Fifteen

1.5K 154 8
                                    

A hankali yake tuk'a motar har ya isa hotoro GRA, bayan yazo saitin makeken gidan ya fara yin horn, bai jima ba aka zo aka bud'e mishi haka ya saka hancin motar shi ya shiga cikin har yayi parking a harabar gidan, ya jima kafin ya fito, a sanyaye ya taka har ya isa parlor d'inshi, yana shiga ya wani zube a kan doguwar kujera tare da k'urawa pop d'in d'akin ido, wani irin nishad'i yake ji, bazai taba iya misilta irin farin cikin da yake ciki ba, ranshi yayi mishi wani irin fari, baima fara azabtar da ita ba, wannan kawai somun tab'i ne, sai ya tabbata an gama da ita a gidan karuwanan an tsorata ta tare da raba ta da kwanciyar hankali da farin cikin ta sannan ya dawo da ita gidan nan ya k'arasa gamawa da ita, yayi alkwarin sai ya maida ita zararriya kuma tab'arb'iya sai ya musguna mata irin muguntar da ta fita daga tsamanin ko wane irin mutum.

Yana gama tunanin shi ya mik'e yayi kitchen, fridge ya bud'e ya d'auko bottle water ya fara zubawa cikin sai da ya sha ya k'oshi sannan ya fita yayi hanyar bedroom d'inshi, yana shiga ya fara neman switch dan ya kunna fitila saboda duhun d'akin, d'akin na kawo haske yayi idu biyu da frame d'in dake fashe akan tiles, wata irin ajiyar zuciya yayi, sannan a hankali ya fara takawa har ya isa wurin, kamar wanda bashi da laka haka ya tsugunna ya d'auke frame d'in a hankali, da fuskar kamil ya fara cin k'aro, jin wani abu yayi ya soki zuciyar shi, ya nemi duk farin cikin da yake ji d'azu ya rasa, haka ya dunk'a kura ma fuskar shi kallo kamar kamil ne yake kallo a zahiri, idanunshi sunyi jajawur dasu a d'ank'ank'ani lokaci, k'walla ta cika idanun taf,

"zan rama maka abunda tayi maka, yarda ta hana ka farin cikin, ta saka ka a cikin rayuwar kwunci nayi alk'warin sai na ninninka mata abunda kaji, sai na saka ta dana sanin zuwa duniya kamil, yacce ta zama sanidiyar mutuwar ka nima sai na zama sanidiyar tata ko bata mutu ba sai na tabbata na raba ta da hankalin ta"

A hankali yake maganar ga wasu kwalla masu zafi da suke zuba a idanunshi, har yau ba wanda yasan mene ya hardasa cutar kamil, ko mami da abba, shi kad'ai ne ya sani, shi kad'ai ne yasan irin tashin hankalin da kamil ya shiga a sanadiyar sakeena, shine kad'ai yasan yarda so ya azabtar da d'an uwanshi, shine k'adai yasan wahalar da kamil yasha a hannunta, dan haka duk abunda yayi mata daidai ne, duk rashin imanin da zai nuna akanta daidai ne dan ita muguwar mace ce, mayaudariya maici amana, dama zai iya maida hannun agogo baya da sai ya hana kamil zuwa turkey, dan ya sani da bai je k'asar ba da ba abunda zai tab'a had'a shi da ita, wani irin tsananar ta yaji ya k'ara bi mishi jini, ba abinda bai gaya ma kamil ba lokacin da yazo wurin shi yayi mishi maganar ta, ba abunda bai gaya mishi ba akan san da yake ma yarinya yayi yawa amma sam sam bai ji maganar shi ba, shi kuwa da yaga d'an uwanashi cikin tsan tsan farin ciki shine abun da ya hana shi k'ara mishi wata maganar, kuma yayi mutuk'ar danasani, hawaye sun gama jik'a fuskar kamal, ji yake zuciyar shi na tafasa kamar zata fashe tsabar bacin rai, ya tsane ta ba y'ar k'aramar tsana ba, yak'i jininta.

Zumbur yayi ya mik'e kamar wanda aka tsikara wa alura, bayan ya ajiye frama d'in a k'asa, hannunshi ya saka a back pocket din wandon shi ya d'auko wayar shi sannan yayi dialing kan number d'in haj maimuna, ba'a dad'e ba ta d'auka, shi ya fara magana ko amsa sallamar ta bai tsaya yi ba,

"Ina so ki had'a ta da wani a daran yau, wanda zai lallata mata rayuwar ta wanda zai mata tabon da baza ta tab'a mantawa dashi ba, ina son ki had'a ta da wanada zai saka ta cikin fargaba da tsoro da dana sanin zuwa duniya"

Yana gama fad'a ya kashe wayar shima bai jira amsar ta ba, wasu hawayen ne suka sake zubowa a fuskar shi, a hankali ya sami wuri ya zauna akan gado tare da saka tafin hannunshi ta kulle fuskar shi ko dan hawayen zasu daina zuba, amma kamar ya k'ara kunna su, ba abunda yake tunawa irin muguwar wahalar da kamil yasha, cutar da yayi wacce tak'i ci tak'i cinyewa, mintinan da yake jera wa yana aman jini, kwanakin da yake a kwance ba ya iya ko motsi, duk sabida wata banza mace, macen da ma yafi k'arfinta, yayi ma kanshi alkwarin bazai tab'a yin kuskuren da d'an uwanshi ya tafka ba, bazai tab'a kula mace ba balle har yayi irin wannan mahaukaciyar soyyayar, haka ya zauna shi kad'ai a d'aki ba abunda yake sai zubar da kwalla dan yayi mutuk'ar kewan kamil, sai da ya gama kukan shi mai isar shi sannan ya mik'e yayi bathroom dan yin wanka da alwala ko ya d'anji sanyi a ranshi.

(To yanzu dai munsan mai ne ya faru da kamil, ciwon mutuwar sa da har yanzu baibar kamal ba

Please vote, share and comment ❤️

Kada ku manta su suke k'ara mun k'arfin gwiwar typing da posting)

ZAFIN RABO ✔️Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt