WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
https://my.w.tt/lcJskJdtpbb
🅿️09
.....Mamakin jin furucin Jaguwa na karshe ya cika zuciyar Alh tanko gote mutumin daya shahara a cikin fadin duniya da aikata masha'a bangaren neman mata cin amana ,makirci, son abun duniya ba dan bashi dashi ba ,daurawa mara laifi laifi domin bawa mai laifi gsky saboda abun duniya ,idan kana son ka kasance dan ta'adda mai lasisi da neman gindin zama acikin kasar nan nemi tanko gote,idan aikinka garkuwa da mutane ne fayde zama dilan kwaya da sauransu nemi tanko gote duk zai tsaya maka asirce kaci karen babu babbaka ko an kamaka zai sa a sakoka cikin kankanin lokaci .............
Duk wannan mugun aikin daya ɗauki tsawon shekaru yana aikatawa adalilin connection din da yake da acikin yan siyasa babu wani mutun ko ɗan fashin da makamin daya taɓa kawowa rayuwarsa farmaki ,
hasalima yana jin sign dinsu ajikinsa kafin su karaso gareshi yake maganinsu , sai gashi yau da ranar Allah dan fashi kwaya daya tal ya farmaki rayuwarsa har yana masa barazana da rayuwarsa , jiki a matukar sanyaye ya soma jan buhun kudi jaguwa na gefensa "idan kayi wata alama da wani zai gane halin da ake ciki wallahi zan ɗauke numfashinka daga doron kasa sai dai nima a ɗauke nawa numfashin wanda daman ni da wannan shirin na fito mutuwa ko akasin haka ..... ""Karka damu babu wanda zai fahimci komai ya fada hannusa na karkarwa, kai tsaye bayan but din motar Jaguwa suka nufa ya jefa buhun kudin da kyar yana haki , haka suka dinga jerewa suna shiga yana dauko buhun kudi har ya kwashe tasssss ya tsaya tare da nad'e hannunwansa guri daya har lokacin zuciyarsa cike take da mamakin irin gogewa da kwarewar jaguwa .
Jaguwa ya manna gun a gefen brain d'insa "muje ka kaini gurin yar gaban goshinka Alh tanko gote ya kalleshi a matukar frigice zuciyarsa na dokawa da karfi "karka taɓa lafiyar iyalina idan wadan nan kudin basu isheka ba zansa akawo ninkisu yanzu
" yayi kyau shugaban fataken dare sai dai kar kwakwaluwarka tayi maka wanann banzan tunani dan nasan daraja da kimar dan adam ba irinka ba wanɗa yake danne hakin dan Adam domin son duniya , a hankali ya dinga daga kafafunsa zufa na karyo masa a gaba-daya sansar jikinsa yana tunanin "waye shi wannan ? "da dukkanin alamun yasan shi farin sani har suka shigo parlou'n zuciyarsa na cikin frigici , yayinda har zuwa wannan lokacin amaryarsa na tsaye hankalinta a matukar tashe tana ganin bindiga a gefen brain din mijinta tayi saurin durkushewa bisa gwiwowinta tana furta "na shiga uku me zan gani haka ni salma ? Alama jaguwa yayi mata da bindiga take tayi shiru jikinta ya kama kyarma .."kin san me yasa na bukaci wannan azalumin mijin naki ya kawoni gareki ban bukaci ya kai ni gungu mattarar tsiya ba ? tayi saurin girgiza masa kanta jikinta na rawa "saboda nasan kece tauraruwar gidansa da dokarki ake aiwatar da komai na gidan nan , sai yadda kika so za'a yi dan tanko gote mijin tace ne agurinki sai yadda kikayi dashi "ki faɗa masa kar ya kuskura ya kawo wa aikina hauka , bayan wannan ya kamata ki san ko waye wanda ke tsaye a gabanki duk da idanunki a halin yanzu a makance suke ,"sunana jaguwa akaro na farko da wani a duniya zai san wani abu daya danganceni sannan ya san sunan dan fashin daya gagarin kasa da yan sanda "
" a wasu shekaru da suka gabata anyi wani natsatsen yaro wanda ya taso cikin gata da kulawa, yana da mahaifi da mahaifiya da kane gudu hudu namiji daya mata uku , wahalar duniya tayi musu yawa naci ma da kyar suke samu sai da wannan azzalumin mijin naki yayi nasarar jefa rayuwarsa cikin gararin rayuwar da yasa ya dawo wannan mutumin dake tsaye agabanki , jaguwa ya sake tsuke muryarsa ya cigaba da magana "abinda yasa na dan baki labari ,mijinki ya cancaci na kashe shi bisa girman laifin da yayi min a shekarun da suka gabata sai dai na barshi da halinsa dan hukuncin Allah zai fi akan nawa hukunci ,sai abu na gaba " idan mijinki yayi kuskuren ko gigin sako jami'an tsaro ciki aikina domin yunkurin tona min asiri ko bincike akaina zan.....
da sauri tace" he wont involved the police farinciki ya ziyarci zuciyar jaguwa saboda ya hango firgici da matsanancin tsoro attare daita, yana gama jin abinda tace yace "shiga muje kou " Alh tanko gote yayi saurin waigowa gefensa inda Jaguwa ke tsaye fuskarsa da alamun tambaya "karka ɗauka bansan abinda nake ba ,nasan halin mutane azzalumai irinku masu bin mutane da bita da kulli ka shiga muje kawai ban gama da kai ba idan kuma mutsu zaka min yanzu na harbeka na harbe kaina muyi mutuwar kasko ,babu mutsu ya shiga gaba jaguwa na biye dashi har cikin mota ,Jaguwa ya zagaya ya shiga bangaren direba ya tayar ya nufi get ....
YOU ARE READING
🌺KuSKuReN 🥀BaYa🌺
RomanceZara-zaran yatsun hannunta wanda suke sanye da zobina masu matukar kyan gaske da d'aukar hankali ,idona ya soma hangowa sanadiyyar motsa hannun da take tana juya stearing tana ɗan kad'asu lokaci-lokaci saboda wak'ar dake tashi a cikin M...