KUSKUREN BAYA BABINA 10

592 20 13
                                    



    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️10

...A hankali  sp  yusif ya sauke   bakin  bindigarsa  yana  haki  yana takowa a hankali  har ya karaso jikin  murfin motar jaguwa  ya ja ya  tsaya tare da d'aura  hannunsa ɗaya a  saman mota  "the wages of sin is death ......."
ya  furta haka yana duban inda  yaransa ke tsaye rike da bindiga   "yau  dai munyi nasara  kashe tantirin  ɗan fashin daya addabi  kasa da kasa   ,Allah na gode maka daka bani dama da ikon kawar dashi daga doron duniya , isar da gawarsa headquater  ma  wani  matakin d'aukaka ne  garemu ,na dade ina addu'a akan zuwan wannan rana sai gashi tazo mana  cikin sauki dole  mu  samu double promotion...... " ya karasa maganar yana kallon sararin samaniya zuciyarsa fes cike da matsanancin farincikin samun nasara .

   "ya sake buɗe  bakinsa da niyyar sake yin magana  yaji an daki  murfin   kofar motar  da karfin gaske   kofar ta buɗe wanda hakan yayi sanadiyyar da hannun  jaguwa ya bugu da murfin kofar dashi kanshi sp  yusif dake tsaye  yayi taga taga ya koma baya sannan ya tsaya bisa kafafunsa yana kallon motar  .

Mutuwar tsaye suka yi gabad'aya  suna kallonsa take  bindigar hannun sp yusif ta subuce  yayi saurin sake  ja da baya idanunshi na kan jaguwa dake ƙoƙarin fitowa daga cikin motar,  duk ilahirin jikinsu rawa yake har sp yusif wanda hankalinsa kusan yafi na sauran tashi dan yanayin bugawar zuciyarsa da yanayin tsoronsa sai ya baka mamaki tamkar ba jami'in tsaro ba  "

  cikin isa da izza jaguwa  yake takowa zuwa inda sp yusif yake tsaye , ya tsaya nisa kaɗan dashi wanda bai fi taku biyu su fuskanci juna ba  , idanunshi dake a lumshe  ya  ware su fesss  akan  sp  yusif yana ciza gefen  lip's d'insa na kasa,sp   yusif  ya kalli jaguwa  kamar zai yi kuka saboda gigita da ganinsa a raye da yayi , tunda yake bai taɓa ganin abinda ya d'aga masa hankali irin wannan ba , "bai taɓa ganin dan adam din da aka yiwa harbi irin wanda suka yiwa motar jaguwa ba amman ya rayu har ya samu damar fitowa  daga cikin motar cikin isa da izza ,tabbas yasan akwai wata a kasa ,wannan abu akwai tsarkakkiya acikinta     "

  Jaguwa  ya had'iye dariyar sp  yusif dake  neman kufce masa saboda gabad'aya ya gama karantar yadda sp yusif da yaransa suka tsorata dashi  ,dan gabadaya fuskokinsu ya sauya daga farinciki  zuwa matsanancin tsoro da firgici  kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin tashin hankali mai tsanani ...

"waye  kai  sp yusif karaye  ? mutumin da cin hanci da rashawa ya aura  tun kana ƙaramin  mataki har zuwa yanzu daka taka wannan matsayin , har kake godiya ga Allah bisa samun nasara akaina  "wani mataki ka taka tukunan ma a rayuwarka da zaka so kama mutun irina  "?yayi masa tambayar yana kafeshi da kyawawan idanushi hade da sauke numfashi .

"Ya kamata kusan ko waye ni kafin ku dinga bibiyar rayuwata  kana min kallon mamakin ko ? "Kana mamakin yadda na rayu ko ? Zan so bude maka hanyar da zaka fahimci ko wanene ni  da kai da sauran tawagar dake bibiyar rayuwata amman bazan yi ba zan barku  cikin duhu da wasi wasi da kai da waɗan nan yaran naka daka taso  gaba " babu abinda zaku iya  akan jaguwa sp yusif karaye  , ba ku   ba hatta shugaban tawagarku  gaba-daya wato commition of police yayi kankatar da zai iya gaba da gaba dani bare kai da yaranka  ya karasa maganar a fusace yana nuna sp  yusif da yatsansa "

"a kasar nan  kowa abinda ranshi yake so yake tare da aiwatar da son zuciya akan kaskantattu marasa  galihu  , "to bari kaji wani labari  da baku isa ba   dubunku ma  basu isa suja da yaran jaguwa ba bare shi kanshi jaguwa , ni nan nafi karfinku nafi karfin hukuma kuma yanzu na sama addabar rayuwar manyan kasar nan   ya karasa maganar yana dukan qirjinshi yana murmushi ......

🌺KuSKuReN 🥀BaYa🌺Where stories live. Discover now