K' A S A I T A [4]

421 14 0
                                    

*K' A S A I T A*
( _LABARIN YAREEMA NASEER_)


By
*Nuceeyluv😘*

4....

Tsam Uwani tayi da ranta tanason yin mgn tana Shakkar sa Dan haka tayi murmushi a nutse Tace, "toh ai banga abin bacin rai anan ba memartaba duba da yadda yaron Nan goben Nan zai bar kasar ma gaba1 kaga kuwa sai yadda kayi da mulkin zaka iya cin Karen ka Babu babbaka batare da'an sa maka ido ba"
sai a lkcn Memartaba Audu yyi kayataccen murmushi yace, "bazaki gane bane tun zaman farko Dana yiwa kurjerar Nan ta mulki na fahimci zaqi da gardin dake tattare da ita kinga kuwa ko waye dole ya qagauta yabar qasar" Uwani Tace, "Wannan gsky ne."

Acan bangaren yareema Ibraheem kuwa kwana sukayi shi da mahaifiyar sa Suna ganawa da juna sbd hirar ban kwana da sukeyi yasa ko kadan Basu san lkci yaja ba har aka Kira asubahin farko, Nan fa zakaru suka Fara cara alamar Alfijir ya keto, Tashi sukayi shi da ummi bayan sunyi Alwala suka jera tare Dan gabatar da sallar nafila kafin a Shiga masalllaci, Saida suka dade Suna Addu'a kafin Nan bcci yace salamu alaikum Nan suka Mike domin rama bccin jiya dake sai wajajen Hantsi ya Kama kamar goma na safe kenan yareema zasuyi tafiyar zuwa kano.

Dukkan ilahirin mutanen masarautar ne suka taru gaban motar katako da zata dauki yareeman Masarauta dayawa wasu Alhini suke da Wannan tafiya tasa sbd ganin kankantar sa za'a rabashi da mahaifar sa a kaishi can kasar Nasara masu Jan kunnuwa, mahaifiyar sa ba karamin daurewa tayi ba Dan karfafa Masa gwiwar tafiyar tasa, sarki Audu ne ya matso fuskar sa cike da damuwa kamar gske ya Kama hannun yareema Ibraheem yace,

"zuciyata rawa take yareema badan neman ilimi yanada kyau ba da kuwa tabbas bamu barka kayi nesa damu ba domin iya Dan zaman da mukayi dakai na fahimci kyawawan halayen ka yareema" Dan guntun murmushi yareema yyi yace, "Kamar yadda zan tafi na barku lpy Insha Allahu haka zan dawo na ganku lpy cike da samun canji kala2 daga Wannan mulkin naka" Sarki Audu yace, "indai canji ne da yaddar ubangiji zaka gani Allah dai ya nufe mu Alkhairi" Nan kowa ya Amsa da Ameen.

Sun dade tsaye gaban motar katako har lkci yaso ya gota yareema ya saki mahaifiyar sa ummi hade da fashewa da kuka ya shige motar Dan ya kasa rike Wannan kukan dayake ta mazewa, kamar kuwa an kunna famfo haka hawaye keta kwarara a kumatun sa mama fulani na ganin haka ta juya cikin gidan da sauri kuyangi na take mata baya Nan motar su yareema ta tashi, tana Shiga bangaren ta dab da zata Shiga daki ta daga hannun ta alamar tana bukatar kebewa Nan kuma aka barta ita daya tana Shiga kuwa ta fashe da Wani irin kuka me tsuma zuciyar mai sauraro.

Tafiya irin ta motar katako akwai jimawa duba da yadda yanayin motar take sai a hankali Amma a wancan lkcn motace ta Alfarma Wanda Babu me hawanta sai wane da wane, Sun Isa kano lpy cikin Amincin suka karasa can filin jirgi anan kuwa suka tarar da yaran sarakuna dayawa an kawo su lkci kawai ake jira jirgi ya tashi, bayan shudewar lokuta aka hada kan daliban su 20 cif zasuyi tafiyar daya bayan daya suka dinga Hawa jirgin har aka Gama shigar dasu kafin masu kula da dalibai suka hau daga baya daga Nan kuwa jirgi ya Fara shatale-tale can ya shilla dasu sararin samaniya.
****
Bayan wata uku da tafiyar yareema canji ya Fara wanzuwa a fadar memartaba sarki Abdulhakim, Ba kamar Wannan ranar ba data kasance yau ranar juma'a Ana zaman fadanci bayan dawowa daga sallar juma'a bayan gaishe2 da aka saba na fada can fadar tayi shiru kowa na jiran Abinda sarki zaice Dan tun jiya aka sanar da Sank'ira yyi yekuwa ga mutanen gari Akan sarki na neman Talakawan gari da bayi a taru a fada sbd yanada muhimman zantukan dayakeson isarwa ga Al'umar sa, kowa da yaji batun Kiran sarki sai hantar cikinsa ta kada Dan izuwa yanzu tsananin Tsoron sa da Shakkar sa ta gama Kama dukkan ilahirin zuciyar su shiyasa Ana sakkowa masalllaci mutanen gari aka Fara wucewa fada Dan gudun lefi, taro yyi taro har baka iya kwakkwaran motsi sbd cika, Amma jiran mgnr sarki yasa kowa yyi gum tamkar Babu mahaluki a wajen,

memartaba sarki Abdulhakim Yana kan kujerar sarautar sa yasha Nadi ba'a ganin komai daga jikinsa hatta idonsa Saida aka kusan rufeshi da nadi, gyaran murya yyi kafin ya dubi bafaden sa kallo na tuni da kuma son a sanar da jama'a Abinda ya tara su, bafaden sarki yyi gyaran murya shima cikin daga murya yace,

"Assalamu Alaikum Jama'a, sarki na gaishe ku kuma dukkanin ku ya amshi gaisuwar juma'ar da kukai, toh Madallah bayan haka kuma jama'a kamar yadda kukaji sanarwa lalle memartaba sarki Abdulhakim Gana yanada muhimman zantukan dayakeson isarwa gareku, Yana kuma Kara Jan kunne ga Jama'ar sa da kowa ya bude kunne sosai domin yaji ya kuma fahimci Abinda akace sbd gudun matsala" Nan ya juya ya sake kallon sarki Audu can kuma ya juyo har lkcn Jama'ar wajen na sauraron mai mgn da yawun bakin sarki, Nan kuwa yaci gaba da fadin,

"ba komai bane face wasu sharruda da sarki yakeson gindayawa a Wannan gari nasa, sharrudan kuwa shine Duk Wani mahalukin dazai wuce ta Gefen masarautar Nan wato gaban masarauta ko bayanta zai cire takalmin sa ko shi waye, nisan zango kuwa ya Kama daga can hanyin madaci zuwa karshen masarauta   (a lissafin yanzu zai Kama 2klm kenan) kowa yasan nisan zangon daga hayin madaci zuwa karshen ginin masarauta, toh kuji dakyau Wannan doka an dorata ne Akan kowa wato dai Babu babba Babu yaro ba tsoho ba tsohuwa ba bako ba bakuwa Dan haka gwarama tun farko ku sanar da Wanda be sani ba ku sanar da bakin da Basu sani ba domin Duk Wanda ya taka doka doka zatayi aiki a kansa Duk shekarun ka kuwa Koh kankantar ka Hakan bazai sa a hukunta ka bisa Karya Wannan doka data Samo asali daga umarnin Mai martaba sarki Audu, Dan haka Ina Kira gareku yaku taron Talakawa daku bi umarnin sabon Sarki sau da kafa Koh kuwa mutum ya fuskanci mummunan hukunci a kansa.

K' A S A I T A (LABARIN YAREEMA NASEER)Where stories live. Discover now