Yana zama a kusa da ita yaga da d'an ja kujerar ta koma baya, yarda su kausar baza su gane ba, kamal murmushi yayi yayin da ya saka hannun shi ya jawo da kujerar ta kusa dashi, sauran k'iris ya k'ara kai hancin shi kan wuyan ta dan ya shak'i dadd'an kamshin ta da ya mamaye mishi kwakwalwa yayi saurin dakatar da kanshi, wata irin harara ta daka mishi, shi kanshi baisan mai ya saka ta kyale shi yake yin yarda yaga dama da ita ba, haka ya k'ura mata ido, yana shafa bayan ta a hankali har da wuyan ta da k'afad'unta, ita kuwa idanunta ta maida kan su kausar, tayi kamar baya wurin har kamila tazo kanshi tayi serving d'inshi, sai lokacin ya maida hankalinshi gaban shi, fried rice ce tasha hanta da vegetables, mac and cheese, potato salad, snacks, kebab, chicken nuggets da dai sauran su, abinci ba damun shi yayi ba amma gaskiya abincin gaban shi ya bashi sha'awa, mai da idanunshi yayi kan sakeena, dan halin da ta nuna yau ba k'aramin mamaki ta bashi ba, yarda ta tashi ta zage tayi wannan hidimar kamar bata tsane shi ba, bai san ya dad'e yana binta da kallo ba har sai da yaji kausar na cewa,
"Ya kamal, abincin ka zaiyi sanyi"
Sannan da sauri ya maida hankalin shi kan abincin tare da d'aukan spoon, a hankali ya fara tsakura kamar baya so, yana kaiwa bakin shi baisan lokacin ta ya zaro idanunshi waje ba, kan ya ankara ya k'ara d'ibowa ya saka a bakin shi, kan kice me ya fara saka loma, sai dai ya cinye komi na gaban shi tsab sannan ya d'ago yana goge baki da napkin ya had'a ido da kamila da kausar da suke mishi murmushi,
"Tunda nake yau ce rana ta farko da na tab'a ganin ka cinye abincin plate d'inka"
Kamila ta fad'i tana maganar kausar na d'aga kai alamun itama ta yarda,
"Nima haka,"
kausar tayi maganar tare da maida hankalinta kan sakeena, wacce har lokacin idanunta nakan abincin gabanta tana tsakora dan ba ci take ba, amma daga ganin hankalinta nakan su, duk tana jin me suke cewa,
"Ya sakeena kina da labari sai yayi 2 days ba abinci a cikin shi sai dai yayi ta shan fruits ko smoothie, mami da abba ba asibitin da basu kai shi ba daga k'arshe choronic ulcer ce ta kama shi da in ta tashi sai yayi kamar zai mutu"
kausar akwai shegen surutu, duk kallon da kamila ke mata na da tayi shiru amma ina, zai zuba take kamar famfo, a hankali ya maida kallonshi kan matar shi wacce yanzu itama ta ajiye spoon din hannunta tana kallan kausar, fuskar ta sai sa sai sa,
"Tunda yazo hannuna yanzu zan tabbata ulcer d'inshi baza ta k'ara tashi ba, zan kula dashi fiye da yarda kuke tsamani"
Dariya ce taso ta kuboce mishi dan yasan duk maganar ta k'arya ce dan duk duniya ba wanda zai so ya mutu sama da ita, maganar kamila ce ta dawo dashi daga tunanin da yake,
"Kai wallahi ba abinda zamu cewa da Allah sai godiya da ya bamu suruka irin ki, ya kamal is very lucky"
Yana ganin sakeena ta saki murmushin yak'e tare da mik'ewa da fara kwasar kayan da suka ci abinci dan yin kitchen, yasan abunda take shirin yi wanke wanke, a hankali ya jawo hannunta, sai gata akan cinyar shi, ya had'a bayanta da k'irjin shi, ya fara mata rad'a a hankali, amma rad'an ko su kamila zasu ji shi,
"Baby nace kin gaji da yawa, ki barsu suyi wanke wanken ke ki zauna ki hutu kinji"
Yana ji tana so ta kwace daga jikin shi amma yayi mata mugun kamu, banza yayi da ita tare ta kwantar da kanshi akan k'irjin ta,
"Gaskiya kam, nida kausar dai bamu gaji ba tunda flight muka hau, bari muyi wanke wanken"
Kamal najin abinda kamila tace ya mik'ar da sakeena daga jikinshi tare da ruke hannunta ta da fara janta, ko da wasa bai kai idanunshi kanta ba dan yasan ba abunda zai gani a fuskar ta sai wannan disgusting look d'in da take mishi wanda yake had'e da tsana, kada ta damu dan shima haka ne daga wurin shi, dole ce kawai ke saka shi yin abunda yake,
Suna shiga bedroom d'inshi ta fusge hannunta da mugun k'arfi, bayan ya kullo k'ofar, tare da saka duk k'arfinta akan k'irjin shi da ture shi daga kusa da ita, kallan shi take, kallan da baya dauk'e da komi sai tsan tsan k'iyayya,
"Kai wana irin d'an rainin wayo ne? Dan na yarda zanyi kamar ba komi a tsakanin mu bance ka dunk'a tab'a ni kana shiga personal space d'ina ba,"
Kwata kwata baiyi mamaki ba, yasan daman ya gama k'ular da ita, hannunshi ya nad'e akan fad'edan kirjin shi fuskar shi d'auke da murmushi, a hankali a niste ya fara ce mata,
"Ki dube ki da kyau, kiga kinyi irin kallar matan dan zanso tab'awa in har ba dole ba?"
Sannan a hankali ya matso dab da ita, fuskar shi har lokacin tana d'auke da murmushi, a hankali ya k'ara furta,
"Ko duk matan duniya gaba ki d'ayan su sun k'are ke kad'ai kikayi saura bazan tab'a sha'awar ki ba, kada ki manta kin bud'e k'afafun ki ma wani gardi kwanaki da suka wuce ya gama amfani da ke, banga mai zanyi da ragowar wani k'at.."
Kan ya k'arasa zancen shi ta d'auke shi da wani wawan mari da a take yastunta biyar sai da suka fito a farar fuskar shi, a hankali kamal ya juyo da fuskar shi da tayi gefe dan sanadiyar marin ya sauke akan ta, idanunshi sun k'ad'a sunyi jaa, mace bata tab'a tunanin marin shi ba sai yau, wata irin tafasa zuciyar shi ta fara amma duk abinda yake ji yasan bai kai kwatan abinda sakeena kije ba a lokacin, idanunta suma sunyi jaa bayan hawayen dake ambaliya a fuskar ta, abun tausayin ya mamaye fuskarta, daga gani maganar da ya gaya mata ba k'aramin ciwo da zafi tayi mata ba, tsanar da take mishi ta k'ara bayyana a cikin kwayar idanunta, a hankali muryarta na rawa ta fara ce mishi,
"In addu'a da Allah ya d'auki raina cikin gaggawa in har zaman da zanyi dakai a rayuwata na dindindin ne"
Yarda tayi maganar itama sai da ta saka dukkan tsanar da take mishi a muryar ta, ga cikin sanyin jiki tayi maganar sai tayi mugun baka tausaya, tana kuma gama zancen ta ta fita daga d'akin shi da gudu fuskarta ta bac'i da hawaye, kamal naji ta buga k'ofar ya lumshe idanunshi tare da d'ora hannunshi akan kyakyawar fuskar shi, wani irin takaici yake ji, abunda ya bashi mamaki shine rashin jin k'unar ran da yayi da ta mare shi, ya tabbata da wata ce sai ya b'alla hannunta, a hankali ya sami wuri ya zauna akan gadon shi, ya k'ara lumshe idnunshi da jan laulausan gashin kanshi, ba abinda ke yawo a kwakwalwar shi irin maganarta ta k'arshe da abinda ke d'auke a idanunta bayan ya gaya mata maganar,
"Anya yana kyautawa abinda yake mata?"
Ya fad'i a ranshi, sai dai yana fara tunanin yayi saurin kawar dashi yayin da wata zuciyar ta tuna mishi da irin rayuwar da kamil yayi saboda ita,
"Ita ta kashe kamil ka manta?, farin cikin ka shine ka ganta a cikin k'unci da bak'in ciki, ka lalata mata rayuwar ta"
Amma me yasa yanzu baya jin da-, sauri yayi ya girgiza kanshi tare da k'ara kawar da tunani gefe, a hankali ya mik'e dan ya fara bama kanshi tsoro, parlor yayi dan ya koma wurin k'ananshi, yasan dai ba wanda yaji komi a cikin su dan shi da sakeena ba wanda ya d'ag murya in har ba ganin ta sukayi da ta fito daga d'akin shi da hawaye ba.
(Okay, i think i will be updating less saboda makaranta, project practicals d'ina ya fara caza mun kai 😂, but i will try na dunk'a updating yarda na saba, ina gaya muku ne dai in har ban samu nayi ba,
Dont forget to share, comment and vote❤️❤️)
YOU ARE READING
ZAFIN RABO ✔️
RomanceLabari ne da ya k'unshi tsana, k'iyayyaya, mugunta, da uwa uba soyayya. Ku biyo ni kuji me zai faru a littafin //Zafin Rabo//