K' A S A I T A [17]

594 22 2
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)



By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv



17......


*K'AUYEN FULANI*

.......Cincirindon Fulani mata da maza ne suka taru a lambun Idi me gari, kowa ya rike haba cike da jimamin Abinda suke gani, a guje ta karaso wajen tana haki ko lura da mutanen dake zagaye batayi ba tahau hankade su tana kutsa kanta ciki da sauri kuwa aka hau matsa mata Dan Bata waje, Kama qugu tayi tana haki tace, "Babbar bala'in Nan kur'ani yau Babu zaman lafiya a garin Nan" wata kawarta ce ta matso adan tsorace Tace, "Kiyi a hankali *JIDDE* Dan da Alama qungiyar Aljanu ce ta Fara sauka a garin Nan namu" juyowa tayi a fusace Tace, "ke lubabatu ki rufemin baki tun kafin nayi kuli-kulin kubrah dake" ja Baya lubabatu tayi Tace, "Kiyi hakuri" tsaki JIDDE Taja tana duban kan gadon karan ta Wanda aka sassaka da Icce aka tula Masa yayin zana sannan aka bi da ledar buhu aka lullube saiya koma kamar gado ga saman gadon shima anyi Masa rumfa kamar tumba gadon JIDDE ikon Allah kenan Wanda take ji dashi a lumbun mahaifin ta idi me gari, kamar ta hadiyi zuciya haka take kallon mutumin dake kwance kan gadon da sanadiyar hawansa ya balle a kife yake shiyasa Sam Basu san da yanayin fuskar sa ba Daga can barin Wani ne kwance cikin kasa shima a kife Dukkan su basa motsi kamar gawarwaki.

A tunzure JIDDE ta Isa gaban gadon nata tasa hannu da niyar ture shi taji ko gizau bayayi kamar Wanda ta tura dutsi, Hakan ya sake Bata haushi ga mutane na kallon ta bataso aga Rashin karfin ta Dan kowa ya shaida karfin JIDDE sbd yawan fada da take walau namiji ko mace Kai hatta mutanen kauyen nasu ma karbar musu fada take a takaice ma saita sayi fada a biya ta, hannun sa ta riko ga mmkin ta sai taji shi taushi kamar audiga wara manyan idanun ta tayi Tana Dan gyara sumar kanta data zubo gaba sbd Dukawa da tayi ta Fara kallon hannu da mugun mmki, kirjin tane yyi ras Anya ba gsky lubabatu ta fada ba? Kodai ba mutum bane? Ta maza tayi tasa iyakar karfin ta gaba daya daidai saitin kafadar sa ta juyashi dakyar tana nishi sai gashi Surar halittar sa ta bayyana gaba1 Abinda ya gigita JIDDE kenan ta Mike a razane tayi Baya Hakan yasa sauran Suma sukayi Baya, jikinta na rawa ta Kama hannun lubabatu Tace, "jama'a kowa yyi ta kansa kur'ani ba mutum bane" tana Ida mgnr ta kwasa a guje sanadin daya janyo Duk mutanen wajen suka ruga a guje kenan Kai kace kura ta biyo su, Suna Shiga gari kowa ya Fara shigewa gidansu,

JIDDE dake falfala gudu tun daga nesa ta hango mahaifin ta Mlm idi tare da gyatumin kauye Ana zaman fadanci irin na karkara iyakar muryar ta ta ware tana fadin, "baffajo Aljanu sun kawo Mana sammaci, Baffajo kur'ani Aljanu a lambun rake..." daidai lkcn ta karaso wajen nasu kadan ya rage ta gitta su mlm idi ya Mike zumbur Yana fadin, "ke JIDDE me naji kina Fadi?" Juyowa tayi tana haki Tace, "Manyan samudawan Aljanu ne a lambun raken mu Baffajo kur'ani kowa yyi ta kansa tun kafin su Fara tashi sama su shafe mu" tana Ida mgnr ta kwanye a guje sai cikin gidansu,

Jikin mlm idi na rawa ya dubi gyatumin dake kofar gidansa yaga tsofi sun Fara mikewa a kidime Hakan ya sake daga hankalin sa batare daya saurare su ba shima ya fada gidansa a tamanin, sanadin daya sake firgita gyatumin Nan kenan Nan suka Fara cakala kafa dakyar Suna gudu wasu ma ko sandunan su Basu dauka ba Hakan ya jawo yawanci wasu daga ciki suka Fara faduwa a hanya Amma mgnr JIDDE idan sun tuna ke sake dimauta su dole kowa yyi ta kansa kafin kace me Duk kauyen an kidime samari da Yara tsoffi da manya maza da mata kowa ya shige cikin gidansa batare daya san asalin meya jawo Hakan ba sudai sunji ance samudawan Aljanu sun kawo masu sammaci.

Acan gidansu JIDDE kuwa lkcn data fada gida Abuwa babbar matar mlm idi a yanzu wacce ada itace ta biyu saidai sanadin Rashin uwar JIDDE yasa yanzu ta Zama itace babba a matan sa tana gaban murhu tana iza wuta dake itace da girki taga fadowar JIDDE, tsaki me daci Taja tanajin kamar taje ta rufeta da duka saidai ba halin Hakan Dan karyane a taba JIDDE ta mlm idi me gari a zauna lfy, furucin da JIDDE take yasa kanta ya kulle domin sanda ta fada gidan fada musu take kowa yyi ta kansa Basu fahimci Abinda take nufi ba Saida suka ga fadowar mlm Idi gidan hankalin su ya tashi, a kidime suka Fara shigewa dakunan su batare da sunsan ba'asin mgn ba,

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now