K' A S A I T A [8]

287 8 0
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)



By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv


8.....


Wani irin qululun takaici ne ya makure makogwaron Sarki Audu, saidai yyi iya bakin kokarin sa wajen boye fushin sa sosai yana duban yareema Ibraheem fuskar sa da murmushin yake yace, "kayi gsky Yareema mgnr ka haka take" tabe baki yareema Ibraheem yyi Yana sauke kafarsa a hankali sannan ya harde hannayen sa bisa kirjin sa cike da izza yace, "meye dalilin ka na Sanya dokar cire takalmi idan mutane zasu wuce ta Gefen masarauta?" Kirjin sarki Audu ne ya buga da karfi, cikin mazewa yyi 'yar dariya Yana fadin, "haba yareema da kanka kke min Wannan tmbyr?" Kallon mmki yareema yyi Masa yana wara idonsa yace, "bani da hurumin tmbyr Abinda ke faruwa a masarautatane?"

Sarki Audu na yake yace, "ko kadan ba Hakan nake nufi ba yareema ai matsayin kane Hakan" "So ina son naji dalilin musgunawar da kayiwa Al'ummata bayan bana gari" sarki Audu yace, "a zahirin gsky Yareema ban musgunawa Al'ummar ka ba, saidon kawai inason na kawo cigaban masarauta ne ta hanyar banbanci tsakanin talakawan gari da gidan sarauta" Wani irin takaici ne ya Kama yareema Ibraheem yace, "Abinda nace kayi kenan?" Sarki Audu yyi shiru, yareema Ibraheem yaci gaba da fadin, "ban nanata maka cewar ka rike amana ka cika Alqawari ba?" Sarki Audu na cika da takaicin fadan da yareema Ibraheem yake yi Masa ya gimtse fuska kawai Dan idan yace zaiyi mgn zai tona Asiri zuciyar sa har yareema Ibraheem ya gano gskyr sa, Yareema Ibraheem ya Mike tsaye cikin haushin Abubuwan da sarki Audu ya gabatar na zalunci ga Al'umar sa Yana zagaye dakin a hankali can ya juyo ya zubawa sarki Audu ido cikin kaushin murya yace,

"Ayau basai gobe ba inaso kamar yadda ka Tara mutane ka kawo musu Wannan shirmen dokar inaso ka koma ka sake tara su ka sanar musu ka soke dokar cire takalmi daka Sanya" a razane sarki Audu ya dago Yana kokarin danne bacin ransa sosai yace, "haba Ibraheem wacce irin banzar mgn kke min haka? Duk irin yadda nake da karfin iko, da mulki, da izza, cike da KASAITA kkeson na soke Abinda na kafa shekara da shekaru? Me kkeso talakawan gari su kalleni dashi? So kke mutunci na ya zube a idon gaban talakawan gari masu tsami da wari?" "Dakyau...ahh..dakyau.. Mlm Audu" yareema Ibraheem ya furta Hakan Yana tafa hannu cikin tsananin mmkin kalaman  mlm Audu, "Da farko Kai tsaye ka kirani da Ibraheem, daga karshe saika karkare da Talakawa masu tsami da wari Ahh lalle na yadda Duk duniya ba Wanda yakai Dan Adam mantuwa" ya Karasa mgnr Yana hade rai sosai yaci gaba da fadin, "bakaji kunyar fadin Hakan ba? Kai da talakawan kasar Dutse tayi maka Riga da wando?" Zaro ido sarki Audu yyi a tsorace, yareema Ibraheem yace, "kana mmki ne? Akace maka bansan komai a kanka ba? Kaidin Nan fah Dan hijrah ne Wanda yabar garin su a gigice yazo yaci Albarkacin kasar Dutse a lkcn da baka da matsugunni bare Abinda zaka Kai baka su Wannan talakawan masu tsami da wari sune dai suka tallafa maka harka Zama mutum Amma dake Dan Adam butulu ne daka samu dama kaga dama sosai a hannun ka memakon ka tuna Baya ka kyautata musu a'a kawai sai ka Fara nuna musu halin ka na gsky, dama akace idan zaka Gane halin mutum toh ka dube shi lkcn daya samu dama anan zaka tantance hankalin Sa..."

Yadda kasan ruwa ya Masa duka haka sarki Audu yyi tsumu2 gaban yareema Ibraheem sai wurga ido yake irin na munafukai kamar Wanda yyi sata, takun yareema Ibraheem yaji na dosawa gabansa Hakan yasa shi dagowa da sauri jikinsa na Dan rawa, yareema Ibraheem ya Kama qugunsa da duka hannayensa ya danyi tsaki kadan Yana duban sarki Audu da shima yake kallon sa yace, "bana cikin mutanen da suke yiwa manyan su Rashin kunya domin dai a girme ka bani shekaru, da ace ni na girmeka tabbas da nayi maka Abinda Koh kare bazaici ba saidai kash darajar shekaru ya kwace ka banason inayin ja in ja da Wanda nasan ya girmeni Dan haka tun wuri kaje kayi Abinda nace kafin na canja shawara" da sauri sarki Audu yace, "an Gama ranka shi dade ai yanzu ma zansa a tara jama'a" Dan murmushin gefen baki yareema Ibraheem yyi yace, "ka kyautawa kanka" Yana fadar haka ya juya cikin takama da kasaita, daidai zai fice a dakin ya juyo a hankali Yana duban sarki Audu daya ke murza zoben hannun sa a hankali batare da yareema Ibraheem ya kawo komai a ransa ba yace, "Bakaji ba" da sauri sarki Audu ya dago Dan be lura daya ganshi ba Hakan yasa shi boye hannun sa a hankali, yareema Ibraheem ya tabe baki kafin yace, "tun wuri kaje ka samu Wannan yaron naka shu'ayb yyi taka tsantsa da Wannan masarauta domin Yana wuce gona da iri matukar beyi hankali ba zaisha mmkina" sarki Audu yace, "kayi hakuri Insha Allahu zan Masa mgn" yareema Ibraheem ya dage kafadun sa batare daya sake mgn ba kawai yabar wajen a nutse.

Saida sarki Audu ya Tabbatar yareema Ibraheem yyi nisa dashi sosai cikin matukar takaici ya saki Kara me firgitarwa Yana Dukawa kasa Kai kace uwarsa ce ta mutu, sumbatu ya Fara Yi kamar mahaukaci Fadi yake, "karayne Wallahi, Babu mahalukin daya Isa ya taka Ikona a Wannan masarauta matukar Ina raye bazan taba lazumtar Hakan ba" yyi mgnr Yana ture Duk Wani kaya dake gabansa take dakin ya hargitse tamkar Wanda akayi dambe a cikin sa, wata irin mahaukaciyar dariya yaji an kwashe da ita gaba1 sautin dakin ya dauki dariyar sai ji kke hihihihihih....huhuhuhu... kyalkyakyalkyal....puhahahah. a gigice Sarki Audu ya Fara waige2 Yana kallon gabas da yamma kudu da arewa...
******
Hajia Uwani na kwance kunyangi na mata tausa taji an bankado kofar ta, a gigice kuyangin suka Mike kafin a Basu dama tafiya ma suka ringa rige2 barin wajen sbd yadda suka ga yareema shu'ayb ya shigo dakin a haukace, cikin tashin hankali itama ta Mike tana duban Dan nata baki na rawa Tace, "Kai shu'aibu lpy kuwa kke?" Zuciyar yareema shu'ayb na turiri yyi jifa da madubin dake gefen Hajia Uwani sai ji kke tartsartsarrr... ya tarwatse a wajen, kallon sa tayi a razane tana dafa kafadar sa tace, "mgn nake maka Wai meke faruwa ne?" Tsaki me karfin yaja kamar bakinsa zai cire yace, "wancan banzan Mana" da mmki Tace, "wa kenan?" Cikin dacin rai yace, "yareema Ibraheem"

Sauke ajiyar zuciya Hajia Uwani tayi tana riko hannun sa a hankali ta jashi can cikin dakinta bayan ta rufe kofar ta sosai ta dube shi rai bace Tace, "har  sai yaushe zakayi hankali shu'aibu?" Kallon mmki yyi mata yace, "umma kinji Abinda nace tun farko kuwa?" Hajia Uwani Taja tsaki kamar ta mareshi Tace, "har sau nawa zan fada maka gidan sarauta ya banbanta da dukkan sauran gidaje?" Tsaki yyi yace, "ke umma kullum mgnr ki kenan toh mu aje Wannan gefe mu fuskanci Abinda nazo dashi" Hajia Uwani Tace, "dallah rufemin baki a wajen baka gyara tushe ba Taya saman zai ginu?" Yareema shu'ayb yace, "kamar ya kenan?" Hajia Uwani Taja karamin tsaki Tace, "a har kullum Ina tunatar maka da ka iya takun ka a masarauta, kamar yadda nasha fada maka gidan sarauta ya banbanta da sauran gidaje da kke gani domin gidan sarauta ko wanne bango kunne ne, Amma dake baka da hankali tun daga waje ka taho bagazam-gagazam kamar guguwa ba nutsuwa ba kamala kawai ka Fara Sakin Zance kamar fitsarin yaro....
~~~~~
Tunda ya baro bangaren sarki Audu yake Kara duba yanayin masarautar wasu bayi ke biye dashi tun dazu Saida ya Gama yawon sa kafin ya nufi bangaren sa da ummi tasa aka gyara Masa daidai zai Shiga kofarsa yyi alama da hannu alamar bayason a bishi ciki haka kuwa sukayi anan bakin kofa kowa ya tsaya cike da bin umarnin Yareema sarkin goben su Ibraheem Sulemanu., Kallon tsarin bangaren nasa ya dinga Yi cikin sha'awa da birgewa yasan umminsa ce tasa a kawata Masa wajen, Zama yyi bayan ya cire takalmin sa yadan kishingida Akan tuntun dake kasan dakinsa, Lumshe ido yyi Yana bukatar hutawa wayar tarho ya hango gefensa Nan ya tuna da ko waya basuyi da Ahmad ba bayan saukar sa, a hankali ya Mike ya jawo tarho Yana danna numbobin hade da karawa a kunne, Saida ta kusa katsewa yaji zazzaqar muryar ta Tace,

"Assalamu Alaikum."

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now