chapter 25

432 78 21
                                    


(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
 
😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

*Ina miƙa saƙon ta'aziyya ta ta bogi zuwa ga ƴan team khamis, inyi muku na Antimee tace Allah ya ƙara nauyin ƙasa,🤭 ah to nidai bani na fada ba😅*

*Sannan sauran wa'inda sukayi comment jiya ban amsa ba suyi haƙuri dan Allah ba ƙyaliya nayi muku ba WhatsApp dina yayi expire ne a maimakon nayi updating dinshi sai nayi deleting na sake downloading wani, domin idan nace zan bari yayi restoring messages din suna da yawan da zasu iya kawo min matsala a wayan, afwan Please🙏*

*Thanks for the love MATAR KULLE fans, ina sonku irin har cikin jini na ɗinnan* ❤️❤️❤

25🧛🏽‍♂️
Daga wurin gida ya Safwan ya maida ni gawar khamis kuma aka kai gidan su, baba da sauran yayu na suna tsaye a bakin ƙofa lokacin da muka isa saboda tun a hanya ya Safwan ya kira su ya fada musu abinda ya faru,

Saboda Jannat dake hannu na har ya Safwan yayi parking ban motsa ba saida ya fita ya zago ya bude min ƙofa, ɗaga rinannun idanu na nayi na sauƙe su a kan fiskar baba lokaci ɗaya hawayen da nayi ƙarfin halin riƙe su suka sami daman gangarowa saman fuska ta, yaya na wanda yake bin ya usman ya dauke jannat daga kan cinya ta ya riƙe ta a wurin shi,

Baba baice komai ba ya kama hannu na ya jani a hankali har zuwa cikin gida mama da Nasreen kaman jira suke yi ina shiga suka rungume ni suna taya ni kuka,
" A kan ido na suka kashe shi mama sun zalince ni, sun cutar dani" shine kalmar da ya fito daga baki na,

Ƙara ruƙunƙume ni mama tayi tare da runtse idanuwan ta hawayen tausayin ƴarta masu zafi suna sauƙa a saman kuncin ta, innalillahi wa inna ilaihirraji'un take maimaita min cikin kunne na ko zan samu na riƙe amman bani ma ɗa ƙarfin magana,

**********
Maman Khamis firr taƙi ta kalli gawan da aka shigo dashiba matsayin na Khamis, rikicewan da na gani a fuskar mahaifin shi bayan yayi arba da gawan ne ya ruɗa ni amman sai naga Ya safwan ya jashi gefe suna magana ƙasa_ƙasa, daga farko sun fara kaman zasu yi hargowa daga baya kuma ban san me safwan din ya fada mishi ba naga sun daidaita, (to me hakan yake nufi? Oho!)

Shigar da gawan aka yi aka wanke shi aka suturta shi sannan aka saka a kan makara aka fito dashi domin yi mishi Sallah, kada kuso kuga tashin hankali a gurin mahaifiya mai ƙaunar ɗanta wanda bata bari yayi nisa da ita gashi yau za'a raba ta dashi dole, da suka fita haka ta zauna dabas a ƙasa tana kuka mai ban tausayi,

Bayan an gama komai an taru ana zaman makoki sai ga Yusrah yaya safwan ya kawo ta tare da jannat, tana sauƙa daga motan ta tsaya tana ƙare musu kallo an zauna anyi jingum_jingum, safwan ma tsayuwa yayi yana kallon ta don ce mishi tayi ya kawo ta akwai abin da take so ta fada,

Bata ce wa mutanen wurin komai ba da ɗan gudun ta tashiga cikin gidan ta bar Safwan tsaye da yarinya a hannu, tana shiga ciki ta dinga kutsawa tsakanin mutane batabi ta kan masu yi mata ta'aziyya ba ta wuce wurin da ta hango maman Khamis tana risgan kuka ta tsunguna a gaban ta murya can ƙasa yanda babu wanda zai ji tace,

"Mama ki daina kuka Khamis yana raye bai mutu ba, na manta ban fada miki ba gawan nan ba nashi bane"

Ɗagowa tayi a firgice tana kallo na yanda na fada mata maganar cikin qwarin guiwa alamun gaskiyar shi tun daga zuciyata ta fito, lallai ta yarda na zauce firgicin mutuwar Khamis ya shiga jiki na domin idan da cikakken hankali na ba zanyi irin wannan maganar ba"

Riƙe hannu na tayi ta saka kuka tana fadin "Yusrah haƙuri zakiyi dukkan mai rai mamaci ne"

Saurin fisge hannu na nayi raina a bace, ta yaya za'ayi ace mahaifiyar Khamis bata gane gawan ɗanta ba? Duk da cewa nima ba kallon ƙurilla nayi ma gawar da aka ciro ba amman ina da tabbacin ba na Khamis bane,

Wannan karon cikin ɗaga murya nace "wallahi mama na fada miki Khamis bai mutu ba gawan nan ba nashi bane, ba kalan kayan da suka kashe shi dashi ba kenan, Khamis bai cika saka fararen kaya ba bayi ma son farin kala sosai kuma gawan nan da farin kaya a jikin shi, kice ma mutanen nan su tashi su tafi Khamis bai mutu ba"

Tsagaita kukan ta tayi tana ƙoƙarin calming dina na daina hayagagan da nake yi kada na jawo hankalin jama'a zuwa gare ni, amman inaa yanda take taro ni haka nake bauɗewa, daga ƙarshe na dawo ihu kaman anyi ma kirista mutuwa, har maza dake zaune a waje suka shishshigo,

bani son ma jin naji an ambaci sunan Khamis an danganta shi da sunan mutuwa don ina ji a jiki na khamis yana raye bai mutu ba idan ma sunce ya mutun basu da hujjan da zasu gwada na an sami gawan shi tunda ni dai ko wuƙa zasu saka min gawan nan ba na Khamis bane,

Daga ƙarshe yayu na aka kira da taimakon ƙannen shi mata suka kwashe ni a wurin da na duƙufa ina kuka kaman raina zai fita, akan me zan fada musu Khamis bai mutu ba suƙi yarda? Ba ni bace matar shi kuma ko yaushe nake tare dashi, ko siffofin jikin Khamis duk na fisu sani so idan nace musu ba shi bane ya zamo dole su yarda amman sunƙi yarda,

Da muka isa gida ma saida suka rirriƙe ni kafin aka shigar dani gida na gama dawowa kaman ƙaramar mahaukaciya, a daki suka saka ni suka rufe tare da mama tun lokacin Jannat ta koma marainiyar ƙarfi da yaji tayi shiruu tana bin mutane da ido ga yunwa sosai a cikin ta amman ko ta kanta bani bi,

Mama ta kada ta rawa ta fahimtar na gane cewa mutuwa gaskiya ce na rungumi ƙaddara ni kuwa nace fyattt ban san da wannan zancen ba Khamis yana nan da rai,

**********
Shigowa suka yi cikin gidan wanda yake na ƙasa rungume da mutum daga gani bayi cikin hayyacin shi , suka wuce cikin bukkar dake bakin ƙofa suka kwantar dashi saman gadon kara, sannan ɗaya daga cikin su ya fara duba gudun jinin shi ta hanyar amfani da yatsan shi yana matsa wrist dinshi,

Yayi hakan da sauran gwaje gwade na kusan 7 minutes sannan ya ɗago yana duban ɗayan mutumin cikin hausan shi mai rauni yace
"Ɗan nan karbo min jaka ta wurin hinde"

Da "toh baba" ya amsa sannan ya fita, bai dade ba ya dawo da jaka irin na fata ya miƙa mishi, shi kuma ya kunna wuta a aci balbal ya ciro wasu qarafuna ya ajiye, ɗaya daga ciki mai baki kaman kwarashi amman baki biyu yake dashi ya saka a jikin aci balbal din ya ƙona bakin abun sosai sannan ya tsoma a cikin ruwa ya ɗaga rigan mutumin tare da yin bismillah yasa a daidai wurin da harbin bindigan yake ya ciro bullet...........🤦🏻‍♀️

_Kuyi haƙuri da gajercin page ɗin yau, ina ɗan bincike kan wani abu ne ban samu kammalawa ba, amman gobe zanyi posting sau biyu idan Allah yaso_

*Masu fada dani da masu jin haushi na da masu cewa sun daina karatu duk dan saboda mutuwan Khamis sai ku maida wuƙan ku🤭 Khamis is alive🤓*

MATAR KULLE(Short story)Where stories live. Discover now