K' A S A I T A [9]

314 8 0
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)



By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv

9....

Lumshe ido yyi a hankali yanajin dukkan gabobin jikinsa Suna Amsa sallamar da tayi Masa cikin zazzaqar muryar ta, ko ba'a fada ba yasan sister din Ahmad ce jin shiru ba'a Amsa mata ba yasa tayi kokarin ajewa kafin ta cire daga kunnen ta taji Yace, "Ameen wa'alaykis salam" a razane ta dubi tarho din hannunta na rawa ta kasa furta komai kokarin ajewa ma take Ahmad ya shigo wajen, "ke lpy?" Ahmad ya furta Hakan Yana duban yadda jikinta yake rawa, "am...dama..dama.. an Kira..ka..ne" tayi mgnr a rarrabe, tsaki yaja ya karbe tarho din Yana hararar ta tuni tabar wajen da sauri, Ahmad ya Kara a kunnen sa yace, "daga tafiya sai naji shiru ba amo ba labari" ya Fadi Hakan Yana Zama, 'yar dariya yareema Ibraheem yyi yace, "Taya kasan nine?" Ahmad yace, "daga wajen Maryam Mana" _Maryam..._ Ya nanata sunan a ransa a fili yace, "Maryam kuma?" Ahmad yace, "kwarai tunda Naga tana rawar jiki nasan ba'a Rasa nono a Riga" dariya ya bashi Hakan yasashi darawa kadan kafin yace, "yasu Hajia?" Ahmad yace, "Alhamdulillah Dan ummi ka sameta lpy?" Yareema Ibraheem yace, "lafiya Alhamdulillah tana gaishe ku ma" Ahmad yace, "Masha Allah" Yareema Ibraheem yace, "yayan Maryam inada mgn" Dan murmushi Ahmad yyi yace, "kunne na biyu" Yareema Ibraheem ya danyi shiru Yana nazarin Abinda zaice can kuma ya daure zuciyar sa yace, "idan Babu damuwa Ina son a hadani da Maryam" shiru Ahmad yyi kafin yace, "Yareema da kanka?" Yareema ya danyi guntun murmushi yace, "ko anyi mata miji ne?" Ahmad yace, "a'a" yareema Ibraheem yace, "so Ina ciki" Ahmad yace, "Masha Allah, Allah ya daidaita tsananin ku idan Maryam ce Kai tsaye Zance ka samu Insha Allahu baka da matsalar komai" Yareema Ibraheem yace, "Nagode sosai" Ahmad yace, "nine da godiya" Nan suka koma hirar su ta abokai Ahmad na tsokanar sa da dole ya kirashi da Yaya tunda sun Zama surukai.
~~~~
Har yanzu sarki Audu be daina waige2 ba sai duban kowanne bangare2 yake cikin rawar jiki Dan besan dalilin dariyar Nan ba, Daga can bangaren yamma da dakin sa yaga hayaki na tashi kadan ya rage be saki fitsari ba sbd tsoro saidai hayaki be dauki lkci ba Boka markuz ya bayyana a wajen daidai lkcn da Amon Wannan dariyar ya daina tashi, wata irin wawiyar ajiyar zuciya ya saki Yana duban Boka markuz yace, "gsky ka firgita ni Boka" Boka markuz fuskar sa a hade yace, "yimin shiru" a sukwane sarki Audu yyi kasa da kansa Yana Dukawa gaban Boka markuz yace, "tuba nake boka" Boka markuz ya yatsina fuska yace, "meyasa kke neman ruguza Mana aikin mu?" Sarki Audu yace, "aikin me?" Boka markuz yace, "daga Dan maganganun da kukayi har ka gigice kana hauka a daki kalli yadda ka hargitsa ko Ina na wajen fah?" Sarki Audu yace, "hankalina ne ya tashi shiyasa na zauce" tsaki Boka markuz yyi yace, "Ashe bakayi imani da Abinda nake sanar maka ba?" Sarki Audu yyi shiru kansa a kasa, Boka markuz yaci gaba da fadin, "tun farko na sanar dakai Kai da sauka kan kujerar mulkin Nan sai kwanan ka ya kare Amma meyasa zaka daga hankalin ka kan Dan karamin Abu daya hada ku?" Sarki Audu yace, "tuba nake Hakan bazai sake faruwa ba" sake Jan tsaki Boka markuz yyi yace, "matukar bazakana yin imani da Abinda na fada maka ba zamu raba hanya dakai" dagowa sarki Audu yyi a firgice yace, "udan ka sakeni ya zanyi?" "Ohon maka" Boka markuz ya Fadi Hakan cikin takaici, sarki Audu yace, "Daga yau bazan sake yin Abinda bakai kace nayi ba" Boka markuz ya saki ransa kadan kafin yace, "Yareema Ibraheem bazai taba Hawa kujerar mulkin Nan ba domin nayi bincike a halwar tsafina na gano Hakan Dan haka ka kwantar da hankali ka kaci Karen ka Babu babbaka Duk Wanda yyi yunkurin tunkarar kujerar ka saidai Wani bashi ba" Dadi ne ya Kama sarki Audu sosai ya washe baki yace, "hankalina ya kwanta Wallahi shiyasa nakeji dakai Boka" Boka markuz ya miko Masa Wani madubi yace, "karbi Nan" karba sarki Audu yyi Yana juya madubin dake walwali a hannun sa, Boka markuz yace, "Wannan madubin kawo maka shi nayi sbd ka rage zirga-zirgar zuwa wajena domin gudun sa ido na mutane kada watarana a gano Inda kke zuwa Dan haka Duk lkcn daka bukaci mgn dani Koh Wani Abu da kkeso cikin gaggawa toh ka dauko Wannan madubin ka shafo Al'aurar ka da tafin hannun ka sai kayi amfani da hannun ka shafi Wannan madubin a take zaka ga na bayyana zamuyi mgn tamkar yadda mukeyi yanzu kagane?"

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now