Chapter 15

323 53 18
                                    

Paris

Heyyo........

Da kyar ta zauna a gefen couch kamar wata marar gaskiya take hararar Iqbaal inda zuciyarta ke bugawa lokaci zuwa lokaci,ba tare da bata lokaci ba doctor ya fara aikinsa yaci gaba da yi mata duk wasu gwaje-gwaje da suka dace tare da yi mata tambayoyi kafin ya fara aikin nasa,bayan ya gama duk wasu gwaje-gwaje ya mikawa maimooon result dinta sannan yayi sallama da Iqbaal ya fita cike da ladabi

Gabanta ke cigaba da faduwa cikin tashin hankali ta rike takardar a hannunta ba tare da tasan makomarta ba,ya salam yanzu idan na bude paper dinnan naga inada ciki taya zan kare kaina daga cin mutuncin Iqbaal?kalar wannan tunanin maimoon taci gaba dayi ba tare da ta kula ba Iqbaal ya karbi takardar daga hannunta,cikin sauri ta mike ta fara kokawar amsar takardar daga hannunsa sai dai tuni Iqbaal ya rike paper din sosai a hannunsa fuskarsa hade yace kinaso ki jiwa kanki ciwone?

Turo baki tayi cikin tsoro da tashin hankali tace who cares?ba abinda ya dameka dani ka bani result dina lafiyar jikina ba abinda ya shafeka bane

Murmushi yayi yace i know,cike da gadara ya fara bude takardar ya karanta abinda ke rubuce jiki sannan ya mika mata ba tare da yace mata komai ba ya fita daga room din,gabanta ne yaci gaba da tsananin faduwa jikinta sam babu karfi ta bude takardar ganin typhoid ne kadai abinda ke damunta ya sanya maimoon yin godiya ga Allah tace Alhamdulillah cike da farin ciki maimoon taci gaba da ayyukanta don yanzu ji take kamar an sauke mata duk wani ciwo na jikinta ashe damuwa da tunani ma kadai suna sanya mutum yaji bashi da lafiya

Karfe 7 iqbaal ya turo kofar dakin,kallo daya tayi masa ta fuskanci baya cikin hayyacinsa saboda zallar buguwar da yayi,juyar da kanya tayi gefe taci gaba da danna wayarta saboda tana matukar enjoying duba page din arewa twitter savages a Twitter suna matukar sanyata dariya,ledar hannunsa ya cilla mata cike da buguwa yake magana

Yo what's up dove?here is your medication ya fada yana sake matsawa inda take zaune akan gadon

Da sauri moon ta tureshi cikin fushi tace iqbaal what are you doing?

Kamar tana zigashi haka ya dinga matsawa kusa da ita yana ambaton sunan dove cikin tashin hankali moon ke ture iqbaal daga jikinta....stop it iqbaal you are drunk ni ba dove bace stop it please

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,shine abinda moon ta dinga ambato bayan farkawarta daga nannauyan bacci,ganinta tayi kwance a jikin iqbaal cikin tashin hankali ta tureshi daga jikinta da kyar ta shiga bathroom tayi wanka banda hawaye babu abinda yake zuba a idon moon,cikin takaici ta dawo palour ta zauna hawayen bakin ciki yana zuba daga idonta

Sai da ya kara 2 hours kafin ya tashi daga hadadden baccin da yake bayan yayi wanka ya fito sanye cikin sky blue shirt da black trouser wanda suka yi matukar dacewa da jikinsa,direct wajen dispenser ya nufa ya hada coffee tare da zuba cookies a plate ya dawo ya zauna a couch da ke kallon inda maimoon take zaune ba tare da wata damuwa a fuskarsa ba ya gama shanye coffee din sannan ya mike har ya juya zai fita ya kalleta yace dafatan kinsha maganinki?

Ko kallonsa bata yiba balle ya fahimci ma tana sauraron abinda yake cewa,sake murmushi yayi yace ohh don't mind idan kinga dama kar kisha ma saboda bani da alaka da wata lafiyar jikinki i am just advising you ba order nake baki ba

A fusace moon ta saukewa iqbaal kyakyawan slap a fuskarsa cikin kuka ta rike rigarsa tace wai kai wanne irin mugun mutum ne?anya kana da zuciya a jikinka kuwa?anya kana neman rahmar ubangiji kuwa iqbaal?meyasa zaka cuceni ka bata min rayuwa?meyasa zaka yimin abinda bana fatan inyishi da mutumin da baya sona kuma baya kaunata wanda baya kunyar fadan haka a duk inda ya tsinci kansa....iqbaal wlh bana sonka bana kaunarka ban sake jin tsanarka ba sai yau saboda kai mugune azzalimi......

Bai jira ta karasa maganaba ya daga hannunsa zai sauke mata mari sedai kafin hannunsa ya kai face dinta yayi saurin janyewa da kansa,yace god save you bansaniba ko kina dauke da cikina yanzu haka a jikinki shine dalilin da yasa kadai bazan mareki ba....and what are you fucking thinking?kina tunanin wai don ina sonki nayi making love dake?kinfi kowa sanin cewar i don't have any feelings on you nayi haka ne kawai saboda i'm drunk and you know it,so meyasa kike damun kanki kike tunanin wani abu daban da wannan karamar kwakwalwar taki wacce bata san komai ba sai shirme da shashanci....shiru yayi kadan wanda zaka gane cewar ran iqbaal a matukar bace yake sosai idonsa yayi ja sannan ya kalleta yace hey miss 9ja don't you ever try this shit with me again sannan meyasa kike wani damuwa?shin kina tsoron kada ki samu ciki da mutumin da baya sonkine?murmushi yayi kadan yace don't worry ke kadaice banaso amma ina son baby na....be jira ta sake magana ba ya dauka phone dinsa ya fita daga room din a fusace

Bin bayansa tayi da kallo sannan ta fashe da kuka cikin fushi tace iqbaal you will never change akwai aiki babba a gabanka,bazan fasa yi maka addua'r shiriya ba,moon ta dade tana kuka kafin lokacin sallar azahar yayi ta mike ta daura alwala ta gabatar da sallah tare da addu'oi...wayanta ne ya fara kara da kyar ta mike ta dauki wayar ganin number maryam ya sanyata yin murmushi kadan atleast someone cares for her,daga wayan tayi cikin fushi tace hey monkey

Hey miss world maryam ta karasa magana cikin tsokana

Tsaki moon tayi tace you see your life zaki fara ko

Ahhh sorry ina nufin miss Eiffel Tower,kinsan Allah moon da nice a paris da yanzu na cika wayata da pictures don kullum sai naje eiffel tower nayi pictures da TikTok videos but you know what?moon wannan pictures din da kikayi kinga yanda sukayi kyau kuwa don ko jiya dana sanya su a instagram story dina morethan 800 people's suka dinga commenting and you know what?

Ya rabb maryam you are very talkative wai shin har yanzu kina nan kina surutun nan naki ba,mutum yana so ya fada miki magana kinqi ki bashi dama sai zancen slaying da blogging kike min haba this person will never change i swear moon ta karasa magana kamar zatayi kuka

Oh no!our dearest moon kar kiga lefina i am just missing you kuma kinga na hada miki pending stories shiyasa yanzu nake baki karki manta amma yanzu ina jinki fadamin what's up ina labarin honeymoon i hope you are enjoying the cool breeze of everyone dream city

Shiru moon tayi kadan bakinta ya kasa cewa komai yanzu ne taga rashin dacewar bawa maryam labarin abinda ya faru tsakaninta da iqbaal ko babu komai akwai sirri tsakaninsu,cike da dabara tayi gyaran murya tace tsokanarki kawai nakeyi we are all fine maryam sedai ina missing nigeria inason dawo wa very soon wlhi sedai har yanzu naga iqbaal bashi da niyar barin paris

Ahh gaskiya moon baki haduba ke yanzu har tunanin barin paris kikeyi?nifa wlhi da kamal zeji shawarata da idan mukayi aure london zamu koma da zama ko paris don inaso na huta sosai amma ke duka duka baki wuce 3 weeks ba amma kina fadin kin gaji da paris ....sun dade suna waya morethan 2 hours kafin suyi sallama wanda hakan yayi daidai da lokacin sallar la'asar moon tayi sallah sannan ta nufi inda kitchenette yake tayi warming abinci taci

Yau 13 days kenan tun bayan abinda ya faru tsakanin moon da iqbaal bata sake sanyashi a idonta ba,bata yi mamakin haka ba saboda tasan dama ya saba dadewa be nemetaba sam sam bata damuba,yau kam tunda moon ta tashi cikinta ke mata tsananin ciwo tare da jin jiri don ko mikewa tsaye bata iyayi a kwance ta wuni,ganin tana shirin halaka kanta yasa ta laluben number din iqbaal da kyar ta fara kiransa sedai har 8 missed calls amma bai daga wayar tata ba

Da kyar ya mike daga baccin da yake yi tare da zame dove daga jikinsa ya shiga wanka,bayan ya fitone ya shirya sannan ya dauki wayarsa cikin mamaki yake bin missed calls din moon don tunda take bata taba kiransa a wayaba balle har tayi masa wannan uban missed calls haka,dialing number din yayi ya kirata amma shima yayi mata 3 missed calls batayi picking ba,key din motansa ya dauka ya nufi hotel din nasu

Bai jira yayi knocking door dinba yasa key ya bude kofar sedai cikin mamaki yake bin maimoon da kallo kwance kamar gawa bakinta duk jini da alama aman jini tayi,wannan shine karo na farko da iqbaal yayi saurin zubewa a kasa cikin tashin hankali yace miss 9ja karki mutu please wake up...

Vote
Share
Comment
Ramadan kareem 🌙
May Allah accept our ibadah amin

IqbaalWhere stories live. Discover now