Ko da suka iso gida tayi bacci, a hankali ya bud'e k'ofar ta ya cire mata seatbelt sannan ya d'auko ta a hannunshi, dank'a ma shaheeda handbag d'inta yayi, daman suna bayan su suma a mota ita da imran, yarda yake tafiya a hankali saboda baya san tashin ta, tun kan ya iso wurin entrance door d'in already an bud'e mishi, da kanshi ya shiga har cikin d'akinta sannan ya kwantar da ita akan gado.
Takalmin k'afarta ya fara zare mata a hankali, sannan ya cire mata mayafi kanta, duk abunda yake shaheeda na gefa na kallon su kana ganin fuskar ta kasan sha'awa suke bata.
"Zaki iya bani rigar baccin ta??"
Yana maganar yana sosa k'eya shi bai yarda wai kunya yake ji, shaheeda murmushi tayi sannan tayi hanyar closet d'in sakeena ta d'auka mata wata rigar bacci, armless wacca zata tsaya mata a cinya, tana fitowa, ta dank'a mishi a hannu, sannan ta fice tare da jawo k'ofar, yana ji ta fita, ya juya kan matar shi da shirin bata duka attention d'inshi.
Sai da ya matsar da gashin kanta da ya zubo ya rufe mata idanu, sannan ya zauna a gefan ta, a hankali ya d'ago da ita, ya jingina ta a jikinshi, sannan ya fara b'alle abayar jikinta, sai da ya gama cire mata komi tsaf sannan ya zura mata rigar tare da maida ita kan gadon a hankali, k'ara maida gashin kanta baya yayi da ya k'ara zubo wa ya rufe mata idanu, sanna ya jaa mata bargon.
Kafa ta yayi da idanu dan baya san ya tafi ya kyale ta, barin ma yanzu da yaga bata jin dad'i, ya koma gida hankalin shi bazai kwanta ba sam sam shi kanshi ya sani, yanzu da ya san dad'in rayuwa da ita ko sakwan d'aya ba ita wahala da wuya take mishi, ji yake tamkar zai zare, shi kad'ai yasan ciwo da azabar da yake sha ta dalilin rashin samunta a kusa dashi ako da yaushe, wata ajiyar zuciya yayi, yayin da ya k'ara shafar fuskar ta.
"Har yanzu bika fahimci yarda nake sanki ba ko?"
Dan da ta gane yarda yake jinta tamkar ranshi da tayi kok'arin daina nisantar kanta dashi ta gaya ma daddy maganar shi, itace rayuwar shi a yanzu, ko wane zama da tashi da zaiya itaca, kiftawar idanunshi itace, a mafarkin shi itace, idanun shi a bud'e itace, wata irin soyyaya yake mata dashi kanshi be san iyakar ta ba, be san adadin ta ba dan bazai tab'a iya sifanta ta ba da ko wace kalma, ko wane sakwan da zai wuce sai yaji kaunar ta tabi jinin jikinshi, sai yaji soyyar ta ta k'ara ninkuwa a tsokar zuciyar shi, shi kanshi baiji son da yake mata is normal dan ya wuce tsamanin ko wane bil adama.
K'ara jaa mata bargo yayi, sannan ya cigaba da zuba mata manyan idanunshi da suke d'auke k'arara da tsantsar son da yake mata, ya dad'e yana abu d'aya kamar bazai tashi ba, sai can da kyar ya mik'e ya saka siraran lips d'inshi a goshin ta tare da sumbata a hankali, shima yayi y'an sakwani a haka, sai can ya d'ago da kanshi, cikin sanyayiyr murya yace.
"I love you so much jewel, goodnight"
Sannnan ya fito bayan ya kashe mata fitila, yana fitowa yaga shaheeda zaune a parlon da aka tanadar musu ita da sakeena musamman na hutawar su, murmushi yayi mata yayin da itama ta mik'e.
"Har zaka wuce??"
D'aga Mata kai yayi, San nan cikin kunya yace ya har mata amanar sakeena, ta taimaka ta kular mishi da ita kafin ya dawo gobe, shaheeda ma murmushi tayi taci mishi ba matsala, sannan ta takashi har gate.
Ko sa suka fito yayi mamakin ganin imran har lokacin bai tafi ba, sai dai tun fitowar su hankalin shi baya kanshi, ya kasa d'auke idanu akan shaheeda ya kuma tuna abunda jewel ta gaya mishi d'azu ya bashi tabbacin maganar ta gaskiya ne, murmushi yayi sanna ya juya kanta.
"Saheeda ko zaka bani number d"inki, in a so in kira ki inji yaya jikinta kan na kwanta"
Yana fad'a ya saci kallon imran, sai a lokacin abokin nashi ya tuna dashi, gani yayi ya had'e gira da fuska can kuma kome ya tuna sai yaga ya saki fuskar tashi, shi dai saurin k'iris dariya ta sub'uce mishi, fito da wayar shi yayi ya mik'a ma shaheeda, sai ta ta gama rubuta mishi numba dinta sannan ta dank'a mishi wayar tace ita bari tayi ta gida, sallama ta musu shi da imran sannan ta wuce ciki, imran be bar kallonta ba har ta b'acce mishi sai washe hak'ora yake, kamal girgiza kai yayi yayin da ya bud'e motar shi zai shiga amma sai ji yayi an kamo hannunshi.
YOU ARE READING
ZAFIN RABO ✔️
RomanceLabari ne da ya k'unshi tsana, k'iyayyaya, mugunta, da uwa uba soyayya. Ku biyo ni kuji me zai faru a littafin //Zafin Rabo//