chapter 5

563 84 2
                                    


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

*Masu complaint din a qara yawan typing kuyi min haquri, typing novels biyu a lokaci daya is not an easy task, Ina Gama rubuta KAMA DA WANE komai zai daidaita insha Allah saboda yanzu shi na saka a gaba,*

*Thanks for the love and support💝 love you so much 💞*

05🧛🏽‍♂️
Kallo kawai nake bin Aisha dashi har ta gama kwararo baya Nan ta Sannan na ja dogon tsaki "wallahi kinban kunya ban taba tunanin hassadan ki har kaina zai hau ba, kina baqin cikin Zan Riga ki aure shine kike so ki 'bata Khamis a Ido na daga baya ki lallaba ki aure min shi ko? Allah ya Isa tsakani na dake Aisha Kuma ni ba irin mutanen dake daukan jita_jita bane ballantana kiyi tunanin qarairayin ki zasuyi tasiri a kaina"

Tsananin mamaki da firgici sun Hana Aisha magana, tayi sakare tana qare min kallo Bata taba tsammanin haka daga gareni ba, ban ankara ba sai naga hawaye zirrr a fiskar ta na sake Jan wani tsakin qasa_qasa Yanda nasan zata jini nace "munafurci kawai"

Muryar ta har sarqewa yake yi saboda takaici da qyar ta iya furta "Yusrah haka Zaki ce? Yanzu idan ma zanyi hassadan sai nayi Miki? Me kike dashi me akayi akayi Khamis da zanyi Miki hassadan auren shi??, I just care about you saboda ke aminiyata ce idan na Bari wani abu ya sameki Bayan inada halin karewa Allah bazai barni ba that's it"

" You are lying maqaryaciyar banza kawai, wallahi tun ranar da na hadu da Khamis na lura da take taken ki, I regret calling myself your best friend tunda amintakar ki batai min Rana ba inda ace bansan me wacece bane Kuma bansan sirrikan ki ba to shine, nasan you are desperate to get married saboda buqata da kike dashi Amman ba hakan na nufin sai kinyi min qwacen Khamis bane Zaki samu kiyi aure, go and find a guy for yourself babe, qeace Bai dace dake ba kwata_kwata"

" Sanin kanki ne cewa ba rasa mijin aure nayi ba, yeah! Na yarda nayi babban kuskure da na bude Miki ciki na Amman kinsan da ace da gaske auren nake son yi ba Zan nemi Khamis ba, ban rasa samaruka ba ban rasa mijin aure ba ke kanki shaida ne a kan haka, Kuma Koda ace na rasa kalma daya Zan fada wa mahaifi na zai kowa min mazaje har gida sai Wanda na zaba, Wanda suka find Khamis asali, dukiya, haduwa da Kuma cancanta ni wallahi ko a qafa aka daura min Khamis Zan since na Yar"

Shewa nayi hade da tafa hannuwa Dan babu qarya Aisha ta bani dariya, tana kuka Amman ita Wai dole sai ta cakka min maganar da zai saka na rabu da Khamis Bata San kuwa ta makaro ba domin ni da shi Mun Riga Mun zama hanta da jini rabamu sai mutuwa,

"Aishatu kenan da Baki samu irin khamis din bane kike cewa idan aka daura miki shi a qafa Zaki Yar Amman wallahi tallahi ba zanyi kaffara ba da Khamis zai Budi Baki yace Kee yake so Babu abinda zai saka kiqi amincewa Kuma ki aure shi a lokacin ba tare da sani na ba"

"Shikkenan Yusrah bazan zauna Bata yawun Baki na Ina musu da ke ba, Ko zamu samu sabani banyi tunanin namiji bane zai Shiga tsakanin mu Yusrah saboda irin son da nake Miki yasa na tilasta mahaifiyata tayi amfani da kudin da za'a canza min system harda qarin nata a kai tayi hiring detective ya bincika Mana Khamis ciki da waje Amman gashi kin watsa min qasa a Ido thank you so much, Babu komai kin nuna min matsayi na da iyaka ta Kuma nayi kuskure da na tsallake shi Kinga tafiya ta" ta dauki jakarta tayi hanyar fita,

MATAR KULLE(Short story)Where stories live. Discover now