KUSKUREN BAYA BABINA 3

642 24 1
                                    



    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️03

Matsawa tayi  gefe da sauri  jikinta  na wani irin  kyarma  yanayin bugun zuciyarta  bai saisaita ba ,  yanayin tsoratanta kuwa ya  wuce  tunanin mai karatu da kyar take fitar da numfashi qirjinta na kasa da sama   ,murmushi ne ya sake  bayyana  akan kyakkyawar fuskarsa  mai cike da annuri  , cike da natsuwa da  jin kai  da izza  ya  matsota  kamar  zai shige  jikinta batare daya sani ba ,  haka nan  ya  tsinci kanshi da kai hannunsa  ya d'ago ha'barta  ya tsura fuskarta   kwayar  idanunshi masu matukar kyau da haske  cikin nata  yana kallon kyakkywawar  fuskarta da kwayar idanunta   har jikinsu  na gugan juna,  wani  irin kamshi ne na musamman  ke tashi a sansar jikinsa tamkar wanda yayi wanka da ruwan turare  , hakan yasa ta kasa kawar  da idannunta daga nasa  ...

Sosai ya tsura mata   kyawawan  idanunshi  yana kallon fuskarta, tunda yake rayuwa   bai taɓa ganin  halittar data masa kyau ba tamkar hallitar dake tsaye a gabansa , tun daga kan  tsiraran  lips d'inta, dara daran idannunta, hancinta komai nata ya tsaru  ga 'yan yatsunta zara-zara  da take nuna masa  hanya fita  dashi , gaba d'ayabaya ya soma fita  hayyacinsa ban da kallon  halittarta jikinta   babu  abinda yake ,a hankali idannunsa  suka sauka akan saman qirjinta  dake cike bam  da dukiyar fulanin masu matukar kyau da haske  a zahiri yake hango  rabin nonuwanta  da suka bulluko waje  sakamakon  rigar baccin dake sanye ajikinta masu matukar kyau  ne da budaden wuya dan rigar ta zamo zuwa kafad'anta kamar up shoder   " ya Salam !'. ya furta a kasan  makoshi yana lumshe sexy eye's dinsa   , a hankali bugun zuciyarsa  ya karu  tare da k'ara ware idannunsa akanta sannan ya kara matsota ya cire hannunsa dake rike da ha'barta  ya cire hanky mai shegen  kyau da kamshi  daga  aljihun wandonsa ya kai fuskarta ya soma goge mata fuska dake kwararar da ruwan hawayen daya rasa dalilin zubarsu, kuma har lokacin idanunshi na kan dukiyar fulaninta  ya kasa daukesu duk da abinda yake son yi kenan amman ya kasa,   rigar   baccin  dake  jikinta sun  mata maseefar kyau bayan bayyanar da surar jikinta da suka yi   .

A tsanake tanweer ta fahimci inda yake kallo ajikinta ya d'ago idanunshi   ido cikin  ido suke kallon juna  a hankali ya soma ko'karin matsawa daga gefenta saboda ganin irin mugun kallon da take binshi da shi mai ɗauke da zargi iri iri , cikin rashin sa'a itama tana ko'karin da'uke kanta dan  gani take kamar tab'ata zaiyi,     
Hannunsa  ya tab'i qirjinta   batare da yayi niyyar aikata  hakan ba sai dan ƙoƙarin saisaita kanshi , cike da takaici da zafin nama tattare da bakinciki  tanweer ta da'ukeshi da wani gigitaccen marin da bai san sanda yayi mutuwar tsaye  agurin ba rike  da gefen fuskarshi   yana kallonta  cike da tsananin mamaki   lokaci daya  ranshi yayi mugun baci ,take  zuciyar shi ta shiga bugawa da sauri sauri  wani duhu ne ya gilma cikin kwayar idanunshi yana jin  wani tuttukin bakincikin   da takaici  mai tattare da "bacin rai..

"What?!". Anas dake tsaye a bakin  k'ofa  jin saukar marin yasa ya lek'o da sauri abunda idanunsa suka gane masa ne  yasa ya karasa shigowa dakin   a daidai lokacin da tanwer ke magana cikin siriryar muryarta "How dare a desperado like you touch me! Waye kai dame kake tak'ama har  da zaka taba'ni da wannan kazamamm han....".

"Barta!"  Jaguwa ya fad'a da karfi jijiyoyin kanshi na mikewa  haɗe da tare hannun Anas wanda sai lokacin ta lura  da isowarsa gurin  . "Amma bo..."nace ka fita!" wannan lokacin sound d'inshi da k'arfin gaske ya fito wanda dukkansu sai da suka tsorata bama ita da tayi marin  ba , ganin yanayinsa yasa Anas saurin fitowa  ya bar da'kin tare da ja musu ko'far ransa a bace "lallai kin dibo ruwan dafa kanki Anas ya furta yana sauke numfashi ...

Da baya jaguwa  yayi taku biyu ya zauna a gefen bed d'inta batare daya sake furta komai ba  gaba d'aya jikinta wani irin kada'wa yake saboda tsabar tsoro da fargabar abinda zai mata a yanzu, dan a kallon da take masa take hango tashin hankali iri iri attare dashi wanda  da wuya ya barta  haka batare daya ɗauki wani  mataki akanta ba ,dan haka ta yanke shawarar barin dakin tun kafin ya mike yasa bindiga ya harbeta , ta juya hankalinta  a  matukar tashe tun kafin tayi  hanzari  barin dakin taji  sautin murmushinsa a bayanta , tayi saurin juyawa tana kallonsa a rud'e , a hankali sautin murmushin ya sake hawa yana k'ara sound yana zamewa daga saman gadon zuwa  kasan tayis yayi kyakkywan  mazauni a k'asa yana murmushin mugunta wanda duk sanda yayi haka mutun ya kuka da kanshi .

🌺KuSKuReN 🥀BaYa🌺Where stories live. Discover now