(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
😈 *MATAR KULLE* 😈_(Thriller)_
_Short story_
©️2020 specialтнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
Blog : prowritersnovels.blogspot.com
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
*BY*
*UMMU NAJMA*28🧛🏽♂️
Wani kaɗawa hanjin cikin ta sukayi suna bada sautin 'ƙulululu' tana zazzare ido kaman wanda akayi ma ƙarya, da azama ta juya ta nufi ɗakin hinde saboda sauri har tana tuntuɓe,Dogon tsaki Khamis yaja yana rayawa a zuciar shi gidan nan mahaukata kawai aka tara komi nasu a baibai, jaɗe yana kawo mishi ruwan yayi alwala ya taimaka mishi ya miƙar dashi suna shiga ɗaki sannan ya shimfida mishi abin da suke sallah a kai ya zauna ya gabatar da sallar isha da asuba dan a tunanin shi kwana ɗaya kawai yayi bayi cikin hayyacin shi,
Yana idar da Sallah ya samu sun shigo mishi da abinci a akushi, kallon ɗukamen tuwon yayi wanda ya sha man shanu har wani gangara yake yi a take yaji amai ya taso mishi sai kawai ya saka murfi ya rufe abincin kada ya sake jiƙa musu aiki dan a rayuwan shi ya tsani man shanu,
"Kaɗɗo bakki shon abinshin ne a kawo miki wani?" Jaɗe ya tambaye shi, gyada kai kawai khamis yayi ya ɗauki abincin ya fita dashi ba tare da yasan dabwani abun zai sauya mishi ba, suma abinda suke ci kenan,
Kitchen ya mayar da abincin sannan ya fita zuwa gidan shi ya gani ko matar shi zata sama ma Khamis abin da zai saka a cikin shi, ɗan ɗanwaken da tayi musu zasu ci dududu bai wuce rabin mudu ba haka ya ɗauko kacokan ya kawo mishi, yaci ya rage tukunna ya bawa yaran saura shi kuma da matar shi su rungumi na annabawa su sake cin ɗumamen safe,
Khamis bai sake komawa barci ba sai bayan da yayi sallan azahar, sai da ɓoɗɗi ta daina jin motsin su gaba ɗaya tukunna ta iya fitowa don zagawa banɗaki, gaba ɗaya khamis ya gama tsorata ta ita bata taɓa ganin shi ba kuma bata da kwanciyar hankalin tambayan waye shi a yanzu,
**********
"Auta.." na kira ta a hankali ina taɓa kafadar ta, bata juyo ba ta sake gyara kwanciyar ta yanda zata bani baya da kyau,"Nasreen please, I'm sorry Allah ba zan sake ɗaura hannu na a jikin ki saboda wannan maganar ba I'm so sorry amman nima ki daina kawo min zancen Safwan don Allah"
Juyowa tayi tana fuskanta na itama cikin muryar nutsuwa tace "meye laifin ya Safwan ne dan Allah? Me zaiyi ya sami lokacin ki aunty Yusrah? Ki faɗamun ko menene zanje na same shi na sanar dashi zai miki"
"Tashi ki zauna" na faɗa ina ɗaga ta, zama tayi ta zuba min idanu tana sauraren bayanai na,
"Nasreen ke yarinya ce har yanzu shiyasa ba zaki fahimci menene soyayya ba, ba'a yi mishi dole, ba'ayi mishi garaje, kuma babu ƙarya a cikin ta domin duk wanda yayi ƙarya a cikin soyayya ba zata taɓa bulle masa ba, zuciyata bata mararin ya Safwan koda ace alal misali na amice dashi zaman mu ba zaiyi mana daɗi ba""Aunty Yusrah ki daina cewa ni yarinya ce idan har maganar soyayya ne because I can clearly understand everything, i can understand your situation, you are troubled and depressed amman halin da kike ciki bai kai wanda zai makantar da ke ki kasa gani ba,
na daɗe banga wani namiji irin ya Safwan ba wanda yake soyayya da duka zuciyan shi kuma yake hidima ma wanda yake tare dashi saboda Allah, bai damu da abinda zai ribantu daga gare ki ba har gobe shi yake ɗaukar dawainiyar Jannat kamar mahaifinta wata mace ce zata samu irin wannan namijin taƙi amincewa dashi bayan ke?
YOU ARE READING
MATAR KULLE(Short story)
Proză scurtăthere is no marriage without love, so also no love without trust, but jealousy have overpowered KHAMIS love, that he tortured his wife YUSRAH to the extent that she can't endure it anymore, will he become a good man and ask for her forgiveness? or s...