K' A S A I T A [1]

2.2K 62 1
                                    

*K' A S A I T A*

ALHAMDULILLAH, Dukkan Godiya da daukaka sun tabbata ga Allah S.W.T cikin Amincin sa da yaddar sa ya sake bani damar sake dawo wa a Wannan karon tafe da sabon Novel dina KASAITA, Ina rokon Allah S.W.T ya bani ikon rubuta daidai Wanda zai amfani dani daku masu karatu baki1 Ameen, Masoyana na kusa Dana nesa Aduk Inda kuke Ina miko sakon gaisuwata a gareku NUCEEYLUV har kullum tana yinku irin sosai dinnan😍🤝🏻

By
*Nuceeyluv😘*

1...

*1967*

A shekarar Alif dubu daya da dari tara da sittin da bakwai, shekara ce me dunbin tarihin da Duk Wani Dan kasata Nigeria bazai taba mantawa da ita ba gaduk me bibiyar tarihin kasar yasan a Wannan shekara aka tafka asarar rayuka fiye da miliyan guda wato lokacin YAKIN BASASA,

A Wannan lokaci ba karamin tashin hankali aka Shiga ba ciki kuwa harda tarwatsewar Al'umma, A irin Wannan tarwatsewar ne ya Samo asalin barin Abdulhakim Gana daga jihar sa ta Maiduguri ya famtsama izuwa kasar Dutse, Jihar jigawa,  A Wannan zamani lkcne da dukkan mutanen Nigera wasu ke hijrah daga Wannan waje zuwa Wannan waje Inda ya maka ka samu ka zauna, Babu ko shakka Abdulhakim Gana Ya samu matsugunni a kasar Dutse,
Anan wata unguwa da ake Kira fagoji, Inda take dab da GARU unguwar masarautar Dutse domin Basu da nisa ainun,

A wancan zamanin Kai tsaye zakace fagoji gari ne daban domin lkcn ba Wani jama'a ne sosai a wajajen ba haka zalika ba'ayi cikar datakai yanzu ba, Dan haka a wancan zamanin ya kasance Fagoji da unguwar sarki wato GARU kowanne gari ne me cin sunan kansa, Abdulhakim Gana Allah yyi Masa masaukin sa anan garin fagoji ta kasar Dutse, tunda Abdulhakim yyi nazari sosai ya fahimci tabbas duka dangin sa na Maiduguri sun tarwatse yasan cewa Abu ne me matukar wahala ace sun sake gamuwa bare Abu da ake cikin tashin hankali wasu na raye wasu na mace? Allah masani, toh uwa uba ma shi da baida gata Dan Maraya ne shiyasa kawai ya saki jikinsa ya Fara neman Abinda zai rufawa kansa Asiri, bayan shudewar lokuta Abdulhakim Gana ya Zama cikakken Dan gari harma yyi Aure da samun karuwar Yara Wanda a kallah bazasu wuce shekaru biyu zuwa hudu ba a kasar Dutse.

Tafe yake da fartanya a kafadar sa dawowar sa daga gona kenan ya hango abokin sa Mlm tanimu yanata zabga sauri da alama be lura dashi din ba ganin haka Abdulhakim ya kwalawa tanimu Kira Fadi yake, "Kai mlm Tanimu lpy kke ta zabga sauri haka inata kiranka baka Amsa ba" Yyi mgnr cikin daga murya Dan ya lura mlm Tanimu beji Kiran da yake Masa ba tun farko, juyowa mlm Tanimu yyi da sauri yace, "Aff.. Mlm Audu Ashe kana bayana ban lura ba hankalin yyi gaba" mlm Abdulhakim ya gyara zaman kafadar sa yace, "lpy dai Koh?" Cikin yanayi na jimami yace, "inafa lpy Mlm Audu?" Yaci gaba da fadin, "yanzun Nan muna majalisa aka Aiko da sarkin GARU ya rasu bakaga yadda kowa ya girgiza da mutuwar sarkin Nan ba mutumin Arziki shiyasa nake ta zabga sauri naje gidanka mu tafi tare can wajen janazar" salati Audu Gana yyi cikin jimami yace, "yanzu kuwa zamuje GARU Dan Zama Sam be Kama mu ba Allah sarki, me martaba Sulemanu kwana ya kare Allah dai ya jikansa" "Ameen" mlm Tanimu ya furta.

Waigawa Mlm Audu yyi ya hango yaronsa shu'aibu na tafe yace, "kai shu'aibu zo Nan" shu'aibu ya taho da saurin sa, Mlm Audu ya mika Masa fartanya hannun sa yace, "kaimin gida" bayan shu'aibu ya tafi mlm Audu ya dubi mlm Tanimu yace, "muje" mlm Tanimu ya gyada Kai Nan suka Fara tafiya dake a wancan zamanin ba abin Hawa sosai koda yake abin hawar Amfi amfani da doki ko jaki Saidai dukda haka mutanen Da Basu dauki doguwar tafiya a kafa a bakin komai ba Hakan yasa suka saba da tafiyar kafa.

Suna cikin tafiya Mlm tanimu yaja dogon numfashi kafin yace, "Allah sarki yanzu ko waye zai maye gurbin sarki kuma?" Mlm Abdulhakim yace, "bashi da dangi ne?"
Mlm Tanimu yace, "yanada yaro Ibraheem saidai beyi girman da za'ace za'a damqa Masa mulki a hannun sa ba" shiru mlm Audu yyi Yana tunani bece komai ba da haka sukaci gaba da tafiya har suka kaiga zuwa garin GARU,

Lkcn da sukaje Ana Shirin Kai sarki makabarta haka sukabi mutanen dake tafe da gawar, bayan an dawo daga Kai sarkin mutane suka taru a fada Ana karbar gaisuwa, Can gefe guda kuwa Yarima Ibrahim ne zaune ya kifa kansa idonsa yyi jajir baya ma iya furta komai sai iya fadawan ke Amsa mutane, cikin haka kuwa harda su mlm Abdulhakim zaune can gefe Suma Suna karbar gaisuwa a haka suka jera kwana uku Suna zuwa wajen har mutane na mmkin su mlm Tanimu ma bisa tilastawar Mlm Audu yake zuwa wajen Sam besan dalilin Hakan ba, bayan an Gama karbar gaisuwa ta sadakar uku anyi Addu'a, kafin kowa ya tafi aka Fara mgnr Waye zai maye kujerar sarki? Bisa duba da sukayi da kankantar Yarima Ibraheem me shekaru Sha uku (13) dole a samu babba me hankalin dazai jagoranci jama'a,

Kowa na wajen yyi tsam da ransa Yana juya mgnr da ake tattaunawa akai, a Wannan zamani kowa kokari yake ya guji duniya da tunanin kada ka kasa rike amanar mutane kaje Lahira kayi bayani shiyasa kowa ya kasa cewa komai Yarima Ibraheem nakan kujera har ila yau bayace komai kansa a sunkuye yake, shiru yyi yawa yyinda a bangaren Abdulhakim Gana yake ta motsa baki ya kasa furta kalma ko daya domin Abinda yake ta sakawa a ransa kenan tun ranar da sukayi mgn da mlm Tanimu wasu tunani ke yawo a kansa game da masarautar, Ganin shirun bazai amfane shi ba Hakan yasa shi daga hannu alamar yanada mgn,

kowa na wajen binsa yyi da kallon mmki, Amma dai an bashi dama domin mafita ake nema, cikin Nutsuwa yace, "idan Babu damuwa Ina miko kokon barata ga Wannan masarauta data bani damar karbar rikon sarautar Nan har Allah ya kawo shekarun Yarima Ibraheem ya karbi sarautar sa wato bima'ana RIKON KWARYA."

A razane dukkanin ilahirin wajen suka dago kansu Suna kallon Wannan bakon mutum da karfin Hali, yyinda yareema Ibraheem karon farko ya dago kwayar idonsa cike da izza da nuna Shidin jinin sarauta ne da kwarjini irinna  *K' A S A I T A*


*NOTE#*
A Wannan karon banyi Alqawarin zan dinga dogon page ba sbd wasu dalilai, bayan haka Wannan littafin daga farko har Inda Naga zan tsaya *FREE PAGE* ne, ma'ana littafin kudi ne, idan lkci yyi zansa amount da account number Ina fatan kowa ya fahimta🥰.

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now