Chapter 21

386 49 26
                                    

"Wani irin gumi ne ya sauko mata ba tare da tasan dalilin yin hakan ba,da kyar ta daga lips dinta wanda yayi mata nauyi tace maryam i didn't get you.....cikin damuwa maryam tace kinga just expect me nan da 2 hours i will be right there naga har yanzu baki fahimci me nakeson fada miki ba stupid brat,okay kawai moon ta fada sannan tayi ending call din,gani takeyi kamar 2 hours ze iya zame mata 2 years saboda tsabar kaguwa da tayi ta samu labarin abinda yake faruwa

"Cikin damuwa ta mike daga inda take zaune ta nufi kitchen se dai for sure babu abinda zata sake iya aikatawa idan har bata ji cikakkiyar magana daga gurin maryam ba,fitowa tayi daga kitchen ta dawo palour ta zauna cikin sanyin jiki ta dauki wayarta ta kira Exquisite cakes and more tayi order din fried rice,macaroni salad,avocado salad da cowleg kafin ta koma daki ta zauna jikinta matukar sanyaye tana zaman jiran karasowar maryam,bata yi wani taking time ba ta turo kofar dakin ta shigo cikin tsoro moon ta daga kanta ta kalli wajen kofar sannan ta sauke ajiyar zuciya tace har kin bani tsoro

"Tsaki maryam tayi tace ke nima a tsoracen nake ai

"Fito da waya maryam tayi daga jakarta sannan ta shiga page din #9jaclassicwedding ta mikawa moon wayar tace kalli da idonki that's what i saw dazun nan sukayi posting picture din sannan ki kalli yanda mutane ke commenting akan hoton suna cewa perfect match,hannunta na rawa ta karbi wayar idonta ya sauka akan hoton Iqbaal tare da zeezah wanda ita kanta tasan sunyi matukar dacewa da junansu,akan comment section idonta ya sake sauka a inda wani yayi commenting "God bless this union"rintse idonta tayi ta bude ta rasa meyasa gabanta ke matukar faduwa sannan zuciyarta ke bugawa haka?meyasa ta damu da abinda be kamata ta damu ba?meyasa zata tayar da hankalinta don kawai Iqbaal ze qara aure?hakan yana nufin tana kishi akansa ne?Oh no this is capital NO wannan bazai taba yiwuwa ba shine abinda zuciyarta ta fada cikin sauri ta mikawa maryam wayar cikin tsananin kunya tace "who cares"yaje chan yayi ta kara aurensa coz ni dama chan i am expecting morethan this from him

"Janyo hannun moon maryam tayi sannan ta kalleta face dinsu yake fuskantar juna tace moon idan bacci kikeyi ki farka,idan kuma ciwon hauka ne a kanki toh ki nemi mental drugs domin babban kuskuren da zakiyi a rayuwarki shine ki bari Iqbaal ya auri wata mace a wannan kalar zaman da kukeyi dashi

"Cikin mamaki moon ke sake kallon maryam,a hankali tace maryam meyasa kikace haka?ko kin manta wanene Iqbaal mutumin da bai damu da rayuwata ba mutumin da rayuwar lalacewarsa da shaye shayensa ya fiye masa komai a duniya taya kike tunanin cewar zanyi asara idan na rasa Iqbaal?

"Murmushi maryam tayi tace moon having Iqbaal as a husband is a full time war,yaqi ne babba me zaman kansa amma ke karki manta kin samu Iqbaal a sama ba tare da kinsha kowanne kalar wahala ba,moon kar kiyi wasa da damarki yanzu shine lokacin da ya dace ki kwace mijinki a hannunki,nasan kinason iqbaal kuma kina kaunarsa please moon prove it ki nuna mishi irin soyayyar da kike mishi kar kiyi wasa da damarki.....wait maryam shine abinda moon ta fada da karfi sanda zuciyarta ke bugawa da sauri tace who told you ina sonshi?

"Your face always defines what is in your mind moon....shine abinda maryam ta fada a takaice

"Da sauri moon ta kalli fuskarta a jikin mirror din da take hangowa tace my face?da sauri maryam ta daga kanta tace of course nasan a yanzu haka kina ji  a ranki kamar ki fasa ihu saboda tsananin kishin ganin iqbaal da wata a jikin hoto sedai har yanzu kina da damar da zaki dawo da mijinki hannunki moon kar kiyi wasa da damarki ki taimaki soyayyar wannan cikin da yake jikinki moon,a hankali hawaye ya sauko daga idon moon ta kalli maryam wacce itama idonta yayi ja kamar me shirin yin kuka tace maryam bani da sauran wata hanya da zan iya janyo hankalin Iqbaal saboda tun farko babu wata soyayya da take tsakanina dashi hakan ya nuna min cewar wannan yarinyar itace zabin Iqbaal wacce yakeso yayi rayuwa da ita ba ni ba wacce akayi mana auren dole dagani har shi sedai a koda yaushe ina matukar jin tausayin rayuwar Iqbaal maryam

IqbaalWhere stories live. Discover now