ya Gama jagwalgwala min hannu sannan ya kwantar dani a Kan kujeran,
"Yusrah har yanzu baki haqura bane?" Ya tambaya cikin muryan shi ta nutsuwa Mai tsananin firgita ni, Baki na Yana rawa nace
"Aa Na haqura""To bude idonki ki kalle ni"
Ko rufe bakin shi baiyi ba na ware idanu na a kan fuskar shi that I hate so much, murmushi ya saki Yana shafa gefen fuska ta a hankali yace
"That's my lovely wife, Ina sonki Yusrah"Shru nayi bance komai ba, wurge ni da wani mummunan kallo tare da hade fuska yace "ba Zaki bani amsa b...."
"I love you too baby"
Dariya yayi ya Kai min peck a cheeks dina Ya cire dankwali na Yana shafa gashin kaina da rabon shi da yaga kitso har ya manta, saidai na wanke na tace Dan bani da nutsuwan yin ko kalaba ballantana stretching,
"Na sani baby, and kada ki damu ciwon Nan Yana warkewa Zan Kira doctor har gida gazo ta duba min ke kinji?"
Da sauri na gyada Kai tare da miqewa, bansan meyasa ko yaushe idan Ina tare da Khamis jiki na yake rawa ba Amman yanzun ma haka ne, bari nakeyi kaman Wanda tayi wanka da qanqara, shima miqewa yayi yana tambayan "Ina Zaki je?"
"Fitsari nake ji zanje toilet ne"
" To muje na raka ki Kinga ma Baki da lafiya"
Gaba nayi ya bini a baya muka Shiga toilet Ina gamawa ya dauko ni cakk ya dire ni kan gado saboda Babu wuta ya dauki mafifici Yana fifita ni har barci ya dauke ni Sannan ya fita ya rufe qofar da key ta waje, kofar parlor ma ya Danna Mata key, gate ma Saida ya rufe shi gamm sannan ya tafi,
2:08 na farka cikin hukuncin Allah ciwon hannu na bai cabe ba, har Baki bakin yayi duhu kaman Yana Shirin fara bushewa, amman zazzabin da na tashi dashi da safe ya dawo sabo jiki na yayi zafi rau, ga baqin kasala ji nake yi kaman bazan iya taka qasa ba saboda Yanda jiki na yayi min nauyi,
A haka na daddafa jikin bango nabi na Shiga toilet na dauro alwala sannan na fito na shimfida sallaya na tada Sallah, Ina cikin addu'a Khamis ya shigo ya zauna gefe na yayi shiruu Yana qare min kallo har Saida na kammala, tashi nayi na koma gado Ina rawan sanyi cike da tausayawa ya dauki blanket ya lullube ni sai jero min sannu yake yi sannan ya fita,
Shigowa yayi dauka da takeaways na abinci a cikin laida sai Kuma plate da cokali, ya ajiye a qasa ya fita ya dauko ruwa da cups, sannan yazo ya daga ni ya zaunar Yana feeding dina, spoon biyar nayi nace na qoshi lokaci daya yanayin Khamis ya canza 'dan lallabi da tarairayan Nan duk ya watsar dashi ya danqo ni Yana dura min abincin Nan da mugunta har Saida na cinye takeaway guda Ina Jin kaman ciki na zai fashe tukunna ya sake ni,
YOU ARE READING
MATAR KULLE(Short story)
Short Storythere is no marriage without love, so also no love without trust, but jealousy have overpowered KHAMIS love, that he tortured his wife YUSRAH to the extent that she can't endure it anymore, will he become a good man and ask for her forgiveness? or s...