KUSKUREN BAYA BABINA 2

731 21 3
                                    




WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️02

A firgice ta juyo Ibrahim ta gani tsaye a bayanta yana sakar mata murmushi, ta yatsina face d'inta tana kauda kanta gefe ,tsaye yayi yana kallonta gabansa na wani irin fad'uwa, musamman daya tuna shine dalilin accident din da tayi.
Cike da sanyin jiki ya k'ara matsowa daf da ita ya rage tsawonsa har tana iya jin karar bugun zuciyarsa da hucin numfashinsa a gefenta, runtse idannunta tayi ta juyo zata mishi magana karaf idanunsu ya tsarke cikin juna har saida hancinsu ya da'n gogi juna.

Tsura ma juna idanu sukai kafin daga baya tayi ko'karin da'uke kanta shima yaso yin hakan sai dai nan suka buge kasancewar guda sukai da fuskokinsu. "Ouch!". Ta furta a hankali cikin Jin zafi ta kai hannunta kan bandage din dake zagaye a kanta.

"So...sor...sorry!". Ya fada lokacin daya d'ago tare da d'aga hannunsa idannunsa a runtse kamar ciwon a kanshi yake haka yaji, ware idannunta tayi tana kallon yadda duk yabi ya rud'e yake bata hakuri tuni gwiwowinsa suka sake yin mazauni a gabanta .
"I.B!". Ta Kira sunansa cikin sassanyar muryarta kamar yadda ta saba kiransa, lokaci guda ya d'ago rinannun idannunsa yana kallonta itama shi take kallo cike da tsananin tausayawa.

"Tan I am really really sorry for causing you so much troubles on your special day". Ya fada yana kallonta cike da kulawa da nuna lallai yana nufin abunda yake furta mata har ransa.

Lumshe idannunta tayi ta bud'e " Hey is not your fault kawai haka Allah ya tsara karka yi blaming d'in kanka". Ta fad'a tare da kauda kanta dan ko kada'n batason ganin irin wannan yanayin nasa dan yana karya mata zuciya sosai.
"Yes of course I am to blamed for everything inda bankira ba this wouldn't have happened but nayi diverting attention di'nki I am ver...".
"Oh my god I.B!"ta fada cike da bacin rai idannunta rufe.

"I am s...".
"I know you are Kuma nayi accepting kaima kayi hakuri". Ta faɗa lokacin data tashi tsaye tana binsa da kallo shima tashi yayi suka kalla juna murmushi ya sakar mata. Da sauri ta da'uke kanta tare da shooking d'in kanta da murmushi me sauti.
Jin sautin murmushinta yasa shima ya fad'ad'a nasa murmushi. Taku tayi zuwa bakin window d'in shima cikin sauri yabi sahunta, yasa hannunsa biyu ya zagayeta dasu ya mannata a jikinsa, Runtse idannunsa yayi yana jin wani irin feelings d'inta, sam baisan ya rasa ta a rayuwarsa.

Bangaren Tanweer kuwa ajiyar zuciya ta sauke tare da runtse idannunta, tana matuk'ar tausaya ma d'an uwan nata irin son da yake mata tun bata san soba, ta rasa mai yasa har yau bata jin sonshi cikin ranta baya ga na 'yan uwanta duk da tasan yana masifar sonta da rawar jiki a Duk abunda ya shafi lamarinta amma ta kasa sakin jiki dashi gashi shi kusan bai da aiki saina rungumarta a ko yaushe hakan baya sata taji irin abunda take jin friends dinta na bata labari sai dai kawai ta biye masa, Sun jima a tsaye yana rungume da ita inda sabo ta saba da wannan hug din nasa wanda iya abunda yake iya samu kenan agunta bayan shi ba wani.

"Salamu Alai... ae!".
Momy tafad'a lokacin data turo kofa yanayin data gansu yasa tayi saurin kokarin komawa tare da jan ko'far da sauri Tanweer ta zame jikinta daga rik'on da Ibrahim ya mata wanda shima tuni kunya ta gama rufe shi.
"Please Momy wait!". Ta fada lokacin data dan taka da sauri zuwa bakin ko'far tana kallon Momynta wacce ke kallonta cike ta tambayoyi ganin yadda take kamar tana Jin tsoron yin magana, sun dauki mins a tsaye a haka tana jujjuya ka'farta ta rasa meyasa take jin tsoron yin magana akansa duk da she don't know him.

"Tanweer I am waiting!". Momy ta fada lokacin data kalla Ibrahim wanda shima ya kasa kunne yake sauraran jin abunda ke zuciyar Masoyiyar tasa, wanda daga shi har Momy suna mamakin yadda take hesitating yin tambayar bayan she is not the type to.

🌺KuSKuReN 🥀BaYa🌺Where stories live. Discover now