Chapter 16

304 46 19
                                    

Da gudu iqbaal ya dauki maimoon kamar wata jaririya ba tare da yasan yana yin haka ba,cikin mota ya sanyata da sauri ya rufe door din duk da yawan maganar da ma'aikatan hotel din keyi masa cikin yarensu na french"excusez moi puis-je vous aider"

Cikin sauri ya daga musu hannu yace "merci Je suis d'accord"ya shiga mota cikin sauri ya fara tafiya,daidai madaidaicin clinic din dake hotel din yayi parking ya sake daukan moon suka shiga da sauri likitoci suka fara aikinsu cikin kwarewa da girmamawa

Sai da moon ta samu cikakken hutu na sama da 6 hours kafin ta farka daga bacci ta shiga toilet din dake cikin dakin ta daura alwala ta gabatar da sallolin da tayi missing,a hankali ya tura kofar ya shigo hannunsa rike da ledoji da alama abincine da drinks don kallo daya tayiwa ledar hannun iqbaal ta gano cewa ledar querento ne wanda ya zama restaurant din da tafi jindadin abincinsu tun zuwan ta paris,sau da ya jira ta karasa addua sannan ta mike ta zauna gefen gadon ba tare da ta yiwa iqbaal kallon arziki ba,abincin cikin ledar ya fara fitowa dasu da drinks ya ajiye gabanta cikin muryarsa marar karfi yace you have to eat something

Wow this is heaven ta fada cikin zuciyarta jin yanda kamshin chicken biryani ya shiga hancinta sai croissant wanda shima ya zama best pastry din da tafiso a paris,hade rai tayi ta turo baki tace thank you amma yanzu bana jin yunwa yana da kyau kayi saurin daukeni daga gurin nan daka kawoni coz i am allergic to hospitals i guess kaine ka kawoni nan for no reason right?

You jerk....ya fada cikin fushi sannan ya gyara tsayuwarsa yace who told you ina da lokacin shirmenki yanzu?kinga yanzu dai tunda kin warke ina jiran doctor ya baki result din wahalar da take damunki kafin ki fara min complain dinki na banza da wofi,shigowar doctor ne ya hana moon yin magana da sauri iqbaal ya karasa kusa da doctor yace hey

Murmushi yayi sannan ya kalli moon da iqbaal cike da kulawa yace congratulations lovelies sannan ya mikawa iqbaal paper din dake hannunsa yace an sallamesu zasu iya tafiya,ba tare da wata damuwa ba iqbaal ya karbi takardar hannun doctor sedai tuni cikin moon yayi wani irin mugun juyawa jin doctor na fadin congratulation....congratulations for what?shine abinda moon ta maimaita ba tare da tasan ta fadi hakan ba da karfi har iqbaal na iya jiyo abinda take fada,murmushi iqbaal yayi bayan ya karanta takardar sannan ya mikawa moon da tayi mutuwar zaune,cikin sauri ta karbi takardar ta duba ya salam ta fada da karfi cikin tsananin tsoro tare da mikewa tsaye tace what?Baze yiwuba this is capital NO wallahi karya kakeyi iqbaal bazan taba hada zuri'a da fasiqi mazinaci irinkaba wai ma in cema yaya na me idan sun girma?hell no this will never happen ta karasa magana cikin kuka tana girgiza kanta kamar wacce ta fara zarewa

Bushewa yayi da dariya irin wacce bosawa keyi cikin films musamman azzalumai,sannan ya hade ranaa fuskarsa babu alamar wasa yace heyyyyyyy idan kin gama madness din naki ki hada kayanki we have to go saboda anyi mana check out ko bakisan irin kudaden da na biya ba kafin na kawoki asibitin nan?yana da kyau ki sanya idiot shoes dinki ki kama hanya ki fita daga dakinnan idan kuma kin shirya biyan wasu kudaden ne don ki samu hutu toh nan asibiti ne not a hotel room got it?

Turo kofar da akayi ne ya sanya moon da iqbaal yin shiru suka kalli matar data shigo hannunta rike da littafi da alama signing iqbaal zeyi na cewar an sallamesu sun bar dakin,murmushi yayi ya karbi littafin yayi signing sannan ya dauki key din motarsa dake ajiye akan table ya kalli moon yace let's go babe cike da kwarewa a rainin hankali da iskanci

Takalminta tasa saboda bata da wani option wanda ta wuce ta fita daga dakin saboda matar dake tsaye tana jiran su,kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta shiga motar har suka karasa hotel din babu wanda yace wani abu duk da tsakanin tafiyar tasu babu wani nisa,jikin moon sanyaye ta zauna a palour lokaci zuwa lokaci tana kallon iqbaal cike da tsana da tsananin takaici,ganin yana shirin fita ba tare da wata damuwa a fuskarsa ba yasa moon fincikoshi cikin damuwa tace kaga mallam bafa fita zakayi ba wlh bazaka fita ba sai ka fadamin menene matsayin cikin nan na jikina don babu abinda ze hanani cire abinda yake cikina bazan taba yarda na hada zuri'a da dan iskan mutum ba irinka wlh iqbaal na tsaneka na tsani duk wani abu da ya fito daga hannunka bazan cuci yaron da besan hawa ba besan saukaba saboda nasan tsana da kiyayyar da nake yi maka shima zata shafeshi ya zama dole ka daukeni da hannunka ka kaini a cire wannan abin da yake jikina ta karasa magana tana nuna cikin ta

Saukar marin da taji a fuskarta ya sanya moon fashewa da kara cikin mamaki take sake kallonsa,point of correction mss 9ja duk sanda zaki zageni ko zaki aibata ni karki sake gangancin hadawa da wannan yaron da yake cikinki saboda ina sonsa kuma ya fiyemin mata irinku dari ina fatan kin gane dalilin da yasa na mareki mss 9ja....and finally i have recorded all your madness in here ya karasa magana yana nuna mata wayarsa sannan ya gyara tsayuwarsa yace don haka wallahi tallahi duk abinda ya samu wannan cikin na jikinki se nayi shari'ah dake a court sannan kinsan babu wanda ze barki a raye idan aka gano cewar kinyi kisan kai ko?....9 months is like 9 seconds to me don haka da zarar kin haifar min yaron zaki iya ajiye minshi ki kama gabanki baki da sauran amfani a wajena kamar yanda kika tsaneni nima na tsaneki yana gama fadar haka yayi ficewarsa daga dakin gaba daya

Zubewa tayi a kasa ta fashe da wani irin kuka mai matukar tsuma zuciya,you guess it wrong iqbaal 9 months is like freaking 90 years to all mothers in the world,ina ganin yanda mata dayawa suke shan wahala daga ranar da akace sun samu ciki basu da wata nutsuwa har sai sun haihu daga ranar da suka haihu wahalar zai karu ne wanda zasuci gaba da raino ina iya cewa har karshen rayuwarsu,iqbaal meyasa zaka min haka na shiga 3...karar wayarta ne yq sanyata dakatawa daga kukan da takeyi da sauri ta wanke fuskarta ganin number mum din iqbaal ce take kiranta,muryarta a sarke tace hello world best mom ina wuni?

Lafiya lau maimoon ya jikin naki?mom ta fada cike da kulawa

Cikin mamaki moon tace da sauki tana sake mamakin shin waye ya fadawa mom bata da lafiya kuma?

Ayya Allah ya baki lafiya moon,ai dazu nayi ta kiran wayarki baki picking ba shine na kira mr london yake fadamin baki da lafiya kina asibiti ma kina samun hutu ne,sai kuma yanzu da na sake kiransa yake sake fadamin cewar ai an sallameku ma ashe na kusa samun siriki masha Allah maimoon naji dadi sosai Allah ya saukeki lafiya mom ta karasa magana cikin farin ciki

Zaro ido moon tayi a zuciyarta tace shikenan karyata ta kare wato iqbaal har ya fara spreading cewa tana da ciki saboda kar ma tayj gangancin zubar dashi kenan ko?toh wallahi iqbaal ko duk duniya zaka sanarwa babu abinda ze hanani cire wannan cikin daga jikina,jin moon tayi shiru yasa mom sake mata magana da sauri moin tace ammmm mom nagode sosai sedai don Allah ina neman alfarma wajenki akan ki fadawa iqbaal ya barni in koma nigeria tunda shi har yanzu be gama aikin nashi ba kuma ni nan kadaici ya dameni wlh ta karasa magana kamar zatayi kuka

Dariya mom tayi tace eh nima nayi tunanin haka don na fada masa ya dawo dake ko gidansu ne amma yace a'a shi yafiso ya dinga zama kusa da matarsa so ina ganin duk abinda zaki neman iqbaal i ready to help sannan banda abinki moon yanzu matan zamani wacce matar ce zatayi gangancin rabuwa da mijinta ta barshi shi kadai ai ina ganin kiyi zamanki kawai yace idan ya kammala komai zaku dawo tare.....cikin ladabi moon ta amince da maganar mom sannan ta kashe wayar suka yi sallama

Mikewa tayi ta shiga bathroom tayi wanka ta sanya sleeping dress dinta ta kwanta saboda rashin karfin jikinta da take ji sedai ko alama babu alamar bacci a idonta sai tsananin damuwa kawai da take damunta wanda ta rasa wa zata fadawa damuwarta,knocking door shine ya sanyata mikewa da kyar ta karasa cikin sanyin murya tace who's that?

Jin wanda yayi magana yasa ta bude kofar,cikin turancinsa da baya fita sosai yace evening ma'am this is from iqbaal sayeed ya karasa magana yana mika mata manyan ledoji da suke cike ga kuma nauyi wanda batasan menene a cikiba,da kyar ta karbi ledoji cikin murmushi tace "merci" sannan sukayi sallama ya juya ya tafi,har ta wuce zata shige bedroom sai dai ta tsaya ta bude fara bude ledojin da ta ajiye a gefen couch....baki bude moon take bin kayan da kallo tare da yin mutuwar tsaye ganin yanda ya ciko manyan ledoji da kayan babies wanda aka kashe thousands of dollars wajen siyansu

Eid mubarak....i hope you celebrated your eid better than ever god bless us amin❤️🙏🏻

I love you all❤️
See you in next page

IqbaalWhere stories live. Discover now