Forty two

2K 211 48
                                    

A hankali ya bud'e idanunshi yayin da yaji k'arar mota, so yake ya tashi ya bita amma baya jin k'afafonshi zasu iya d'aukan gangar jikinshi a yanzu yarda yake jinshi, wani irin rawa jikinshi yake bayan wani irin zafi da azaba da zuciyar shi take mishi, azabar da baii tab'a ji tayi ba dan har wani duhu duhu yake gani har sai da ya bud'e bakinshi yana neman numfashi dan yaji yana san guduwa, hannu ya sa a daidai inda zuciyar shi take yayin da ya saka duk k'arfinshi ya matse k'irjinshi.

Wani irin nunfashin yake fitarwar, d'aya bayan d'aya yayin a hankali ga idanunshi ba abunda suke sai zubar da kwalla masu mugun rad'ad'i, duk matse k'irjinshi da yayi bai dai na mishi zafi da ciwo ba sai ma ji da yayi kamar an samo garwashin wuta da kuma barkono an watsa mishi a zuciyar sa.

Wani sabon hawaye ne ya zuba da yaji motar ta fita daga gidan, shikenan abba ya tafi da farin cikin shi, hannunshi ya cire ya d'ora akan fuskar shi yayin da kuka ya kub'uce mai, ko yarda yake fitar da sautin kukan kasan yana cikin tsan tsan k'unci da ciwo, kowa yaga kamal a wurin dole ya baka tausayi kuma ya girgiza koda mara imani ne, kuka yake kamar jariri sai da ya shafe mintoci yana abu d'aya can kuwa yayi shiru yayin da ya jinginga a jikin kujera, carpet d'in parlon yake kallo amma kana gani kasan gaba d'aya hankalinshi baya wurin, ko kiran sallar magribar da aka fara bashi da alamun yaji.

                 ———————————————

Yarda yayi a wurin kamar gangar jiki ba rai, ko mosti baya yi, sai dai d'igin hawayen dake zuba daga idanunshi, imran da ya shigo ya ganshi sai da yaja baya dan ya tsorota ga parlon yayi duhu ko fitilar kwai be kunna ba.

Sai da imran ya kunna fitilar parlon ya gwarye da haske sannan kamal ya d'an mosta yayin da ya lumshe idanunshi da alamun hasken ya mishi yawa, a hankali imran ya masto kusa dashi da zama a gabanshi, wani irin tausayin abokin nashi ne ya kama shi yanzu kwata kwata baya jin haushin kamal ba kamar d'azu ba dan zai iya cewa yana d'aya daga cikin mutanen da suka san kamal kamar yunwar cikin shi, bayanin da yaji daga wurin shi da sakeena da kuma yarda ummeeta tayi jikinshi na bashi baiji abokin nashi ya aikata ko wane irin mumunan abu, laifin shi d'aya kawai abunda yayi ma matar shi ta sunna.

Sun shafe mintuna talatin a haka imran ya kasa cema kamal komi dukda so yake yayi mishi magana, gaba d'aya tausayin abokin nashi yake ji amma be san yarda zai rarashe shi ba, kamal shima yayi shiru har lokacin idanunshi na lumshe, farar fuskar shi ta kowa jajawur har wani fad'awa yayi na yini d'aya cak, da imran yaga abu bazai yuwu ba ga shirun yayi yawa ya bud'e baki dan yin magana kamal ya tsai da shi.

"Abba ya tafi da ita"

Cikin muryar me rawa tana sark'ewa ya fad'i, dukda kanshi na sunkuye amma bai hana imran gani hawayen dake zuba ba, take yaji tausayin abokin na shi ya k'ara nininkuwa a ranshi, sai da sukayi sakwani a haka kamar kamal nasan taro nustuwar shi, sannna a hankali ya k'ara cewa.

" A lokacin na zata shine abunda ya dace da ita saboda ta sanadiyar ta kamil ya wahala, takaicin da haushin yarda santa ya kashe mun d'an uwa shi ya saka na saka a wulaqanta ta"

Koda yake magana be d'ago ya kalli abokin nashi ba har yanzu idanunshi nakan carpet, shi kuwa imran yayi shiru kawai yana jinshi amma ba abunda yake ji sai tausayin abokin shi da irin kuskuran da ya tafka gashi yanzu yazo ya afka kogin sonta,

"Kasan irin danasanin da nayi?"

Sai a lokacin ya d'ago ya sauke idanunshi akan imran, wanda sun koma jaja ye ga sun kumbura sunyi suntum, tsabar tashin hankali, imran kuwa duk ya bashi hankalin shi,

"Duk lokacin da na saka ta a idanuna sai na tuna abunda na mata, in har ta kalle ni cikin ido sai naji munfashi na ya sark'e mun kamar an d'auke dutse me nauyi an d'ora mun shi anan"

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now