Chapter 7

782 103 7
                                    

Suprise chapter 👌🏻

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Suprise chapter 👌🏻

Karar wayarta ne ya sanya maimoon ajiye samosa din da takeci ta dauko tissue ta goge hannunta ganin sunan maryam ya sanyata murmushi tace heyyy idiot!naji dadin ganin kiranki maryam ina kika shigene?

An gaisheda female bodyguard,a girl with tons of confidence maryam ta karasa magana tana dariya

Goddess you are so boring maryam,kinsan Allah daga yau na dena yiwa iqbaal komai gaba daya bashi da hankali i dont know how to explain his madness he is the worst person that i ever meet,kar kiso kiga yanda jiya yayi min a office saboda kawai an rubuta masa sunana jikin rigar sa ya mareni gaban mutane kar kiso kiga irin zaginda yake min maryam i have already hate him

Murmushi maryam tayi tace nasani Maimoon iqbaal yana da matukar zafi amma karki manta da alkawarin da kika daukarwa kanki saboda farantawa mahaifin iqbaal akan abinda yayi.....sorry maryam ana knocking door anjima zan kiraki tana fadan haka ta kashe waya ta juya don sake jin karar knocking din yayi yawa

Da sauri ta sanya hijab dinta cikin muryarta mai sanyin gaske tace waye?

Shiru babu wanda ya amsa mata sai cigaba da buga kofar akeyi kamar za'a ballashi,gabantane ya fadi tayi saurin sanya hannu ta murda kofan ta budeshi,zaro kyawawan idonta tayi ganin iqbaal tsaye fuskarsa yayi ja saboda tsananin bacin rai

Meyasa kike tambayar waye yake knocking bayan kinsan nan ba gidanku bane?ko kin manta masu gidan zasu iya shiga duk inda sukeso kuma a lokacin da suka ga dama?ya karasa magana yana zama a kujerar dake gefen dakin

Murmushi tayi tace hakane nan ba gidanmu bane gidanku ne kuma kana da damar da zaka shiga ko ina sedai baka da damar da zaka cimin mutunci ko cin fuska saboda nayi resigning din yarjejeniyar da nayi ta yi maka aiki,saboda haka baka da ikon da zaka tsaya gabana kana fadamin maganar banza saboda yanzu bani da wata alaka tsakanina dakai kuma zan bar cikin gidannan gobe insha Allah maimoon ta karasa magana cike da rainin hankali tana kallonsa a wulakance

Shima murmushin yayi yace hakane dole kiyi resigning saboda kin samu cikar burinki right?abinda ya kawoki gidan kin samu dole kuma ki barshi wai ma in tambayeki shin munin fuskarki ne yayi miki yawa har kika kasa samun wani namiji da yake da interest akanki har kika zabi ki aureni saboda talauci ya isheki da iyayenki wanda suka kasa rikeki har sai kinzo gidan mutane kin zauna?toh ina tabbatar miki cewar idan har baki janye muradinki na aurenaba wallahi tallahi i promise to make your life worst and i will try my best to make your life hotter than hell

Cikin mamaki maimoon ke kallon iqbaal wanda ta kasa gane inda zancensa ya dosa,shin har yanzu yana yin magana ne akan abinda ya faru a office jiya har yake tunanin tayi hakane saboda ta aureshi ko kuma wani abune daban?bata karasa tunaniba taji karar rufe kofar iqbaal da karfin gaske,itama tsaki tayi tace koma dai me zakayi sedai kayi amma aiko ne na dena,cigaba da cin samosa tayi duk da zuciyarta sam babu dadi,karar wani knocking din taji cike da damuwa tace ya rabb who's this again?

IqbaalWhere stories live. Discover now