Bayan yabi bayan su mami ya tabbata da sun isa airport yayi saurin juyowa ya koma gida, bayan yayi parking a harabar gidan ya fito da yana takawa a hankali har ya isa cikin gidan, yayi zatan zai ganta a parlor d'in da ya barta amma yaga wayam, a tunanin sa ta koma dakin ta shima haka ya fara takawa tare zuwa daidai wurin k'ofar ta, Kamal da wani mugun karfi ya banka k'ofar, ya dan tsaya na sakwani yana dube dube had'e da karasawa cikin d'akin harda bud'e bathroom shima dai bai ganta ba, wani abu ne ya fad'o mishi, kada dai ta gudu?, shi yasan ba san auran take ba, tuni hankalin shi ya tashi da sauri yayi waje dan ya tambaye mai gadi a dai dai lokacin da ya wuce ta bedroom d'inshi ya ganta a tsaye da abu a hannunta ta k'ora ma abun ido, tsaya wa yayi da saurin tafiyar da yake tare da yin wata ajiyar zuciya,
A hankali ya fara takawa har ya isa bakin k'ofa, had'a hannunshi yayi akan k'irjin shi sannan ya jingina da k'ofar ya fara zuba mata kallo, a lokacin k'ara jin wani irin haushin ta yayi bai san daga ina ba, wane ya bata izinin shigo mishi d'aki har ta tab'a wani abunshi?, zuciyar shi ce ta k'ara wani irin hanzarta shi, bai san lokacin da ya daka mata wata irin gigitaciyar tsawa ba, yana gani ta saki abun hannun ta ta juyo a firgice, shi kuwa gaba d'aya fuskar shi ta canza a lokacin, kawai ganinta da yake ya sake saka mishi wani irin bacin rai, sai da ya matso dab ita yaga ta k'ara shigewa jikin bedside drawer din dake bayan ta, jikinta har wani irin rawa yake.
Kamal wani irin mugun kallo yayi mata tare da tsugunnawa da d'aukan frame din da ya fad'i, yana d'ago shi yaga hotan shi da kamil lokacin da suna secondary school, ji yayi wani abu ya soke shi a zuciya, b'acin da ranshi yayi d'azu ba komi bane dan yanzi har duhu duhu yake gani, wane da aikin nan? bai ce kada a saka mishi ko wane abu da ya danganci kamil a cikin gidan nan ba, yasan bai wuce aikin mami ba, damk'e hotan yayi da k'arfi sannan can ya d'aga shi ya rosta shi da k'asa, k'arar da hotan yayi k'ara saka sakeena rud'e wa, d'aga way'annan manyan idanun nashi yayi da sun kowa ja ja wur dan ba'acin rai ya sauke akan ta,
"Wai ya baki izinin shigo min d'aki?"
Yarda yayi maganar sai ya saka ka sakin fitsari muryar shi da fuskar shi basa d'auke da ko alamun wasa, banda rawar da jikinta yake ta kasa yin magana, wani irin haushi ne ya k'ara kama kamal ji yayi gaba d'aya baya san ganin ta a wurin, hannun shi ya saka ya fusge nata hannun da k'arfi sannan yayi parlor da ita, wani irin hurgi yayi da ita har sai da k'ugunta ya daki makeken center table d'in wurin, ta d'an saki k'ara k'adan bai bi ta kanta ba ya fara mata bayanin,
"Kada ki kuskura ki k'ara saka k'afar ki a cikin d'akina balle har ki tab'a wani abu na dan zan iya b'ala miki hannu"
Bayan ya gama nunta da d'an yatsan shi tare da yi mata kashedi ya juya ya koma cikin d'akin, yana shiga ko zama baiyi ba yaji ina ba zai iya zama da ita a cikin gida d'aya ba, komawa parlor d'in yayi ya ganta a inda ya barta tana ta kukan munafinci, ji wani hushin ta ya k'ra ji yaji kamar ya mangare ta, zaiyi mata magana yaga ba shima da time d'in da zaiyi wasting akan ta, ya shiga d'akinta tare da d'auko mata lafayan da yake kan gadon ta, ko da ya dawo parlor d'in ya cilla mata shi a fuskar ta ita kuwa har lokacin, bata bar kukan da take ba,
"Tashi ki saka"
Haka ya tsaya ya tsira ta da ido alamun tayi sauri kada ta b'ata mishi lokaci, sakeena kuwa jikina na rawa ta mik'e ta fara yafa lafaya, da kamal yaga ta kamala tsab ya nuna mata hanyar fita, shima alamun tayi gaba, ta tsaya kamar baza ta tafi ba can kuma ta fara takawa a hankali kamar wace kwai ya fashewa a ciki, amma kannan sai da ta rarumo jakar ta da take ajiye akan kujera tun shigowar su gidan ita da su mommy, yana ganin jakar yayi saurin fusge ta daga hannunta, sannan ya bud'e ya fara lalime, sai dai ya d'auko wayar ta da wallet d'inta, sannan ya maida jan idanunshi kanta
"Wato kina so ki kebe ki d'aya ki kira gida ki kaini k'ara kenan"
Ya fad'i bayan yarda yake nuna mata wayar ta dake hannunshi dai dai fuskar ta, bai bi ta kanta ba da take faman girgiza kai fuska d'auke da hawaye shab'e shab'e, hamdalla kawai yake a ranshi dan Allah ya taimake shi, da mami taji labari kashin shi sai ya bushe, samu yayi ya cire sim d'in wayar sannan ya saka ta aljihun shi, atm cards d'inta kuwa da suke cikin wallet d'inta duka ya fito dasu ya b'alla su gida biyu sannan yayi hurgi dasu, jakar ma cillar da ita yayi gefe d'aya sannan ya saka ta a gaba har suka shiga mota.
Tsit kake ji in banda sheshek'an kukan sakeena, shi kuwa sai sharara gudu yake akan titi kamar ba abunda ya tab'a damun shi a duniya, yi yake yi kamar bata zaune a kusa dashi kuma kamar kukanta baya adabar rayuwar sa, a haka har suka zo unguwar sheka da take a cikin kano, sai da ya sai sai ci wani gida, plastar siminti ne a gidan kamar yaji jiki, sannan yayi parking, daukar wayar shi yayi ya kira wacce zai kira basu jima ba suka kashe wayar, haka ma jiran da sukayi shima baiyi cikkaken minti biyar ba sai ga wata y'ar dattijuwa ta fito, tunda ga nesa ya hango tana washe musu hak'ora, shi kuwa ya had'e girar sama da k'asa fuskar nan tashi a daure, da dattijuwar nan tazo dab dasu kamal ya juya ya kalli sakeena sannan ya umarce ta da ta fita ta bashi wuri, yana gani ta fara mishi kallan tambaya, idanunta d'auke da tsan tsan tsoro,
"Malama baza ki fita bane"
Tsawa ya k'ara daka mata da yaga bata da shirin fita, kan ma yakai ayar maganar shi yaga ta fara lalumar murfin mota tana shirin fita, ga jikinta ta ya k'ara rikecewa sai rawa yake, hawaye sai kwarara suke a fuskar ta, binta yayi da muguwar harara har sai da ta gama fita daga motar gaba d'aya sannan ya maida hankalin shi kan motar shi tare da fisgar ta da barin wurin har yana tayar da k'ura.
(Sakeena kuwa taga ta kanta. Ina kuma kamal ya kawota??
And na d'an dade banyi updating ba ina ta shirin exams though yanzu saura guda d'aya na gama.
Dont forget to vote and share ❤️)
YOU ARE READING
ZAFIN RABO ✔️
RomanceLabari ne da ya k'unshi tsana, k'iyayyaya, mugunta, da uwa uba soyayya. Ku biyo ni kuji me zai faru a littafin //Zafin Rabo//