K' A S A I T A [16]

279 8 1
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)



By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv


16...

Cikin tafiyar sa ta KASAITA yake karewa yanayin gidan nasu kallo tunanin rayuwar da yyi a Baya yake yi Hakan ya tuno Masa da ummi bazai manta da zaman su ba domin ta nuna Masa soyayya irinta kakanni ta rasu da shekara daya yabar kasar cike da kewar ta maganganun da sukayi a zaman su da ummi yake tunawa a koda yaushe domin ta bashi labarin masarauta tsaf daga mutuwar kakansa Sulemanu har RIKON KWARYAR sarki Audu da kuma dawowar sarauta zuwa ga mahaifin sa Memartaba Ibraheem, Tunda wayon sa tayi Masa mgnr shiyasa har yanzu ya kasa mantawa kuma shine dalili na farko daya sawa su shu'ayb ayar tmby Dan ko kadan beji sun kwanta Masa a rai ba shiyasa ma beso mahaifin sa ya bashi Galadiman Dutse ba sam, bangaren Hajja kareema yaje bisa umarnin Mummy domin su gaisa tun kafin ya Karasa aka sanar da zuwan sa bangaren Hakan yasa hajja kareema ta fito daga can dakinta zuwa parlo dan tarbar yareema NASEER, sallama yyi ta Amsa Masa Nan kuyangi suka fito Dan Basu waje, Yareema NASEER ya Shiga a nutse Yana Zama kan kujera, Hajja kareema Tace,

"Wannan bazata haka Yareema? Ai daka sanar Mana sai mu shirya sosai Dan tarbar babban bako"memakon ya Bata Amsa sai kawai Yareema NASEER yace, "mun same ku lpy" "Alhamdulillah" hajja kareema ta furta Hakan da murmushi, yareema NASEER ya Mike tsaye batare daya kalli Inda take ba yace, "sai anjima" Hajja kareema Tace, "haba yareema daga zuwa sai tafiya?"  "I've something to do.." ya Ida mgnr Yana ficewa a parlon gaba1, binsa da harara tayi kamar idonta zai Fado kasa Taja tsaki sama2 a hankali Tace, "wuyarta dai kazo hannu Duk Wannan izzar muma sai munyi ta.." Bata Ida rufe baki ba yaron ta habib yayan Mansoora ya shigo parlon, Duban ta yyi yace, "Ammi lpy kike tabe baki?" Gyara yanayin fuskar ta tayi da murmushi Tace, "No ba komai" Zama yyi yace, "yanzu muka hadu da yareema Ashe ya dawo" Ammi Tace, "tun jiya ma ai zuwan bazata yyi Babu sanarwa" 'yar dariya habib yyi yace, "I like he's style" Tsaki Ammi tayi tana hararar sa Tace, "ai sai kayi tayi" ta Karasa mgnr tana mikewa zuciyar ta na ayyana mata matukar hakar su ta cimma ruwa ita da Mansoora Nan gaba kadan sarautar gidan zata dawo garesu.

Yana zuwa parlon Mummy ya zauna kan kujera mummy na kallon sa Tace, "har ka dawo?" Dubanta yyi a nutse yace, "har ne mummy?" Mummy Tace, "duka yaushe ka fita Amma Wai har ka dawo" Dan murmushi yyi yace, "Mummy kenan bayan gaisuwa me kuma zamuyi?" Mummy Tace, "Kanata miskilanci yaushe zaka sake Ayi Hira da kai toh Duk gidan Nan Inaga ba me son mu da gsky kamar kareema da yaranta" yatsina fuska Yareema NASEER yyi yana dago Wayarsa ya Kara a kunne kafin ya Mike da sauri yabar wajen yyi haka ne kawai Dan kar Mummy tayi tajan mgn.

Fitowar sa keda wuya ma sai Kiran Fahad ya shigo wajen garden din gidan ya nufa Yana Amsa wayar daga dayan bangaren Fahad yace, "yaushe zaka wuce kano?" Yareema NASEER yace, "ban Fara Wannan tunanin ba" Fahad yace, "pls kayi tunani akai" yareema NASEER yace, "okay idan na yanke shawara I will let you know" Fahad yace, "Thanks zan shigo anjima" yareema NASEER yace, "Okay."

Mansoora tsabar zumudin ta dawo gida sai tsawa take bugawa driver yyi sauri ita ta kagu ta ganta a gidansu, kawu driver ya gyada Kai cike da girmamawa sannan ya sake bawa motar wuta, kafin Wani lkci kuwa har sun isa masarautar, Tunda ta doshi part dinsu ake zubewa Ana girmama ta ita kuwa sai taku take cike da izza tamkar wacce ta hada iri da gidan sarautar koda yake yadda takejin kanta idan tazo masarauta Koh jinin sarauta Albarka, Hajja kareema ta rungume Mansoora cike da farin ciki Zama sukayi Mansoora Tace, "I missed you Ammi" Ammi Tace, "me too diyata ya school?" "Fine" Mansoora ta Bata Amsa, sannan taci gaba da fadin, "Yah Naseer Yana gida?" Hajja kareema Tace, "tun dazu nasa asa Masa ido Dan musan Yana nan ko Baya Nan" Mansoora Tace, "toh ya ake ciki?" Hajja kareema Tace, "Yana part dinsa" cikin jin Dadi Mansoora Tace, "daidai kenan" Nan ta Mike da sauri ta wuce dakinta da aka gyara mata, toilet ta shige ta watsa ruwa sharp2 kafin ta fito ko tunanin cikin ta batayi ta dauki wasu arnayen kaya tasa a gurguje kafin ta dora abaya da Alkebba akai ta yadda baza'a gane ba, tana fesa turare Ammi ta shigo dakin baki bude Tace, "Wai Ina Zaki kiketa sauri haka?" Mansoora tayi murmushi Tace, "haba Ammi Ina zanje idan ba wajen Yah Naseer ba" Dan murmushi Ammi tayi Tace, "toh ai kya tsaya kici abinci Koh?" "No Ammi saina dawo so nake Nima nayi Masa bazata kafin lbrin zuwana ya Isa gareshi" Ammi Tace, "weldon sai kin dawo" Mansoora Tace, "Aha bye" Nan ta fice a parlon tana fita kuwa kuyangi suka Fara take mata Baya, Koh kallon bangaren su Hajia Uwani batayi ba ta wuce direct sashen Yareema NASEER.

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now