Sixteen

1.5K 154 10
                                    

Tana zaune akan katifa da had'a cinyoyinta da k'irjinta, ita kanta bata san awani nawa ta shafa tana yin abu d'aya wato kuka kenan, yanzu kanta ba irirn sarawar da baya mata, jin da tayi an bud'e k'ofa ya saka ta saurin mik'ewa, ka ganta gaba d'ayan ta a tsorace take, duk ta birkice bayan fargabar da ta cika mata ciki, ummeeta da sisi ta gani a tsaye, sakeena jikinta ne ya hau rawa ganin irin kallon da suke mata, hantar cikinta ta k'ara kad'awa,

"Mik'a mata kayan"

Sisi da fad'a a gadaran ce, haka ummeeta ta ajiye mata su a kan katifar, sakeena kuma ba abunda take in ba binsu da kallo ba, idanunta d'auke da alamun tambaya

"Ki kintsa cikin kayan nan dan nan da k'aramin lokaci zakiyi bak'o"

Zuciyarta wani mahaukacin bugawa tayi, tare da fara harbawa kamar zata tsage daga k'irjinta, yanzu idanunta sun k'ara cika taf da k'walla, tayi zuru zuru da ita ba abinda take sai bin tsinaniyar rigar baccin da take a ajiye akan katifar da ido, ko yau da yake daran farkon ta ita da kamal wanda igiyar shi uku take d'aure akanta kuma koda tana gidan shi, baza ta saka irin wannan kayan ba, balle har ta d'auka ta saka ma wani banza k'ato, wanda ba muharamin ta ba, maganar sisi ce ta dawo da ita duniyar tunanin ta,

"Baza ki d'auka ki fara shirin ba ko sai na saka yaran nan sun tub'e ki sun saka miki da kansu ne"

Ji tayi jikinta ya fara rawa, barin ma yarda taga fuskar sisi bata d'auke da alamun wasa, sakeena k'ara rikicewa tayi, ba abunda take fad'i a ranta in banda nashiga uku, ba irin tsinuwar da bata aikawa kamal ba, duk da a rud'en da take bata da shirin d'aukar rigar ta saka, a hankali ta bud'e bakinta ta fara ma sisi tambaya,

"Ki gaya mun kamal ne ya baki umarnin a cimun wannan irin mutuncin"

So take taji amsa, so take ta k'ara tabbatar ma kanta wani irin mugun namiji ta aura, Tana jiran taji amsa kawai taga sisi ta tintsere da dariya ta d'an dad'e tana abu d'aya kamar tab'arb'iya, sannan can kuma ta had'e fuskar ta tare da juyawa dayi ma ummeeta wani irin kallo, kan sakeena ta ankara kawai taga doguwar rigar atamfar dake jikinta a k'asa, tana tsaye daga ita sai bra da underwear, ga ummeeta ta take shirin b'alle ma b'allin bra d'in jikinta , tsirara suke san yi mata da gaske, wata irin k'ara ta saki tare ta saurin tsugunnawa, da rugume jikinta, kan kice ma hawaye sun fara ambaliya a fuskar ta,

"Yi miki tsirar kad'an ne daga cikin aiki na, dan haka in zaki tashi ki saka kayan nan da kanki tunda sauran mutunci to in kuma kinga baza ki iya ba in saka ta ta cigaba da abinda ta fara"

Tsigar jikinta wani irin tashi take, amma gaskiya way'annan mutannen laananu ne, su basu damu da suga tsaraicin taba wato, ba abunda zuciyarta take in ba bugawa ba tsoro fal cikin ta, amma har lokacin sakeena bata da niyar canza ra'ayin ta na baza ta saka kayan ba, ko kashe ta zasuyi da kanta dai baza ta tab'a kai kanta ga halaka ba, jin ummeetan da tayi akanta ne ya sata saurin k'ara damk'e jikinta wuri d'aya, tana ji hannuwa sunkai hud'u suka rik'eta, bama tasan lokacin da sauran y'an matan suka shigo ba, wani hawaye ne masu zafi suka k'ara zuba, ita yau za'a tub'e ma kaya me yakai wannan cin mutunci, shure shure ta fara tana ihon da su kyale ta, amma ina sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, haka suka cire mata sauran kayan ta suka barta a cikin pant d'inta, sakeena ba abunda take in banda kuka me abun tausayi, jikinta wani rawa yake tsabar k'arfin kukan, haka suka saka mata wannan jar rigar bacci, wacce da ita da babu duk d'aya ne a wajan ta, kan ta k'ara ankara taji an d'aga ta cak, wani shure shuren ta fara, dan a ajiye ta, amma baza ta tab'a iyawa da k'atotan gardin da ya ruk'e ba, wata irin tashin hankali ta shiga da taga namijin da ba muharaminta ba ya ganta a cikin wannan yanayin bayan kayan dake jikinta da suke nuna tsaraicin ta b'aro b'aro, kamal ya saka yau an tsige mata duk sauran mutuncin ta na y'a mace,

"Sai da aka gaya miki ki saka kayan tunda sauran mutuncin ki amma taurin kai ya hanaki"

Tana ji ummeeta na fad'a, ita kuma bata bi ta kanta ba sai faman saka hannunta take tana shirin kulle jikinta a haka har suka shiga wani side daban a gidan aka shigar da ita wani bedroom sannan wannan gardin ya jefa ta akan gado, yana ajiye ta ta k'ank'ame jikinta wurin d'aya, tana ji ya fita ya kullo k'ofar, sakeena na ganin haka ta duro daga kan gadon tayi wurin k'ofar a guje, ta murd'a handle d'in amma an kulle ta waje, tuni ta fara buga k'ofar tana rok'an su da Allah da annabi su bud'e mata, haka akayi banza da ita har ta gaji ta k'ara zubewa a k'asa ta cigaba da kukanta, bata san lokacin da ta shafa a wurin ba, tana fara jin k'arar takun mutum gabanta ya fara fad'uwa, zuciyar ta ta fara wani irin bugawa, da mugun sauri ta mik'e ta yayimo duvet blanket d'in dake kan gadon ta kulle gaba d'aya jikinta harta kanta wanda baya d'auke da d'ankwalli, dube dube ban d'anki ta fara yi yarda zata iya shiga ta kulle kanta amma ba band'aki a cikin d'akin, ta taji k'arar key a jikin k'ofa ya k'ara saka ta saurin shigewa jikin bango, haka ta rungume jikinta wurin d'aya tare da k'ara damk'e duvet d'innan, ta sunkuyar da kanta k'asa tare toshe kunnanta da kulle idanunta, ko wane bil adama ne zai shigo d'akin bata san jin muryarshi balle ta ganshi, in ka ganta a lokacin ko mara imani ne sai mutuk'ar tausayinta ya dakan maka zuciya, tana ji aka shigo ko da wasa bata d'aga kanta ba, ba abunda take in banda add'ua ga jikinta da har lokacin bai bar rawa ba saboda tsoro, jin mutum d'in da tayi a kusa da ita ya k'ara saka ta shigewa jikin bango tare da cigaba da addu'ar da take,

"Duk tsoro ne ya saka ki yin haka?, kada ki damu nan dan lokacin kad'an zan tabbata kin nemeshi kin rasa"

Dukda ta kulle kunnanta tana d'an tsintar maganar shi, ji tayi hantar cikinta ta k'ara kad'awa, hawaye sun sake jik'a duvet d'innan, jikinta ya k'ara kyarma, sakeena ta k'ara rungumo jikinta wuri d'aya, kamal ya gama da rayuwar ta, kamal azalimi ne, haka kawai bata ji ba bata gani ba, wannan wace irin mugunta ce yana ji Allah zai barshi abunda yake shirin sawa a aikata akanta, jin wata irin tsanar shi tayi tana bin jinin jikinta, Allah wadaran da irin mai halinshi, Mommy da daddy suka san irin mugun da suka aura mata sai sunyi mutuk'ar dana sanin, danshi kamal a mugayen mazan ma ya cira tuta, dan ita tunda take a rayuwarta bata tab'a ji ko ganin inda miji yakai matar shi ta sunna wurin karuwai ba duk tsanar tan da rashin santan da yake, ko a litafi ko a film.

Jin hannun da tayi akanta ne ya saka ta saurin d'agowa da idanunta da suke d'auke ta tsan tsan tsoro da fargaba, wanda ta gani a tsugunne a wurin ne ya saka hankalin ta k'ara tashi, tare da k'ara zaro manyan idanunta saboda abun mamakin dake gabanata, me ya kawo shi wurinan me yake yi anan? Haka ta fara jera ma kanta tambayoyi, a hankali ta furta sunan shi.

(Da fatan dai masu cemun nayi updating suna voting da sharing,

Yaya zaku ce game da abunda kamal yayi ma sakeena??

Please vote, share and comment ♥️♥️)

ZAFIN RABO ✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora