Chapter 19

286 46 13
                                    

"Duk da bacin ran da moon keyi da iqbaal be hanata yin shirye shirye ba kamar wata karamar yarinya take shirya komai gani takeyi kamar idan tayi wasa da damarta zata rasa komai,tasan morning flight zata bi ya sanyata kwanciya da wuri bacci mai nauyi yayi gaba da ita sedai time to time tana farkawa ba tare da tasan dalilin yin hakan ba

"Murmushi tayi a hankali ta janyo littafinta na addu'oi ta fara karantawa bayan ta sanya seat belt dinta idonta ya sauka a kyakkyawar background din airport din kasancewar window seat shine favorite din moon wow home sweet home ta fada a hankali inda take kallon sky a hankali jirgin yake tashi tana sake samun damar kallon sky daga nan ta mayar da hankalinta wajen karatun adduointa,sedai duk lokacin da ta tuno da cikin da yake jikinta wani irin takaici yana matukar kamata sam yaron da yake cikinta beyi sa'ar mahaifiba mutum mugu mazinaci kamar iqbaal be dace ace ya zama uba so soon ba

"Bata dade tana jira a airport ba mutum 2 daga cikin guards din gidan iqbaal suka karaso suka karbi traveling bag dinta inda tabi bayansu,oh shit!ta fada a hankali ganin sunyi parking a kofar gidanta,sam moon batayi niyyar sauka a gidanta ba son ranta a kaita gidansu ta karashe kwanakinta duk sanda iqbaal yazo sai ta koma gidanta amma tasan tunda aka sauketa nan toh umarnin dad ne ya zama dole tayi following rule dinsa,a gajiye ta shiga bathroom tayi wanka idonta ya sauka akan dining area wanda aka cikashi da food flask kala kala,wow ta fada a hankali tayi saurin karasawa ta fara budewa colours din abinci kala kala masu matukar birgewa tana da tabbacin daga gidansu iqbaal aka kawo wannan abincin,zama tayi taci abincin sosai da drinks natural masu matukar dadi da birgewa tayi mamakin yanda taci abincin dayawa sosai...simcard din wayarta ta cire ta sanja cikin tsananin farin ciki ta fara kiransu nimcy face time a lokaci daya gaba daya freinds din sukayi picking video call din

"Hey lovelies ta fada fuskarta cike da farin ciki

"Hey girl moon have you see yourself in mirror?maryam ta fada cikin tsokana

"Bata rai moon tayi kadan tace no any problem?

"Malama kalli yanda kikayi kyau kalli kumatunki omg i'm dead kin koma orobo..maryam ta karasa magana tana dariyar tsokana

"Tsaki moon tayi tace kanku akeji you know how i missed you ba,so yaushe zan ganku?

"Murmushi sukayi a tare sukace not that soon ooo ki gama hutawa sosai...sun dade suna waya kafin suyi sallama bayan sun gama tsokanar moon

"Tunda moon ta dawo 9ja iya kacin gidansu iqbaal da gidan aunty falila kadai taje ta gaishesu kowa kallo daya yakeyi mata ya tabbatar da tana dauke da ciki ganin yanda moon ta kara wani kyau mai masifar birgewa...yau kwanan moon 5 da dawowa 9ja sedai sam babu labarin iqbaal balle ma ya kirata yaji labarin ya ta iso

"Knocking din da akeyi kamar zaa fasa kofa yasa moon saurin farkawa daga baccin da takeyi a tsorace ta sanya cap a kanta ta sauko daga bed din ta nufi kofar cikin mamaki da tunanin shin waye yake buga kofa haka cikin tashin hankali,idonta cikin mamaki take bin iqbaal da kallo da kyar ta daga lips dinta ba tare da tasan tayi hakan ba tace is that you?

"Harara ya sauke mata bayan ya ajiye traveling bag din hannunsa a gefe yace "may be"

"Harararsa tayi cikin tsananin tsana ta juya zata koma daki sedai da sauri iqbaal ya kama hannunta yace hey sau nawa zan fada miki cewar doctor ta fada miki cewar ki dinga yin aiki kina exercise din jikinki amma sam baki da aiki sai kwanciya shiyasa nazo nayi checking dinki saboda nasan baki da cikakken hankalin da zaki kular min da abinda yake cikinki right?

"Kallonsa tayi a wulakance dariya kadan yaso kwace mata tace ohh ai bansan ma kana da wani baby a wajena ba,kaga mallam please don't disturb me ka koma ka tambayo yanda ake rainon cikin dai daga step na farko har na karshe tukunna sai ka dawo ka fadamin amma ba yanzuba da bakasan komaiba,bata jira ya sake magana ba tayi juyawarta daki tayi locking door tana mamakin shin wanne irin daliline ya dawo da iqbaal nigeria a irin wannan lokacin?

IqbaalWhere stories live. Discover now