WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
https://my.w.tt/lcJskJdtpbb
🅿️07
......Kusa daita ya ɗan duka yana kallonta ,a hankali yaji ta kamo yatsun hannunsa cikin nata tana murzawa bai san sanda ya zauna a gefenta yana sauke numfashi tare da tankwashe ƙafarsa ɗaya yayinda d'ayar kafar ke kan tayis yana jijigawa , matso da kanta tayi ta d'aura saman cinyarsa, idanunta a lumshe take jin yadda idanunshi ke yawo a fuskarta ,motsa hannunsa yayi da niyyar zarewa daga cikin nata saboda yanayinsa daya ji yana sauyawa, ta bud'e idanunta tar akanshi Ido cikin ido suke kallon juna lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud'esu akanta ya mik'e dan baya son kusancinsu tare "me yasa baki jin magana ?"
cikin sanyi murya tace " me nayi maka ?" tana janyo hannusa ya rankwafo jikinta bakinsa ya sauka a daidai kunnenta hucin numfashi yasa ta runtse idanunta da sauri. "Ki tashi muje na maidake gidan ku" yayi mgnr yana sakin numfashi haɗe da ciza gefen kunnenta ta saki qara mara sauti tana jin wani iri a gabad'aya ilahirin jikinta ."No! bance maka bazan tafi ba but atleast na.....
"Shiii!". ya katseta ta hanyar d'aura yatsansa kan lip's d'inta, shiru sukayi gbdy zuciyarsu na bugawa "ka hanzarta maida yarinyar nan tun bata zame maka kaska ba'. zuciyarsa ta faɗa masa haka mik'ewa ya sake yi yana kamo hannunta "Ke! tashi muje". banza tayi masa tana yatsina fuska "bana son Ki sake min mutsu ". yayi maganar yana matse yatsun hannunta cikin nashi yana ko'k'arin sauko dai ta, Cikin rashin sa'a ta fad'o jikinsa tare dan k'ara. "Ahm!". Idannunta rufe, yadda ta runtse su yasa ya k'ura mata idanunsa masu kyan gaske, dan kanne d'aya idon tayi ta bud'e sai tayi saurin mayarwa hakan ya bashi murmushin da sam bai shirya yiba me sauti jin haka yasa tayi saurin bud'e idannunta akansa.Murmushin ya k'ara mishi kyau sosai , d'an k'ara ware idanunta tayi tana kallonsa wanda har lokacin fuskarsa na d'auke da murmushin. Ko'k'arin gyara tsayuwarta ya soma Tanweer kuwa da sauri ta kai ma bakinsa cafka tamai peck a lips d'insa ware idannunsa yayi yana kallonta. 'Do want to kill me wannan yarinya'. Ya furta a ransa Tan kuwa murmushi take masa, sake kai mai Cafka tayi a karo na biyu sai dai wannan karon taji ya bude 'yan lip's dinsa inda ya soma kokarin kissing d'inta cafko harshenta yayi cikin nasa kamshi sweet taji mai kamshi lemun ware idannunta tayi ganin kallon da yake mata yasa tayi saurin runtse idanunta .
Tsura mata idanunshi yayi tare da d'an murmushi, yana jin yadda take jujjuya harshenta da sweet din dake cikin bakinsa take zuciyarsa ta dasa ayar tambaya akanta. 'anya kuwa yarinyar nan cikakkiyar buduwar ce ? anya kuwa ba watsatsiba ce take neman kawowa zuciyarsa farmaki? to idan itace kai meye ?Me ye marabinka daita? " wata killa ma ta fika tunda bata aikata abinda kake yi...'.......
Kasa k'arasa zancen zucin nasa yayi saboda yadda take bin kunnensa da lallausan yatsunta tuni ya kasa jure abinda take masa a hankali ya cafko harshenta yana tsotsa a tare suka shanye sweet din sai ji sukayi sweet din ya kare aiko ta saka masa kukan shagwa'ba. "Wayo! Why?". Tsura mata ido yayi yana kallonta tare da d'an janyewa, Tanweer banda tab'e baki ba abunda take tana kallonsa. "Ba...ka..kaine ka shanye sweet din byn bai isheni ba". Tayi maganar a shagwab'e kamar zatai kuka. 'bata face yayi wannan karon ba alamun wasa yanzu a fuskarsa. "okay tashi muje idan ma dubunsu kike so zan miki guzurinsa ta sauko tana gama saukowa ta rungumeshi a jikinta "i love you Mr.No Name!". tsintar kanshi yayi da kasa rabata da jikinsa. "Just one day with you but ina jinka tamkar kar mu rabu, is it necessary sai mun rabu?". bakinsa ya kai cikin kunneta yana busa mata hucin numfashinsa, lumshe ido tayi "ka barni zuwa gobe plz ban gaji da kasancewa tare da kai ba"ta furta cikin sanyin murya kamar zatai kuka, dan ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta. "ta kowani bangare mahaifinki ya baza mataken tsoro ya damu sosai da rashinki me yasa zaki so zama dani fiye da iyayenki why?"
yay mata tambayar tare da ko'karin kaucewa.
"I know zasu damu sosai hatta I.B ma zai damu da rashina mutumin da muryata kadai idan bai ji ba a rana babban tashin hankaline gareshi "
take qirjinsa ya buga zuciyarsa ta shiga rawa shiru yayi yana ƙoƙarin 'ban'bareta a jikinsa idan bai manta ba shine mutumin da suke waya daita a wancan ranar da tayi accindent "wannan damuwarki ce murmushin karfin hali tayi wanda yafi kuka ciwo "mutum mai dakakkiyar zuciya kamarka bai dace ya damu da lamuran mutane ba sai dai acikin kwayar idanunka kadai za'a iya hango tarin tausayi mutane bila'adadin". "Ki daina wasa da zuciyarki da tunaninki muje kawai". Yayi yunkurin sake bambareta ta manne masa tana gyara tsayuwarta a jikinsa gabansa na bugawa da matsanancin karfi yayi nasarar zareta a jikinsa suna fuskantar juna " ki daina bata mana lokaci saboda hakan babu abinda zai janyo sai tarin damuwa dan bazan taɓa sonki ba kuma ki daina sona sannan daga yau bazaki sake ganin ko mai kama dani ba, kiyi rayuwarki tare da wanda kika fara, ni ba mutumin da zaki yi rayuwa dashi bane"
YOU ARE READING
🌺KuSKuReN 🥀BaYa🌺
RomanceZara-zaran yatsun hannunta wanda suke sanye da zobina masu matukar kyan gaske da d'aukar hankali ,idona ya soma hangowa sanadiyyar motsa hannun da take tana juya stearing tana ɗan kad'asu lokaci-lokaci saboda wak'ar dake tashi a cikin M...