Chapter 6

848 90 7
                                    

"Gumi ne mai zafin gaske yaci gaba da zubowa a fuskar maimoon cike da nazari take cigaba da kallon takardar inda gefe daya zuciyarta ke mata zafi cike da takaicin marin da iqbaal yayi mata

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

"Gumi ne mai zafin gaske yaci gaba da zubowa a fuskar maimoon cike da nazari take cigaba da kallon takardar inda gefe daya zuciyarta ke mata zafi cike da takaicin marin da iqbaal yayi mata

Excuse me,shine abinda ya sanya maimoon dagowa a firgice ta kalli wanda yake mata magana kamal ne tsaye jikinsa sanyaye yake kallon maimoon,shiru tayi ba tare da tace masa komaiba sai kallonsa da taci gaba dayi cike da tunanin meya kawoshi,ruwan da yake hannunsa ya mika mata wanda take da tabbacin yana da sanyi idan har tasha ko kadanne ze sanyaya mata zuciya

Girgiza kanta tayi cike da rashin son yin magana tace thank you

Sake mika mata cup din hannunsa yayi yace kiyi hakuri ki karba kisha ko kadanne naga ranki a bace yake kuma kyakkyawan mace kamarki bai kamata ace tana fushiba

Lumshe idonta tayi tace karka damu wannan ba bakon abu bane a wajen maimoon kawai ka tafi abinka

Shiru ya sake yi yace please ya marairaice kamar zeyi kuka

Ganin kamal na shirin takura mata ya sanyata karbar ruwan tasha kadan sannan ta nufi office din iqbaal cike da bacin rai da takaici ta tura kanta ta shiga ba tare da sallamaba sannan ta sake rufe kofar ta tsaya a cabin din fuskarta babu alamar tsoro sedai zafin da zuciyarta keyi mata

Ganin inuwar mutum a kansa ya sanyashi dagowa cike da tuhuma yake kallon maimoon da alama shima har yanzu ransa a bace yake,kallonta yayi a wulakance yace what?

Gyara tsayuwarta tayi tace nothing,nazone na tuna maka cewar dan adam abune mai matukar daraja da kima Sannan Allah baya farin ciki da mutumin da yake tozarta dan uwansa,menene ribarka don kayimin sharri don kawai ka tozartani a gaban mutane dayawa?ko ba komai ya kamata kasan cewa ni macece mai matukar rauni a zuciya kuma menene ribata idan nayi maka rubutu jikin kaya saboda tozarci,ka zageni ka mareni duk gaban mutane.......saurin daga mata hannu yayi hakan ya sanyata kasa cigaba da magana

Will you shut up! Idan kina tsoron abinda nayi miki meyasa zaki min rubutu ki sanya jikin kayana?saboda kawai kinaso duniya tayi min kallon wani shashasha bana bukatar jin wani zancen banza sannan ina sake warning dinki karki kuskura ki sakeyimin irin wannan kalar shashancin...i will never ever love you

Murmushi maimoon tayi tace me too baka yimin ba ko kadan ko alama balle har na sanyaka a raina saboda tsarin rayuwarka kadai abin gudune ga kowacce mace idan har tasan ciwon kanta da rayuwarta toh tabbas bazata taba yin shaawar hada zuri'ah da kaiba balle har ka zama uban yaranta

Mikewa yayi tsaye bayan ya dauki rigarsa da wayarsa ya kalleta yace cool smart girl zan gwada kadan daga cikin habits dina wanda baki sansuba sannan yayi murmushi ya ajiye mata breif case a gabanta ya fita

Turo baki tayi a zuciyarta tace Allah wadaran naka ya lalace sannan ta dauki breifcase din ta bishi,kamal ne yasha gaban iqbaal yace Mr london nifa gaskiya na kamu wannan kanwar taka nakeso

IqbaalWhere stories live. Discover now