(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
😈 *MATAR KULLE* 😈_(Thriller)_
_Short story_
©️2020 specialтнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Blog : prowritersnovels.blogspot.com
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*29🧛🏽♂️
Tun Khamis yana ƙoƙarin zama a ɗaki domin barin ta ta sake agidan ubanta har ya fara gundura da zaman ɗakin shima kawai yaci gaba da fitowa kaman ko yaushe, idan dare yayi sai jaɗe ya taimaka mishi ya fito tsakar gida a haɗa wuta suna shan dumi saboda wurin akwai sanyi sosai,Satin Khamis 5 da kwanaki 5 a wuroɓokki malam Arɗo ya dawo daga tafiyan da yayi, saidai yana shigowa gari da labarin abinda ya faru da boɗɗi ya fara cin karo bai zarce ko ina ba sai fadan mai gari don jin ba'asi, ba zallan mai gari da mutanen shi ba harda shi yariman yaron da bai wuce shekaru 19 zuwa 20 ba suka zauna suka ci mutuncin malam Arɗo ta uwa ta uba da duk dangin su, basu barshi ba har saida suka tabbatar da ya zubda hawaye sannan hankalin su ya kwanta,
Da ya tashi tafiya suka ƙara mishi da wani kayan haushin, yarima da bakin shi ko kunyar idon shi baiji ba yace idan boɗɗi ta gyara halayen ta a faɗa mata zata iya zuwa ta bashi haƙuri ya maida ta ɗakin ta,
Malam Arɗo ji yayi a zuciyar shi kaman ya kama yarima yayi mishi dukan tsiya amman hakan ba zai yiwu ba, don bala'in da suke ciki yanzu kaɗai ya ishe su ba zai sake jangwano musu wani ba, saidai ya ɗau aniyar duk abinda zai faru boɗɗi ba zata taɓa dawo da kanta ɗakin yarima ba in dai baizo yayi bikon ta ba,
Da baƙin cikin abun a ranshi ya shiga gida, amman yayi iya ƙoƙarin shi ya danne nashi bacin ran saboda ya samu ya kwantar da hankalin boɗɗi, jikokin shi yaran jaɗe da yaron yayar boɗɗi sahura mai shekara 1½ wanda take wurin su saboda laulayin ciki da take fama dashi itama duka duka shekarun ta 16 ne, suna ganin shi suka ruga da gudu suna mishi oyoyo,
Boɗɗi kuwa tunda taji shigowar shi ta koma ɗaki ta rufe tsananin kunyar mahaifin ta ya kamata, itace mace ta farko a dangin su da ta taɓa yin aure ta fito kuma wannan tabon abin kunyan da tayi musu tun yanzu zasu fara ganin sakamakon shi ba tare da ɓata lokaci ba,
Zuwa jikin ƙifar yayi yana kiran ta a hankali da taxo ta buɗe mishi ƙofa bayan ya ajiye kayayyakin da yazo dashi, ya ɗauki tsawon lokaci a wurin yana lallashin ta da ƙyar ta yarda ta bude mishi ƙofar ya shiga ta koma ciki ta haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,
Yanda ta rame ta zagwanye gaba ɗaya saida ya bashi tsoro, harta yatsun hannunta saida suka gwada rama ga wasu gashushuwan wuyan ta da suka fito kaman wanda aka ɗaura mata necklace, gashin kanta da yake a bude yanzu ya zube don a yanzu iyakacin shi ƙasan kafaɗun ta kaɗan gashi ya sauya kala saboda datti tayi baƙi ta lalace,
Danne hawayen dake ƙoƙarin zubo mishi yayi ya ƙarasa wurin da take zaune ya durƙusa yana patting bayan ta a hankali tare da maimaita mata wa'innan kalman da yaren fillanci
"Kiyi haƙuri inna ta, shi rayuwa haka yake cike da darussa kala_kala, kuma wanda Allah yafi so shi yafi jarabta idan kin zubar da hawaye yau tilas wata rana zakiyi dariya"A ko wani lokaci idan wani daga cikin mu yana cikin matsala kalaman da yake faɗa musu kenan, idan sun tambaye shi ma'anar haka sai yace musu wannan saƙo ne a dunƙule ga mai tunani,
YOU ARE READING
MATAR KULLE(Short story)
Short Storythere is no marriage without love, so also no love without trust, but jealousy have overpowered KHAMIS love, that he tortured his wife YUSRAH to the extent that she can't endure it anymore, will he become a good man and ask for her forgiveness? or s...