K' A S A I T A [7]

339 11 1
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)



By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv



7.....


"Toh nikuma Wallahi matukar Ina numfashi bazan taba bari Yareema Ibraheem yyi mulkin Nan ba...." Hajia Uwani ta saki murmushin jin Dadi a hankali ta tako har gaban yaronta shu'ayb tana Dan dukan kafadar sa a hankali Tace, "dakyau Dana aini sai yau ka Tabbatar min da kaidin jarumi ne" muzurai yareema shu'ayb ya Fara Yi shi a dole an Kira shi da jarumi cikin kumburi yace, "ai ki Barni dashi ummah cikin ruwan Sanyi zanyi mgnin abin" Hajia Uwani Tace, "na yadda dakai dari bisa dari Dan haka zan zuba maka ido kayi kokarin samun sarautar Nan ta dawo garemu gaba1" "na miki Alqawarin haka ummah" yareema shu'ayb ya Fadi Hakan cikin yakini da Tabbatar da Abinda ke ransa.
*****
Fadin sura ta kamala da kyawu irin na fulanin usul ga yareema Ibraheem Bata lkci ne domin Duk Inda kyau yake tofah Shidin karshe ne Dan kwalisa me tashen samartaka Wanda yake ji da mulki da kuma tsantsar KASAITA, tafe yake Yana gyara hannun rigar sa harya iso babban parlon ummi dake jiransa Dan suci abinci, kuyangi sai Kai kawo suke wajen shirya teburin abincin Wanda aka cikashi makil da kayan ciye-ciye Wannan Yana wane Wannan gwanin ban sha'awa da dandano a baki, shigowar sa wajen yasa Duk kuyangin wajen suka sake Shiga taitayin su Dan ko ba'a fada ba kowa ya sani jinin sarauta dabanne sabanin irinsu yareema shu'ayb da ake kakaba sarautar dole ba kwarjini a gaban jama'a saidai a nuna tsoron sa sbd mugun halin sa, ummi na murmushi Tace, "har ka fito?" Shima murmushin yyi mata yana Zama gefenta yace, "da fatan na sameki lpy" Ummi tace, "Alhamdulillah" Nan ta umarci da kuyangin dake kula da teburin su Fara zuba musu abinci, Nan suka Fara aikin su aka cika gabansu da kayan ci da Sha na Alfarma Saida suka Gama ummi ta umarci gaba dayansu su fice cikin bin umarnin mama fulani suka fice daga wajen cikin gaggawa koda yake dama Duk sun kagu da subar wajen sbd kwarjinin da yareema Ibraheem keyi masu dukda tunda ya shigo be daga Kai ya kallesu ba bare yasan Allah yyi ruwan halittar su a wajen, dubansa tayi da murmushi Tace, "Bismillah" yareema Ibraheem yace, "ummi tunda nazo baki bani lbrn bayan rabuwa ba, I mean ya masarautar Nan take ciki? Akwai Wani ci gaba da aka samu ne? Wanne irin sauye-sauye aka samu a ciki?" Shiru ummi tayi ranta a dagule ba komai take tunawa ba sai zaluncin da sarki Audu keyi shi da dansa yareema shu'ayb, girgiza ta yyi yace, "ummi akwai matsala ne?"

Murmushi tayi Masa cikin danne damuwar ta bataso tayi mgnr dazai daga Masa hankali Alhalin beci komai ba Dan haka Tace, "Dadina dakai yareema akwai gaggawa Ina lefin ma kaci abinci sai na baka lbrin komai?" Dan sauke ajiyar zuciya yyi Yana furzar da iska a hankali yace, "ko dede da Rana daya ban taba cire masarautar Nan a Raina ba, inason gadon mahaifina inason nayi sarauta kamar yadda mahaifina yyi inaso na sauke dukkan nauyin daya rataya a Kaina idan ya kasance tun bayan rasuwar mahaifina Talakawa na wahala bakya ganin Duk nauyin a Kaina yake?" Jikin ummi ne yyi Sanyi ainun saidai tayi kokarin boye Hakan tana duban yareema Ibraheem tace, "shiyasa dazu nake fada maka kwanan zaune zamuyi sbd na sanar maka dukkanin Abinda ya faru bayan tafiyar ka saidai da alama bakason ji Dan Naga baka da niyyar cin abincin" ta Karasa mgnr da murmushin karfin Hali, yareema Ibraheem yace, "haba ai ban Isa ba ummi dole na cika umarnin ki" ya Karasa mgnr shima Yana matso musu da abinci daf da juna Nan suka Fara ci a plate daya Suna taba Hira cikin nutsuwa.

Bayan sun Gama cin abincin suka koma dayan gefen Dan tattaunawa, cikin zaquwa da son jin lbri yareema Ibraheem yace, "inajin ki ummi" ummi Tace, "badan ace fannin shari'a ka koyo ba tabbas da sai nace Kai Dan jarida ne" dariya ta bashi sosai har ya Fara murmushin daya bayyanar da kyawawan hakoran sa yace, "ai ummi Duk sammakal" itama tana murmushi Tace, "kumafa hakane" Nan ta gyara zamanta shikuma ya tattara nitsuwar sa a hankali tace, "bayan tafiyar ka......"

Daya bayan daya ta dinga zayyane Masa Abinda ya faru a masarauta da irin canjen2 sarki Audu har izuwa yanzu da suke zaune, jikin yareema Ibraheem har rawa yake sbd bacin rai ransa idan yyi dubu toh kuwa ya baci, cikin azama ya Mike da nufin barin wajen mama fulani tayi saurin damko shi, kallonta yyi idonsa harya Fara canja kala yace, "me Hakan yake nufi ummi?" Ya Karasa mgnr Yana duban hannun sa data rike a yanzu gaba1 idonsa ya rufe burinsa yakai ga sarki Audu, mama fulani Tace, "a Wannan halin da kke ciki kkeson zuwa wajen nasa?" "Toh ummi meya rage da za'a daga Masa kafa? Koma aya naje ummi ai ya cancanci fiye da Hakan ne Dan Allah ki Barni na tafi" ya Karasa mgnr kamar ya fashe Dan takaici, mama fulani Tace, "banason daga dawowar ka aji tashin hankali ya billo daga gareka" zubawa uwar tasa kallo yyi da mmki yace, "ummi? Kin manta girman hakkin talakawan dake kanmu ne? So kike Allah ya tsayar damu Akan Wannan mulkin zaluncin da yyi shekara da shekaru?" Ummi Tace, "ba haka nake nufi ba"

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now