Chapter 9

703 78 4
                                    

"Gidan Aunty falila cike yake da manyan baki wanda yawancinsu daga nesa suka zo,shirye shirye akeyi kamar babu gobe wajen ganin bikin Iqbaal da maimoon ya kammala

"Kamar karamin yaro haka Iqbaal yayi hugging mom cike da zumudi da farin cikin ganinta,oh god Iqbaal you are too heavy sake ni a gurin nan kar ka karyani mom ta fada tana rankswashin kansa,dariya yayi yace naji din mom you are welcome to 9ja,murmushi tayi tace thank you Iqbaal na gaji sosai kasan banason doguwar tafiya kuma kaga tafiyar 6 hours and 43 minutes is not a small deal

"Dariya Iqbaal yayi yace mom don dai kawai kin tsufa ne shiyasa,hannu tasa ta ja mishi kunne ya danyi kara kadan yace mom idan ba tafiya muka yi a wajen nan ba yanzu zaki tasheni a aiki,guards ne suka bude musu mota suka shiga,basu wuce 20 minutes  ba suka karasa gida,sosai Iqbaal ke farin ciki kamar karamin yaro duk inda mom ta sanya kafarta nan yake sanyawa,abinda ya bawa mom mamaki shine ganin sam tunda tazo Iqbaal beyi mata zancen aurensuba sedai hakan sam be dame taba

"الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور"
(Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.)Shine abinda maimoon ta fada bayan bude idonta da tayi sannan a hankali ta sauka daga kan gadon ta shiga bathroom ta daura alwala,bayan ta iddar da sallah ta dade akan dadduma tana adduoi sannan ta mike jikinta sanyaye ta tsaya gaban dressing mirror tana kallon kanta,sosai take matukar tausayin kanta hawayene suka gangaro daga idonta cikin muryarta me sanyin gaske tace Ya Allah!Ka dubi wannan jihadin da zanyi ka bani iko Allah ka tausaya min Allah ka saukaka komai nasan auren Iqbaal ba karamin jarabawa bace a rayuwata ya Allah ka bani ikon cinyeta amin,turo kofar dakinne ya sanya maimoon saurin juyawa,falmata,mufeeda,nimcyluv da mubeena ne suka shiga dakin fuskokinsu cike da farin ciki

"Amarya mu da mukazo tashinki a bacci ashe ke har kin riga kowa tashi saboda you are so excited ko?nimcyluv ta fada a takaice tana dariya

"Ai ni yanda na kalli idon maimoon bana tunanin ma tayi bacci wlhi saboda zumudin auren Iqbaal baze barta ma tayi bacciba falmata ta fada tana zama a gefen gado

Kallon mubeena da mufeedah tayi tace toh ku kuma me zakuce?ya Allah ni kadai nake da kawaye masu shegen surutu ne?maimoon ta fada tana zama gefen gadon itama lokaci zuwa lokaci gabanta yana faduwa

"Kinga malama ki zauna muci abinci saboda makeup artist yanzu ta kirani waya nan da 1 hour zata karaso cewar mubeena ta karasa magana tana karbar tray din abincin su daga hannun daya daga cikin masu aikin Aunty falila

Kunga malamai waye ya fada muku ina jin yunwa ne?ku dai da kuke jin yunwa sai kuyi tacin abincinku amma ni a koshe nake,dariya nimcyluv tayi tace naji dama nasan yawancin amare basa cin abinci kuma basayin sallah ranar bikinsu amma nasan ke bakya daya daga cikinsu saboda haka ki zauna muci abinci maimoon kinfi kowa sanin how we care about you and finally kinsan we are going to miss you so please maimoon kici abinci tare da best freinds dinki please......

Turo baki maimoon tayi tace uhmmm dramatic queen kenan wannan idan kika shiga film tsaf zakiyi kasuwa saboda kin iya yaudara amma dai congratulation tunda yaudararki yayi tasiri a kaina girls let's eat together maimoon ta fada tana murmushi

Murmushi suka sakeyi a tare sukace cheers.....sannan suka fara cin hadadden wainar shinkafa da kunun madara,ita kanta maimoon tayi mamakin yanda taci abincin dayawa saboda bata yi tunanin zata ci abinci me yawan haka ba

Bathroom ta shiga tayi wanka da ruwan hadadden turaruka wanda ta dade tana amfani dasu tunda Aunty falila tayi mata order kayan kamshi na yan ajin tubarkallah gurin hajiya husna kamshi ikon Allah,bata jima ba ta fito daga wankan inda jikinta yake tashin kamshi

IqbaalOnde histórias criam vida. Descubra agora