K' A S A I T A [14]

228 7 0
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_ )



*Hey fans Naga wasu nata korafin Wai meyasa sarki Audu ya mutu da wuri cikin sauki haka?😹 Wasu ma duk sunyi zaton Yareema Ibraheem ne zai mutu, Toh bari kuji gskyr mgn lbrn KASAITA TRUE LIFE STORY ne Dan ya faru a gske shekarun Baya da suka gabata kamar yadda tun farkon labarin nasa 1967 toh tabbas abin ya faru a wancan lkcn saidai nayi canjin sunaye, da canjin Gari wato masarauta sannan na Kara nawa labarin a ciki, Kuma a gske sarki Audu yyi mulkin zalunci Dan Abubuwan Dana rubuta tofah yyi a gske Wani abin ma ban rubuta ba irin mulkin da yyi ya taka Wanda na rubuta a pages din Baya koda yake na yanke wasu wuraren ne sbd Naga kamar akwai Wanda har yanzu basu fahimci Inda labarin ya dosa ba Suna ganin anasa labarin YAREEMA NASEER Amma idan an Shiga ciki sai aga yareema Ibraheem shiyasa kawai nayi sauri Dan mu tsunduma cikin labarin YAREEMA NASEER, sannan kuma a gsken sarki Audu ya sanar da yaransa Babu me hawa mulki sai me kujerar, Yareema Ibraheem Baya mutuwa sarki Audu ke mutuwa, Ina fatan kowa ya fahimta sannan za'a gyara Zama domin jin LABARIN YAREEMA NASEER wasa farin girki💃🏻*



By
*Nuceeyluv😘*

*Wattpad* #nuceeyluv


14.....



~~~~Fitowar sa daga wanka kenan farin towel daure a qugun sa yyinda yake rike da Wani karamin Yana gyara sumar kanshi Wayarsa ce ta sake yin ringing a karo na Babu adadi yaja dogon tsaki batare daya nufi Inda wayar tasa take ba ya zauna gaban mirror dinsa Dan shiryawa, *PRINCE NASEER IBRAHEEM* kenan matashin saurayi Dan shekara talatin cikakken namiji meji da mulki cike da izzar KASAITA Wanda 'yan mata dayawa ke rububun sa yana ja masu aji tamkar Wani mace Kai hatta mazan ma akwai masu son Zama frnds dinsa saidai Babu halin Hakan Dan Prince Nas bada kowa yake mgn ba, Mutum ne me shegen ji da kai bare abin ya hade da tsantsar kyau da kyawun halitta da Allah ya bashi tamkar shi yyi kansa Dan kyau kowa ya ganshi yaga jinin sarauta, shafa cream yake a nutse Harya Gama ya Fara gyara sumar kanshi da take luwai-luwai tamkar ta larabawa daga nan ya debo turare ya Fara feshe jikinsa dasu, kayansa dake bisa gado ya dauko ya saka Yana Shirin sake fesa turare phone dinsa ta sake ringing,

Yatsina fuska yyi kafin ya dauko iphone dinsa ya Kara a kunne batare da yyi koda tari ba, daga dayan bangaren ansan bazaiyi mgnr ba Dan haka cikin zumudi Tace, "Mrng Yah Naseer pls ka amsamin tmby ta yaushe zaka koma Nigeria?" Tayi mgnr cikin sauri2 Dan bataso Dan lkcn da tayi sa'a ya Bata ya kashe wayar Bata gabatar da Abinda ya kawota ba, kusan few seconds cikin amon muryar sa me shegen Dadi da kwantar da zuciyar 'yan mata yace, "I don't know" Yana Gama mgnr ya kashe Yana Jan karamin tsaki,

Daga dayan bangaren dafe goshin ta *Mansoora* tayi kamar tayi kuka kawarta yasira Tace, "har yanzu be fada miki ba?" Mansoora Taja karamin tsaki Tace, "I don't why Yah Naseer yake min haka" tayi mgnr tamkar tayi kuka, yasira Tace, "toh ki Kira Mami kiji ko tasan da dawowar sa" girgiza Kai mansoora tayi Tace, "idan da ace ya sanar da komawar sa Nigeria da tuni Mami ta kirani Dan kowa saiya shaida zuwan sa" yasira Tace, "toh yanzu haka zamuci gaba da Zama a chaina har lkcn da Namijin kasaitar zai koma?" Mansoora Tace, "pls ki Kara hakuri yasira nasan a Wannan lokutan Yah Naseer yake komawa Nigeria toh nafi so nasan ranar komawar sa muma sai mudai hanya banaso na koma gida yah Naseer baya Nan Dan na qagu ya fahimci soyayyar da nake Yi Masa" yasira Tace, "iska na wahalar da me kayan Kara Dan ni ko a fuska ban taba ganin alamar son ki wajen Yah Naseer ba" Mansoora tayi murmushi Tace, "ke ko baya Sona haka nake fata ayi auren" "Aure?" Yasira ta furta da mmki, kallonta Mansoora tayi sai Kuma ta tashi da sauri tana fatan kada ta Tona asalin Abinda suka shirya ita da mamin ta.

Aje Wayarsa yyi ya koma gaban mirror dinsa yana gyara tie dinsa bayan ya gama ya dauki turaren kaya masu Kamshin gaske Wanda ba kowa ke iya siyan irinsu ba sai Dan wane da wane ya dinga fesawa kamar zai karar da kwalaben, Yana gamawa ya dauki sauran phones dinsa ya fito waje cikin takun sa na KASAITA, Yana bude kofa Wani dogari na jikinta Yana jiransa, kallon sa yyi batare da yace uffan ba yyi gaba ko ba'ace komai ba ya fahimci Abinda yake nufi Dan Zama da Yareema NASEER yasa kowa ya Fara fahimtar maganganun sa na kurmanci, dakinsa ya shige ya jawo trolley dinsa daya barta ciki da sauran Abubuwan amfanin sa daya bari ya kammala Masa shi ya kwaso yayo waje, kusan su biyar ne dogarawan da suke tare dashi a London, can ya koma yyi karatun sa na Engineering  secondary kawai yyi a Nigeria ya tsallake ya koma London, acan suka hadu da Wani Dan Nigeria Fahad Wanda ya Zama frnd dinsa ko ace best frnd dinsa domin shima Dan jigawa ne shikuma babansa ne Dan kasuwa masu kudin gske wato dai kwarya tabi kwarya, Dan shima yanaji da kansa saidai Duk jin kansa bazai taba kamo jinin sarauta ba, a parlo ya tarar da Fahad din yana jiran fitowar sa, Fahad na ganinsa ya Mike da sauri yace,

"Haba prince Wannan ai wulakanci ne sai faman jiranka nake ka shanya ni" Wani irin side look yareema NASEER yyi Masa kafin yyi gaba Abinsa, tsaki Fahad Yaja yana girgiza Kai yabi bayansa da sauri, tun kafin ya isa gabar motar daya nufa aka bude masa gidan Baya cikin girmamawa, Shiga yyi shima Fahad ya shige ta dayan side din Nan aka rufe kofar sauran dogarawan suka Shiga wata motar direct Airport suka nufa.

Suna zuwa suka shige cikin jirgi Inda aka tanadar domin irinsu, zaman sa keda wuya ya zaro Wayarsa da nufin sata a flight mood yaga message ya shigo, daga saman screen din ya karanta layin farko _Mr handsome I LOVE YOU it's me...._ be Ida karanta sakon ba yadan ja tsaki yasan cikin 'yan matan dake rububun sa ne wata ta turo kashe wayar yyi gaba1 Yana aje ta gefe ya dauko dayar wayar sa itama zai sa flight mood Fahad yace, "tun dazu sai Jan tsaki kke kamar tsaka Wai ka sanar da gida komawar taka ne?" Kallon sa yyi a nutse karon farko yace, "No" Fahad yace, "but why?" Yareema NASEER yace, "Ganin dama" tabe baki Fahad yyi Yana daga kafada ya zaro waya yace, "bazan iya biye maka ba let me call my Ammi tasan da zuwana" tabe bakin shima Prince Nas yyi Yana bude laptop dinsa yace, "kanka akeji" murmushi Fahad yyi shima ya maida Wayarsa flight mood beyi Kiran ba Dan yasan dalilin dayasa yareema bayason asan da zuwan sa, jirginsu ne ya Fara shawagi harya wulwula dasu sararin samaniya, Fahad ya juyo Yana duban Yareema NASEER da murmushi daidai lkcn Prince Nas ya dago Yana duban sa yace, "Yadai?"

Fahad yace, "kawai Ina tuna Mansoora ne gaba1 taki komawa gida tun last two months da sukayi hutu Dan kawai ta jiraka ku sauka Nigeria tare" tabe baki Prince Nas yyi yace, "Bata da aiki."


*Idan Naga yawan comments dinku lalle zan dinga typing Medan yawa haka zalika zan dinga posting akai-akai*

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now