K' A S A I T A [6]

402 10 0
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEEER_)

By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv



6.....

"Ahh.. nothing" Ahmad ya furta Hakan Yana murmushi, "kaji dai da gulmar ka" Yareema Ibraheem ya furta Hakan Yana mikewa kan gado hade da Lumshe ido tarrr ya hango kyawawan idonta cikin nasa Suna Masa gizo da sauri ya bude idon nasa Yana duban bakin kofa daidai lkcn da Ahmad yaja kofar ya fice kenan Kama kansa yyi Yana girgizawa a hankali yake furta "What is wrong with you Ibrahim?" Ya fada Yana Dan cije lips dinsa a hankali, a takaice dai Ibraheem kusan kwana yyi Yana juyi Akan gado Duk sanda ya rintse idonsa ba Abinda yake gani sai hasken idonta. Washe garin ranar tunda Ibraheem ya Shiga part din maman su Ahmad yake dubawa a sace ko zai ganta saidai har suka fito da Ahmad bega koda kyallin ta ba, shigar sa bayan mota kenan Yana dagowa ya hango ta can saman beni ta makale tana leken sa a hankali, wara Mata manyan idonsa yyi da sauri tasa tafin hannayen ta biyu ta rufe sbd kunyar kamata da yyi tana kallon sa, murmushi ne ya subuce Masa saiji yyi Ana tafi a bayan sa da sauri ya juya ya kalli Ahmad da yake tafin Yana dubansu, Dan hararar sa yyi yana tabe baki yace, "kai nifa bansan lkcn daka Fara Zama me sa ido ba" er dariya Ahmad yyi Yana Dukawa jikin window mota yace, "haba Aboki irin Wannan Kama Kai haka?" Ibraheem yace, "Kama Kai kamar ya?" Ahmad yace, "Naga sai Surutu kke bansan Inda yasa gaba ba" saurin zuge glass din motar Ibraheem yyi cikin mazewa yace, "toh naji munafiki dallah matsa kada na Bata lkci Banga ummi ba" Ahmad na murmushi yace, "Dan ummi a gaida ummi sauran mgnr zamuyi waya Dan nasa akwai maganganun daka kunshe a ranka zaka tafi dasu" Dan murmushi Ibraheem yyi Yana sake duban Inda take a sace yaga Bata wajen sai kawai ya daga Masa hannu alamar bye, Nan driver yaja mota a nutse har suka bar harabar gidan kafin suka hau babban titin dazai sadasu da hanyar Jigawa Tarin Allah.

****
"Dakata memartaba kada ka bamu kunya Mana" cewar Boka Markuz bayan ya Gama sauraron Abinda sarki Audu ya fada Masa game da dawowar yareema Ibraheem, Dan sauke ajiyar zuciya memartaba Audu yyi Yana dafe kirji yace, "Wlh hankali nane ya tashi shiyasa ka ganni a gigice" Tsaki Boka Markuz yyi yace, "sai akayi me kuma? Dawowar tasa shine zaisa ya karbi mulkin?" Sarki Audu yace, "a bisa yarjejeniyar da mukayi kenan idan ya girma a bashi sarautar sa toh ni Kuma har ga Allah banason tashi daga kujerar Nan yanzu"

Boka Markuz ya fashe da dariya Yana dukan cinyar sa yace, "Mulki kenan ga zaqi ga gardi Duk Wanda Baya Mulki besan Dadi ba, Wanda yake Mulki kuwa Koh mulkin kashi ne sai yaji kaunar sa" Sarki Audu na washe baki yace, "kaima dai ka fada Boka shiyasa nakeson asan yadda za'ayi kada na sauka a kujerar Nan" Boka Markuz yace, "Baka da matsalar Wannan kaidai Abinda nakeso dakai ka kasance me bani yadda da amincewa a koda yaushe" Sarki Audu yace, ai ni tuni na Gama mika dukkan Al'amurana gareka Boka" Boka Markuz ya bushe da dariya Yana gyada Kai yace, "tashi kaje Kai da barin kujerar ka sai idan mutuwa kayi" a razane sarki Audu yace, "me kke nufi Boka?" Boka Markuz yace, "ina nufin bazaka sauka a mulkin Nan ba har lkcn da rai yyi halinsa kamar yadda dukkan sauran sarakuna suke dole sai sun mutu kafin Wani yahau"

Cikin tsananin farinciki sarki Audu yace, "gsky ban taba jin mgnr data sanyani jin Dadi Duk duniya ba sama da Wannan mgnr ka Fadi ko me kkeso Boka nikuwa na maka Alkawarin zan idar maka shi" Boka Markuz ya fashe da dariya kafin ya hade fuska Yana duban sarki Audu yace, "kaima kasan halina Duk Abinda nakeso zan maka mgn basai ka tmbyeni ba" Sarki Audu yace, "Wannan haka yake kuma Ina sake godiya a gareka ni zan tafi" Boka Markuz yace, "Madallah" Nan sarki Audu yabar wajen zuciyar sa fari tass kamar an wanke da ruwan Sanyi.
~~~
Gagarumar walima sarki Audu yasa aka shirya domin tarbar Yareema Ibraheem, idan kaga yadda yake washe baki sosai abin zai baka mmki Matuka toh ba komai yasashi sakin jikin Nan ba saidan maganganun da sukayi da boka markuz jiya domin ya Tabbatar Masa da shi da rabuwa a mulkin Nan sai mutuwa shiyasa ya saki ransa kwarai Yana haba-haba da zuwan yareema Ibraheem.

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now