Forty nine

1.8K 234 35
                                    

Yarda taga rana haka taga dare, kwata kwata ta kasa rintsawa duk yarda take so, ga yau har anyi kwana biyu tun zuwan kamal gudan, kullum bata iya samun bacci, in ma ta kule idanunta ba abunda take gani sai kamal yayin da hawaye ke zuba a idanunshi, a take, ta ke k'ara shiga wani sabun rud'in in ta tuna duk bak'in cikin shi ta dalilin ta ne, tunanin ta a ynazu ya zatayi ta ceto kamal daga halin da yake ciki dukda ita ta jefa shi a ciki, wata zuciyar ta ce shawar ce ta da kawai tayi hak'uri da komi ta yafe mishi ta koma gidan shi, dan shine kad'ai zai zama farin cikin shi, amma kuwa d'ayan b'ari na zuciyar ta sam sam baya san haka, baya san rayuwar gidan kamal ko yaya take.

Ya zatayi, ina zata saka ranta taji dad'i, tana san faranta mishi amma ita kuma farin cikin ta fa?? wasu sababin kwalar ne suka sake zuba mata, a hankali ta saka hannunta goge, ta gaji ta kukan da take, ina ma zata iya dawo da rayuwar baya tun kafin ta had'u da kamil ko kuma kamal, dan a ganinta duk sune suka ruguza mata rayuwar ta.

Jin da tayi anyi knocking k'ofar ta ya saka ta saurin mik'ewa tare da saka hannun da share hawayen ta, dan bata san hankalin mommy ya tashi, gyara zaman ta tayi sannan ta bada izinin shigowa, ko da aka bud'e k'ofar way'anda ta gani sai da abun ya bata muguwar mamaki.

Kamila da kausar ne a tsaye, da sauri ta sauko daga kan gadon tare da d'ora murmushin yak'e akan fuskar ta, suna isowa cikin d'akin kausar tayi wurin ta ta rungume, sakeena murmushi ta saki tare da shafa bayan ta, kamila kuwa na gefe itama sai murmushi take sakar wa.

Samun wuri sukayi suka zauna bayan ta saka blessing ta kawo musu kayan sakawa a baki, kamila ce ta juyo ta mai da idanunta kanta.

"Kingan mu da sassafe ko??"

Sai a lokacin ta d'ago da idanunta ta suke kan yastun hannunta, yarda tagan su haka har gidan su abun ya bata mamaki sosai, har zuciyarta ta fara gaya mata kodai kamal ne jikinshi yayi tsanani, sai dai kuma a zayiri da kwar da damuwar ta sannan ta amsa ta.

"Nasan zuwan ku da dalili, Fatana dai Allah ya saka lafiya"

Murmushi kamila tayi, sannan ta matso tare da kama hannayen ta, "komi lafiya, sai dai wata alfarma muka zo nema, raka mu wani wuri zakiyi"

Shiru tayi a wurin dan bata gane inda zata raka su ba, kada dai asibiti ko gidan su zasu d'auke ta suje dan yanzu kwata kwata bata san rab'on kamal, bata san ganin shi dan tasan in har ta saka shi a idanunshi, gabaki d'aya katangar da tayi ma kanta a dalilin shi zata ruguje ne.

"Ina zamu je?, ba dai asibiti ba??"

Kausar ce tayi saurin yin kanta, tana dariya sannan tace mata "its going to be a surprise, Ya kamal ma an salame shi yana gida ba abunda zai kaimu asibiti"

Wani dad'i taji, dan zata iya binsu ko da bayan duniya ne amma banda wurin kamal, kausar ce ta fara jan hanunta  ta fara faman janta, haka ta cusa ta cikin band'akin ta kullo mata k'ofar, sakeena tsabar mamaki a wurin da ta barta ta tsaya har ba tsawon mitoci sannan can ta fara rage kayan ta ta fara wanka.

Ko da ta fito suna zaune suna jiran ta, haka fito sak'ayo tana takawa, yarda kamila ta ganta tana rab'e rab'e ya bata tabbacin she is not comfortable, mik'ewa tayi tace bari suje suyi ba mommy sallama kannan ita kuma ta gama shiryawa, taba fad'a kausar ma ta mik'e suka fita suka bata wuri.

Shirin ta tayi cikin wata atamfa pink da ratsi ratsin navy blue da white, ta d'auara d'ankwalin ta tare da d'auko farin mayafi ta d'ora akan ta, fuskar ta d'auke da saisa saisan make up ga ta feshe jikinta da turare masu dad'in kamshi, bata san inda zasu ba shi ya saka tayi shigar da baza ta takure ba, jakar ta da wayar ta ta d'auko sannan ta fito, kamila da kausar na ganinta basu san lokacin da suka fara santi ba, suna kwad'a kyan da tayi, ita dai ta bisu da kallo dan a ganinta ba wani abun zo in gani da tayi a jikinta,
yarda dai ta saba shiga haka tayi ma yau, nan suka k'ara yi ma mami sallama sannan suak fuce.

ZAFIN RABO ✔️Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon