Thirty two

1.8K 176 17
                                    

Koma tsit yayi a d'akin bayan kamal ya gama kora jawabin shi, kana ganin dr kabeer ba k'aramin shan jinin jikinshi yayi ba, kamal kuwa har lokacin idanunshi nakan docton din jira yake ya k'ara wata maganar da bata mishi ya kuwa nuna mishi koshi wane da abun da zai ya yi mishi, sakeena ita kuwa baki a hangame, ta kasa daina kallan kamal, dan a ganinta mugun k'arfin hali yake dashi bayan rainin hankalin da yayi mishi yawa.

Jajayen idanunshi da basa dauke da ko d'igo d'aya na wasa ya cigaba zubawa doctor kabeer dan jira yake yaga ya b'ace mishi daga gani, dr kabeer jiki a sanyaye sum sum yabar d'akin be k'ara iya magana ba, yana tura k'ofar, sakeena ta saka duk k'arfinta ta tsige jikinta daga hannun kamal, itama ranta a b'ace ta sauke idanunta akan shi.

"What is wrong with you??"

Da tsawa da fad'a duka ta had'a tayi mishi tambayar, me yake nufi da yi mata haka a gaban shi, ta mugun tsnar yarda yake wani kamata a gaban jama'a kamar akwai wani abun arziki tsakanin su, yau harda kiranta matar shi a gaban wani k'ato dan tsabar ya raina mata wayo, ga ya kora doctor dan kawai yazo yin aikin shi.

Kamal kuwa banza yayi da ita kamar ba magana take mishi ba kana gani har lokacin ranshi a b'ace yake, mik'ewa ma yayi daga kan gadon ya fara jan sandar drip d'inshi ya fara hanyar bathroom, yayi ma kamar bata wurin, wani irin haushi da takai ci ne ya k'ara kama sakeena, da sauri ta fara takawa ta tsaya a gabanshi, ranta ya k'ara mutuk'ar bacci, jajayen idanunshi da har yanzu basu koma kalar su ba ya sauke acikin kwayar idanunta, itama kallon shi take,

"Magana nake maka,"

Tana fad'a ta nanad'e hannunta akan k'irjinta tare da k'ara saka idanunta cikin na kamal, jajayen idanunshi basu isa su bata tsoro ba,

"Kowa sai ka kora da halin ka, bayan kasan doctor aikin shi yazo yi, in har baka so ka warke then fine, nima sai na tattara kayana na koma inda na fito dan basan jinyar ka nake ba nima"

Tana maganar tana daka mishi harara, kamal kuwa ya k'ura mata ido baya ko k'iftawa, can kuma ya lumshe su, ya d'an yi sakwani sannan ya bud'e, sun k'ara komawa jajaye, yarda sakeena tace basu isa su bata tsoro ba ta yi k'arya, dan yanzu kamar shi tama canza gaba d'aya, a hankali ya fara takwa kusa da ita har sai da ya matso dab, sannan ya fara magana muryar nan tashi ta zata saka ka jik'ewa da gumi,

"Ki k'ara ambatar shi, wallahi, wallahi sai nayi sanadiyar barin aikin shi a asibitin nan, na kuma sa neman aiki a k'asar nan yayi mishi wahala"

Yana gama maganar ya wuce ta gefan ta ya yayi hanyar bathroom yabar sakeena da baki a hangame, haka ta bishi da kallo har ya kollo k'ofar bathroom, ta dad'e bata ga wanda bashi da fasali ba kamar shi, bashi da dad'in zama ko kad'an, kullum ace mutum na cikin canzawa kamar hawainiya, aiko bai ji dad'in halin shi, ta tabbata kamal zai iya sawa a kori doctor kabeer dan kowa yasan wane ne baban shi a k'asar nan, haka tayi tayin zance a ranta can kuma ta samu wuri ta zauna akan wata sofa tare da kunna tv dan bata ga me zatayi ba.

Kamal yayi mugun dad'ewa a band'aki har ta fara mantawa da shi, sai can ya fito, jikinshi a jik'e, laulausar gashin kanshi shima a jik'e, da towel a hannunshi yana goge kanshi, wando ne kad'ai na sweatpants a jikin shi babu riga, ya tsige abun drip d'inshin dai da ta hana shi cirewa, ko da ya fito daga band'akin bai kalli inda take ba, yi yayi kamar bata zaune a wurin, ga har lokacin fuskarshi a murtuke take.

Ganin shi a haka ba riga kuma sai yawo yake a d'akin ko ajikin shi, ya harda sa ma sakeena tsoro, sauri tayi ta kau da kanta kada ma yace kallon shi take, tsoro ne fal cikin ga so take ta tashi ta bar d'akin amma kuma tasan tana mik'ewa zai gaya mata wani abun da zai saka ranta ya b'aci.

Haka ta k'urawa tv har ta fara jin kamshin turaren kamal alamun ya gama shiryawa, amma ko kad'an bata maida idanunta kanshi ba, tv ta cigaba da kallo abunta, hankalinta har ya fara karkata kan wasan da ake, ba zato taji shi a gabanta, sai da zuciyarta tayi wani irin fad'uwa sannan tayi saurin kallon shi, shima d'in ita yake kallo, yana sanye cikin wani gray jeans da white shirt, yanzu wannan had'e fusar da yayi babu shi, amma kana kallon shi har lokacin kasan he is not in the mood.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now