K' A S A I T A [2]

756 24 0
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_ )

By
*Nuceeyluv😘*


2...

Har zuwa Wannan lkcn kowa kallon sa yake da mugun mmki yyinda mlm Abdulhakim ya dukar dakai cikin dabara ya Fara murza zoben hannun sa a hankali cike da fatan Allah yasa Shirin sa da yyi kwana uku yanayi wato tun bayan rasuwar sarki ya tafi daidai zuciyar sa sai bugawa take Dan besan amsar da za'a bashi ba.

"Ko zaka iya gaya Mana dalilin dayasa kkeson karbar Wannan mulkin?" Yareema Ibraheem yyi mgnr cikin nutsuwa yyinda kowa na wajen ya juya a firgice jin Abinda ya furta, wata irin boyayyar ajiyar zuciya mlm Abdulhakim yyi Yana ganin kamar Hakan sa Yana dab da cimma ruwa yyi murmushi a takaice Yana sake dukar dakai yace, "Allah ya karawa yareema lpy da nisan kwana ba komai ya sani sha'awar karbar mulkin Nan ba face kwadayi da romon samun ladar shugabantar Al'umma, na Tabbata Duk Wanda yyi shugabanci da gsky Al'umar sa basuyi kuka dashi ba Ana Masa kyakkyawan zato bayan mutuwar sa, Dan haka nake sake rokon Wannan masarauta tare da amincewar yareeman masarauta da a bani damar Wannan RIKON KWARYAR har Allah ya kawo lkcn dazan mayarwa me ita."

shiru wajen yyi mutanen wajen Suna gyada Kai bisa jin maganganun mlm Abdulhakim da sukayi shikuwa mlm Tanimu bakinsa a hangame yake bin abokin nasa da kallo da mugun mmki, Yareema Ibraheem besan ya akai ba Amma tashin farko yaji gaba1 ya aminta da Abdulhakim Gana, cikin matukar amincewa da nuna goyon baya yareema Ibraheem ya kalli bafaden dake gefensa ya gyada Kai cike da izza Kai kace Wani babbane me shekaru, bafaden dake gefensa ya dubi Mlm Abdulhakim yace, "rokon da kayi ga Wannan masarauta ya karbu"

Nan kowa na wajen suka Fara Surutu wasu na goyon baya wasu na amincewa toh Abu dama na mutane ba lalle ra'ayi yazo daya ba, cikin tsananin farinciki mlm Abdulhakim ya tako daga can Inda yake ya matso tsakiyar Inda aka zagaye gaban Yarima tamkar zai rungume shi fadawa suka tare da babbar Riga Fadi suke hattara dai, sai a lkcn ya nutsu Yana daidaita Zaman sa yace, "na gode Kwarai dgske yareema, tabbas Banda Abinda zan saka maka saidai nayita maka Addu'a Allah ya jikan magabata Allah yaja da ran Ka har lkcn da zaka amshi sarautar ka na gode sosai"

Lumshe ido yareema Ibraheem yyi Yana me jingina ga kujerar da yake zaune bafaden yareema yace, "yareema ya Amsa maka" cikin murna Abdulhakim ya sake risinawa Yana godiya kafin ya juya ga ilahirin mutanen wajen Yana godiya a garesu bayan shudewar sa'anni Ana fadanci hade da mgn Akan sabon Al'amarin RIKON KWARYAR Mlm Abdulhakim aka rufe taro da Addu'a bayan ansa ranar nadin sarautar sabon  Sarki wato Abdulhakim Nan da kwana bakwai masu zuwa.
~~~
Fuskar ta cike take da tsananin bacin rai tanajin kamar ta wanka Masa Mari Dan takaici Tace, "Dan meyasa zaka yanke hukunci batare da sani na ba?" Har yanzu kansa a kasa yake ya kasa dagowa ya kalleta tun bayan barowar sa fada Yana Shiga cikin gidan ko daidaita zamansa a kan gadon dakinsa beyi ba yaji bankowar kofar ta tunda ya kalleta sau daya ya dauke da sauri be sake kallon ta ba sbd yadda fuskar take a murtuke,

"Wai ba mgn nake maka ba Ibraheem?" Karo na biyu kenan daya dago kansa kirjinsa na bugawa Dan idan zai iya tunawa to tabbas ya mance rabon data kirashi da sunan sa Kai tsaye, cikin matukar kankan dakai da nuna girmamawa ga mahaifya yace, "Kiyi hakuri Ummi bansan Hakan zai Bata miki rai ba tabbas nayi kuskure wajen yanke hukunci cikin gaggawa Amma yanzu ma Bata baci ba sai nasa a soke zancen" tsaki mahaifiyar tasa Taja tana me Zama gefensa cikin matukar takaici Tace, "kasan me ake Kira da sarauta kuwa yareema? Tun kana karamin ka kanaso ka halaka kanka da kanka?" Cikin Rashin fahimta yace, "me kike nufi ummi?" Dan dogon numfashi Taja me sauti kafin Tace, "mutumin Nan daka damqa Masa amanar masarauta kasan waye shi? Kasan daga Ina ya fito? Kasan asalin sa? Ko kuwa Rasa amintattun mutane akayi cikinmu zaka jefamu Inda zamu Shiga uku?" Cikin matukar rudewa irinta Yarinta yareema Ibraheem ya Mike jikinsa na rawa yace, "cewa yyi zai rike mulkin da gsky ummi, yace kuma kwadayin lada yake bari naje fada na sanar an fasa nada shi" jawo shi tayi ta kwantar Amma har yanzu jikinsa rawa yake hankalin sa a mugun tashe,

Ummi tace, "ba haka akasan halin Adalin yareema sarkin Gobe ba, ba'asan sarakuna da saba Alqawari ba, Ina horon ka da Duk rintsi kada ka Zama me saba Alqawari Koh Rashin gsky, ka kasance a koda yaushe kana riko da gsky Yareema Sannan kayi iya kokarin ka kada ka sake ka zubar da mutuncin ka domin Duk Wanda ya kasance Yana saba Alqawari a hankali mutuncin sa da kwarjinin sa zai Fara zubewa a idon mutane" Shiru dakin ya dauka bayan ummi ta Gama zancen ta da mintuna kadan yareema ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa da kalaman ta yace, "Nagode ummi Allah ya saka da Alkhairi" ummi ta sauke nata ajiyar zuciyar itama tace, "yanzu dai sake yimin bayani a nutse yadda kukayi a fada" sake nanata mata yadda sukayi yyi a hankali take binsa da kallo cike da gamsuwa da bayanan sa Kai kace Wani babban mutum ke mgn toh abinka da yaro me zuciya da Hali irin na manya hankali da wayo yafi karfin shekarun sa, "Toh Masha Allah" ummi tace tana murmushi hade da shafa kansa Tace, "Allah yyi maka Albarka Yareema, Allah ya nuna min lkcn da sarautar zata dawo hannun ka." shima murmushi yyi Yana rike da hannun ta yace, "Insha Allah ummi."
~~~~
Tunda suka Kama hanyar komawa fagoji mmki bebar mlm Tanimu ba har ya kasa shiru cikin hanzari ya shige gaban mlm Audu, mlm Audu dake tafe cikin farinciki yaja ya tsaya cak Yana duban mlm Tanimu cikin jin Dadi yace, "da alama yanzu ka shirya mgn kenan" ya Fadi haka Yana washe baki Dan tun dazu mlm Tanimu be iya ce Masa komai ba har suka hau hanyar komawa gida, Jan numfashi me sauti mlm Tanimu yyi daga bisani yace, "mlm Audu me kke nufi da karbar sarautar RIKON KWARYAR Nan?" Murmushi mlm Audu yyi yace, "Koh akwai lefi a cikin Hakan?" Mlm Tanimu yace, "tabbas bakayi lefi ba Amma abin dubawa shine Kai dinnan kwata2 badan kasar Dutse bane sannan ba a GARU kayi masauki ba kana ganin Wannan karbar mulkin da kayi bazai zame maka matsala ba?" Dan rage fara'ar sa mlm Audu yyi yace, "so kke kayimin gorin gari ko me kke nufi?" Mlm Tanimu yace, "Sam ba Abinda nake nufi ba kenan, Abinda nakeso ka fahimta shine kada giyar mulki tasa ka cuci Wanda suka baka amanar sa domin ita kujerar mulki zaqi ne da ita tabbas mutum baya sanin haka saiya hau ta domin a lkcn sababbin buri zasuyi ta karuwa a zuciyar mutum haka zalika idan kaunar mulkin ya shige shi sosai tofah matukar baya mutu ba bayajin zai iya sauka daga Wannan karagar mulkin musamman mulkin irin na sarauta."

Dan Jan numfashi mlm Audu yyi Yana me dafa kafadar mlm Audu yace, "tun farko bada Wannan niyar na amshi mulkin ba, Aduk lkcn dame mukamin shekarun sa yakai nikuwa zan damqa mulkin a gareshi batare da jayayya ko Wani Abu me Kama da haka ba" sai yanzu mlm Tanimu yaja numfashi me sanyi Dan shi a bangaren sa tunda ya kalli yareema Ibraheem yaji Yana tausayin sa musamman da a yanzu bashi da karfin dazai gaji mafahin sa fatan sa dai Allah ya tsare su da dukiyar su har lkcn da karfin sa zai kawo. Cigaba da tafiya sukayi tunda suka karasa fagoji kowa yyi hanyar sa ta zuwa gida, tun daga bakin kofar gida mlm Audu ke rafka sallama, Uwani matarsa dake hura Wutar hayaki ta fyace majina hade da sa bakin zaninta ta goge hanci tana kallon saitin kofar gidan Tace, "haba Audu sai kace gidan kurame sai raraka sallama kke kamar an koro ka" mlm Audu dake Karasa shigowa gidan yaja tsaki "ke matsalar ki tanada yawa Uwani bakya bari kiji ba'asi sai ki Fara mgn" Dan hararar sa tayi tana ci gaba da tura Wutar karanta Tace, "toh meya faru?" Fara'ar sa ce ta karu Dan ya kasa boyewa yace, "Albishirin ki" Uwani Tace, "goro fari tass" Mlm Audu yace, "Daga yau na tashi daga mlm Audu na koma Sarki Abdulhakim Gana" zaro ido da mmki Uwani tayi sai Kuma ta fashe da dariya "haba Audu saikace a tatsuniya?" Mlm Audu yace, "ke dgske fah nake" Nan ya Fara labarta mata yadda akayi tun farko, tashi zumbur Uwani tayi jikinta na rawa tace, "domin Allah gsky kke gaya min Audu?" Mlm Audu yace, "Karya zan miki?" Wani irin guda Uwani ta saka me cike da tsantsar farinciki Tace, "Allahu Akbar Allah me hikima yau nice nake auren me martaba sarki guda?" Mlm Audu yyi murmushi Uwani taci gaba da fadin, "gaba kadan saidai kaji Ana hajia Uwani ayuririii.." ta sake yin guda kamar hancin zai cire, mikewa mlm Audu yyi yace, "bari na fita waje Ina zuwa" Uwani Tace, "toh mlm adawo lpy ka turo min keyar shu'aibu idan ka ganshi waje" yace, "toh."
***
Can cikin wani sarkakiyar daji mlm Audu ya nufa Yana Dan waige2 a haka ya tsunduma cikin wasu dutsuwa masu duhu sosai da yanayin ban tsoro tun kafin yasa kafarsa cikin kogon dutsen ya Fara jin Ana dariya kafin kace me duka dutsin wajen yadau sautin dariya, "gafaran ku dai" mlm Audu ya furta Hakan, cikin wata irin murya marar dadin ji bayan an daina dariyar akace "ni da ilahirin tawaga ta muna Taya Audu Gana samun nasarar Zamtowa sarkin GARU na kasar Dutse" murmushin farinciki yyi Yana gyada Kai kamar kadangare yace, "Godiya nake boka markuz, haka zalika Ina sake mika godiya ga tawagar boka markuz lalle na amince da aikin ku domin kuwa haka yakeci tamkar yankan wuqa.

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now