K' A S A I T A [13]

234 14 3
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)


By
*Nuceeyluv😘*


*Wattpad* #nuceeyluv



13...

Dagowa yareema NASEER yyi yana duban yadda Jama'ar gidan ke girmamasu sai abin ya birgeshi kwarai Hakan ya tuno Masa da zaman su na america Ana girmama su sosai acan har mutanen wajen ma sukayi Masa lakabi da prince Nas, Barrister yareema Ibraheem ne ya daga musu hannu fuskar sa cike da annuri alamar ya Amsa girmamawar da suka Basu kafin suka Mike direct zuwa bangaren sarki Audu.

Acan bangaren nasa kuwa sarki Audu ne yake kwance yasa duka a Kira Masa yaransa da matansa Duk sun taru acan Dan haka Basu san wainar da ake toyawa ba musamman da shike Suna tattauna Abinda yaja hankalin su ga me da Masarautar, zaman nasu ya kasance ne bayan Haruna me bin yareema shu'ayb ya shigo gaida sarki Audu shine ma me hankali dama can bayan sun gaisa sarki Audu ya umarci daya tara iyayen sa wato Hajia Uwani da hajja kareema kishiyar Uwani sai yaran Suma Yana bukatar ganin su, Hakan kuwa akayi Haruna ya tattaro dukkansu suka zauna a parlon kowa na sauraron Abinda sarki Audu zaice, dakyar ya Mike zaune daga kan gadon sa Yana dubansu duba na tsanaki a nutse yace, "yaku Ahalina Ina son nayi maku wasiyya" hankali tashe Hajia Uwani Tace, "haba memartaba wacce irin mgn kke fada haka?" Hajja kareema Tace, "Dan Allah ka daina cewa wasiyya Ina lefin nasiha" Dan murmushi yyi kafin yace, "ko naki ko naso dole na tunatar daku Abinda kuke nema ku mantar dashi da gangan da ganganci"

zuba Masa ido sukayi kowa nason yaji mekeson fada, sarki Audu yaci gaba da fadin, "ke Uwani kece babba haka zalika yaranki sune manya Dan haka Duk yadda aka faro da Wannan sarauta kunsan asalinta, sannan ke kuma kareema tun wuri dama na sanar dake RIKON KWARYA nake ba sarautata bace Dan haka ki dubi yaranki kanana habib da mansura, (yaran data haifa kenan namijin shine babba sai mansura me bi Masa wacce take Shan nono yanzu) ko kadan kada ki cusa masu akidar sarauta Dan ba tamu bace bare suzo Suna tunanin samunta Kota halin kaka" duban sa ya koma kan yareema shu'ayb yace, "kai kafi kowa ma domin kafi dukkansu zaqewa Akan Wannan RIKON KWARYAR da nakeyi, Ina horon ka da tun wuri ka cire son mulkin Nan a ranka dan bazaka taba Hawa kujerar Nan ba, Kai kuma Haruna banaji ta kanka Dan kuwa baka taba nuna alamar son mulkin Nan ba saidai zuciya Bata da kashi kada bayan Raina ku juyawa maganganu na Baya kuzo Kuna yaki Akan Abinda bakuda gsky" Dubansu yyi gaba1 Yana ci gaba da fadin, "Wannan itace takaitacciyar wasiyya ta Ina Kara tunatar daku da kada ku kuskura ku tada tozarma ko jayayya Akan me Wannan kujerar, Ina muku mgnr Nan ne cikin karfin Hali domin ni kadai nasan Abinda ke damuna a cikin zuciyata"

Kafin ace dukkansu kowa ya tofa nasa Albarkacin Wani bawa ya Fado wajen nasu a sukwane Yana haki, dukkansu suka maida Dubansu gareshi kafin a daka Masa tsawa yace, "Dan Allah ku gafarceni Ina tafe ne da Wani muhimmin labari" Sarki Audu yace, "meke faruwa?" Bawan yace, "ranka shi dade zuwan bazata akayiwa Wannan masarauta wato Abinda nakeso nace shine ga Yareema Ibraheem can da iyalin sa sun dawo daga amurka kuma zancen da nake muku ma Basu zarce ko Ina ba sai Nan da suka iyo"

Mikewa da sauri sarki Audu yaso Yi ya kasa sbd yadda yakejin jiki, su yareema shu'ayb kuwa sai zare ido suke, hajja kareema kam dama ta dade tana son ganin wa'annan mutanen Dan har tayi aure ta haife batasan kamannin su ba sai mama fulani kawai Dan haka ta juya cike da kaguwar ganinsu, Hajia Uwani da yareema shu'ayb kuwa kamar suyi ihu Dan takaici Dan kusan tunanin su dayane Akan Abinda suke kitsawa lkcn da sarki Audu ke mgn, Haruna kam ko kadan abin be daga masa hankali ba, habib Dan shekara biyar bema san wainar da ake toyawa ba.

Yareema Ibraheem da gimbiya maryama direct suka shige ciki batare da sun nemi iso ba sai tashin Algaita kkeji a bayansu sallama sukayi a nutse Haruna da hajja kareema ce ma suka iya Amsa masu, sarki Audu ma a hankali ya Amsa Dan baida Wannan karfin, daga Masa hannu yake Hakan yasa yareema Ibraheem ya Isa gareshi ya zauna daga gefen sa Yana bin mutanen parlon da kallo, Gimbiya maryama kam kujera ta samu ta zauna yyinda prince Nas ya makale a gefen ta yana duban mutanen parlon da manyan idanun sa, Hajja kareema baki yaki rufuwa Sai sawa take a ranta Wai Anya kuwa wa'annan kyawawan mutanen sune magajin Wannan masarauta ko idonta ne? Shiru dakin ya dauka kowa ta ciki na ciki, sarki Audu ya dubi Yareema Ibraheem yace,

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now