Chapter 8

785 95 2
                                    

Dariya Aunty falila tayi tace oh kaga love birds yanzu dai da gaske bazaki nuna min angon ba?toh shikenan rike abinki nasan dai tunda kina gidan nan yanzu zai fara zarya a gidannan kinga sena ganshi arha free of charges ta karasa magana tana mikew...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Dariya Aunty falila tayi tace oh kaga love birds yanzu dai da gaske bazaki nuna min angon ba?toh shikenan rike abinki nasan dai tunda kina gidan nan yanzu zai fara zarya a gidannan kinga sena ganshi arha free of charges ta karasa magana tana mikewa tsaye ta nufi hanyar kitchen

Babban tray ta dawo dashi a hannunta ta ajiye gaban maimoon tace ga abinci nan kinsan ba'a son mata musamman amare suna zama da yunwa saboda rashin energy a jikinsu yana kawo musu karancin ni'ima don haka yanzu kici abinci tukunna sai in nuna miki dakinki kije ki huta,shiru maimoon tayi bayan tayi Murmushi sai a lokacin ta tuna rabonta da abinci tun jiya da daddare sai coffee din da tasha da safe

Hannu tasa ta bude food flask din hadadden kamshin farfesun kazan ya shiga hancinta wanda yasha kayan kamshi musamman kanamfari yana taimakawa sosai wajen dawowa mutum darajar jikinsa da martabarsa both males and females,dayan flask din ta bude shi kuma white rice ne da vegetables sai macaroni salad da fresh strawberry juice,duk da maimoon ba wani farin ciki takeyi da cin abincinba amma yayi matukar birgeta abincin,a plate ta zuba ta fara cin abincin ita kanta tayi mamakin yanda abincin yake tafiya sosai don taci dayawa kafin a nuna mata dakinta

A hankali ya cire takalmansa ya tsuguna gaban dad haka nan kawai yaji yana matukar tausayin mahaifin nasa wanda babu abinda be mallaka a duniya ba,kudi,nasarori da sauran abubuwan da duk wani dan adam yake burin mallaka Allah ya riga ya mallakawa Alhaji sayeed sedai yau kimanin shekara 6 kenan bayan rashin lafiya da yayi yake amfani da wheel chair baya iya mikewa balle yayi aiki da kafafuwansa,shiru iqbaal yayi a hankali ya dauke idonsa daga kallon dad cike da tausayinsa ya tsuguna yace gani duk da fushin da yake yi dashi

Kallon iqbaal dad yayi yace okay inaso kaje ka dauki maimoon ka kaita gurin tailor dazu mom dinka ta kirani tace na fada maka cewar ka kaita "Heroine Beauty palace"tayi magana dasu akan dinkunan da zaa yiwa maimoon a wajen,wani irin takaici iqbaal yaji to wai banda auren dolen da zaa yi masa har sai an sanyashi ya dinga yiwa yarinya bauta kamar wata sa'arsa?kallon dad yayi da jajayen idonsa yace dad this is unfair fa gaskiya ina ganin kawai a tura mata kudi tayi duk abinda taga dama amma a dena takura min haka

"I am not begging you iqbaal i am ordering you" dad ya fada a takaice,shiru iqbaal yayi yace okay sannan ya mike jikinsa babu wani kwari

Iqbaal,dad ya kira sunansa a hankali

Saurin juyowa yayi yace yes dad

Nan da 2 hours nakeso ka dauketa ka kaita saboda suna jiranku ne,aikin is too late dole sai anyi komai cikin hanzari dad ya fada yana kallon iqbaal

Shiru iqbaal yayi yace okay sannan ya fita still jikinsa babu wani karfi

Oh god!tunda naji wannan ringing din yayi yawa nasan kece maryam bazan dauki wayarki ba har sena fito daga wanka maimoon ta fada tana karasa daura towel din jikinta sannan ta fito daga bathroom din,wani karar wayar taji cikin sauri ta karasa ta dauko wayar se dai ganin sunan "Mr london"ya sanya hannunta fara yin rawa kamar ze cire saboda tsananin tsoro,cigaba tayi da kallon sunan ganin wayar na shirin katsewa ya sanyata saurin dauka ta sanya a kunnenta cike da fargaba

IqbaalWhere stories live. Discover now