K' A S A I T A [10]

290 11 0
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)



*Yadda bakya gajiya wajen yimin cmmnt bazan Yi jinkiri wajen mallaka miki Wannan page din ba MUMMYN ILHAM, Thank you😘*


By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv


10....

Hannayen ta daya Sha Jan lalle tasa hannu ta rufe idonta cike da kunyar hada ido dashi, murmushi yyi yace, marayamana sarkin kunya yaudai ai sai a Barni na more kallon gimbiyar tawa Koh?" Oh Allah itadai yareema Yana sata jin kunya, tattausan hannunsa yasa ya zame hannun nata sai gashi ta rintse ido tana murmushi, shima murmushin yyi cike da kaunarta yace, "tashi muyi sallah" ba musu haka ta Mike dama da Alwala a jikinta haka ya shige gaba tana bayan sa ya jasu sallah, Bayan ya idar da sallar ne ya juyo Yana dubanta cike da shauki ya dafa kanta data sunkuyar kasa a nutse ya dinga karanto Addu'o'i daya kamata ango yyiwa amaryar sa a daren farko sosai yyi masu Addu'a Yana fatan Allah ya sadashi da Alkhairin ta yyi Masa tsari da akasin sa hakadai yyi ya Gama marayama na amsawa a ranta da Ameen.

Tashi yyi ya matso da kwarya wacce ke cike da madarar nono zallah ya dire a gabanta sannan ya matso da kwaryar zuma itama ya dire a gabanta akushin dake gefe shima ya dauko Wanda yake shake da soyayyan naman dawisu shima ya aje, dago fuskar ta yyi Yana dubanta duba na soyayya da kauna cike da kasala yace, "gimbiyata ki kalleni koda sau dayane Mana ko naji Sanyi a Raina" ba yadda maryama ta iya domin itama cike take da zumudin ganin kyakkyawan angon nata kunyace kawai yasa ta kasa kallon sa, a nutse ta dago dara-daran idonta masu masifar kyau da walwali ta dire kan nasa kyawawan fararen idon nasa masu sheqi, tuni suka sarke juna da kallon soyayya yyinda bugun zuciyar su ya ninka Akan da, karfin Hali na maza yasa yareema Ibraheem yyi kissing kan pointed nose dinta Yana Lumshe ido, itama Lumshe idon tayi tanajin tsigar jikinta na tashi, dagowa yyi ya jawo Duk Abinda ya aje gabanta ya dago kwaryar nonon 'yar madaidaiciya yakai bakinsa a nutse yyi Bismillah ya kurba kafin ya mikawa marayama a baki cike da soyayya yasa daidai Inda yasa bakinsa itama ta kurba a nutse, tun daga haka suka Fara Shan madarar nonon da gasasshen naman dawisun suka dinga ci Suna jifan junan su da kallon kauna me narkar da zuciyar masoya, bayan sun Gama suka dora da tatacciyar zuma mekyau da gardi, rada yareema Ibraheem yyiwa maryama a kunne sai gashi ta sunne kanta a kasa shikuma yyi 'yar dariya Yana mikar da ita yace,

"kinsan Wani Abu?" Ta girgiza kanta alamar a'a, murmushi yyi ba zato kawai sai ji tayi yyi sama da ita ya Fara taku a hankali yyi uwar daki dasu, wayyo Allah kunya kamar Maryam ta nutse irin Wannan shammata haka? Yana direta bisa lallausan gadon su ta rufe fuskar ta, yareema Ibraheem yace, "nasha ganin turawan london Suna daukar matansu abin ya birgeni kwarai Hakan yasa nasa a Raina Duk ranar Dana mallaki Rabin ruhina da hannaye na zan kaita lumbun amarcin mu" "Oh ya salam!" maryama ta furta Hakan a fili batare da tayi zaton Hakan ba, murmushi yyi Yana duban ta yace, "Yah Ibraheem Yana baki kunya Koh?" Maryama ta Girgiza kanta a hankali yareema Ibraheem yace, "that's why tun farko nace banason yayan Nan a canja min Suna pls" maryama tayi shiru haka take Allah ya Bata kunya tun farko kuma gashi abin ya hade mata da miskilanci bata da surutu sosai, duko kansa yyi daidai saitin kunnen ta yace, "kinajin Abinda nace kuwa?" Yyi mgnr Yana goga hancin sa bisa gefen kumatun ta, "uhummm....uhummm....eh" maryama ta furta Hakan da sauri sbd yadda taji salon mgnr tashi ta canja, murya can kasan makoshi yace, "pls ki nutsu just wanna teach u something...." Ya kare zancen da canja tashar hirar.

Washe garin ranar kuwa dakyar ta iya hada ido dashi Hakan ma Saida ya fitine ta da tsokana kafin ta ware badan taso ba ita har mmki take dama yareema Ibraheem haka yake? Koda yake Sarki shi a waje yake mulki a gida kuwa mata ke juya Alkalamin, mama fulani tayi murna kwarai da samun surukar kirki domin marayama sosai take kula da mama fulani kamar ta goyata tana sonta sosai tamkar mahaifiyar ta Hakan ya Kara mata kima da daraja a idon hubbynta Yareema Ibraheem, ya zame mata masoyi na gasken gaske idan Suna tare sai kace ba yareema Ibraheem me ji da kansa da tinkaho ba, a dole Saida ya sabar mata kansa ya zame mata jiki idan Baya tare da ita kamar marar lpy Suna son junan su kwarai d gske shiyasa take Alfahari dashi a matsayin mijinta na aure, bangaren su sarki Audu da Hajia Uwani kuwa abin ya danyi sauki zuwa yanzu kusan wata uku kenan Suna kokarin danne kiyayyar su game da yareema Ibraheem sbd Wani irin mugun kulli da suke shiryawa kwana da kwanaki ba ga sarki Audun ba baga su Hajia Uwani ba kowa dai kokarin sa shine ya samu damar zaman kujerar Nan har karshen rayuwar sa.
*****
Kamar ko yaushe Suna zaune a parlon mama fulani bayan dawowar yareema Ibraheem daga fada Suna Shirin cin abincin dare Ana bude kwanon abinci Maryama ta rufe hanci da sauri, diban abincin aka Fara Yi kamshin ya bulale dakin sai gashi maryama ta Mike da hanzarin ta da sauri mama fulani da yareema Ibraheem suka Mike tsaye da sauri Suna tmbyr lafiya? Bata iya Basu Amsa ba sbd yadda taji 'ya'yan hanjin cikinta na juyawa da sauri tayi hanyar bayi saiga yareema Ibraheem ya cimmata shima jikinsa na rawa, mama fulani hankali tashe ta Kira wata kuyangar ta asabe Tace taje ta Kira mata me kula da marasa lpy da sauri kuyangar tayi waje mama fulani ta juyo garesu kirjinta na bugawa Tace,

"lafiya dai Koh?" Maryama na cije lips bayan sun iso gabanta yareema Ibraheem na rike da hannun ta ba ko kunya yace, "Kiyi mgn plss" maryama Tace, "kamshin wainar can ya tadamin zuciya wari takemin sosai" Ta Ida mgnr tana komawa mazaunin da suka tashi dazu Dan batason jin kamshin wainar kuma, kuyangar da mama fulani  ta aika ce ta dawo Tace, "Allah yaja da ran mama sarauniya malamar lafiya na tafe" mama fulani Tace, "toh ku kwashe Duk abincin Nan dake Nan waje ayi waje dashi" kuyangar ta Girgiza Kai cikin ladabi ta nemo 'yan uwanta kuyangi suka Fara fitarwa da kayan abincin da suka jera.

Cikin Rashin fahimta yareema Ibraheem yace, "Koh dai Wani Abu kikaci ya Bata miki ciki?" Yyi tmbyr da damuwa sbd yasan yadda takeson wainar Masa wacce taji miyar tantakwashi, Girgiza Kai maryama tayi tana Lumshe ido haka Nan taji jikinta ya saki kamar wacce take cikin ciwo tuntuni, mama fulani kuwa dogon nazari ta tafi tana Addu'ar Allah yasa hasashen da take yanzu ya Zama gsky, Matsawa tayi dab da ita tana dafa bayanta Tace, "karki damu yanzu Malamar lafiya zatazo saita dubamin ke" Dan murmushi tayi cikin karfin Hali Tace, "ai da ba'a Kira ba ummi naji sauki" ummi Tace, "a'a gwara dai muji meye matsalar" Suna haka Malamar lafiyar ta iso bayan ta nemi izinin Shiga aka Bata dama, tambayoyi sosai tayiwa maryama tana Bata Amsa daga karshe ta umarci da tayi fitsari Dan tanason yin gwaji, haka maryama tayo fitsari ta Bata tana gwadawa da minti biyar Malamar lafiya ta Tabbatar da zargin ta na samun karuwa, bakinta a washe ta dubi mama fulani da tayi jugum tana jiran tsammani tace, "Allah ya taimaki mama sarauniya uwa ga yareeman Dutse sarki gobe da yaddar Allah Cikin hukuncin Ubangiji an samu karuwa gimbiya maryama Allah ya Albarkaceta da samun jaririn ciki" wayyo Allah fadin irin yadda Ahalin cikin Nan suka Shiga murna Bata lkci ne domin Kuwa bakinsu har kunne Dan murna, Malamar lafiya kuwa ta samu kyauta me tsoka kyauta wacce ta Amsa sunan kyauta kafin kace me tuni labari ya zagaya masarautar Dutse da kewayen ta.

Hankali a mugun tashe yareema shu'ayb ya Shiga bangaren Hajia Uwani, tsaye ya tarar da ita sai Kaikwo take kamar wadda aka yiwa rasuwa domin tunda taji mgnr cikin maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye tamkar ta hadiyi icce, yareema shu'ayb ya rufe kofarta Yana kokarin daidaita nutsuwar sa yace, "ummah..." Hajia Uwani ta dakatar dashi da daga Masa hannun ta tana duban sa ranta a bace Tace, "Dan meyasa na baka damar ka shige jikin yareema?" Yareema shu'ayb na kokarin danne zafin dakatar dashi da tayi yace, ""sbd nasan sirrin sa" Mtwsss Taja tsaki kamar ta mareshi Tace, "Kai wanne irin malohon mutum ne da har akayi Wannan shegiyar matar meji da kan tsiya ta samu ciki a cikin Wannan masarautar da muke burin ta Zama tamu cikin karfi da yaji?" Cikin jin haushi yareema shu'ayb yace, "toh ummah Duk sa idona a kansa zan hanashi take matarsa ne?" Ummah ta banko Masa harara Tace, "Tho bari kaji Wallahi Koh Ana ha maza ha mata sai mun kwato sarautar Nan da karfin tsiya ban damu ba koda za'a Rasa Rai ne.

*Wattpadians pls...*
#vote
#cmmnt👏🏻

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now